Ƙungiyoyin Saudiyya sun dage kan Vinicius Jr, Manchester City na son Luiz

Manchester City na son dauko dan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz daga Juventus, Saudi Arabiya har yanzu tana zawarcin Vinicius Jr, Chelsea na son daukar Trevoh Chalobah kan fan miliyan 40.
Manchester City na duba yiwuwar daukar aron dan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 26, duk da cewa kulob dinsa Juventus na son ganin an sanya yiwuwar sayansa a matsayin din din din cikin yarjejeniyar. (Athletic)
Kungiyoyi a Saudi Arabiya har yanzu suna sha'awar kawo dan wasan gaban Real Madrid Vinicius Jr, mai shekaru 24, zuwa kasar yayin da babban jami'in kula da gasar ya ce matakin "batun lokaci ne". (ESPN)
Chelsea na son fam miliyan 40 ga duk wanda ke da sha'awar sayan dan wasan bayanta dan Ingila Trevoh Chalobah bayan ta dawo da shi daga Crystal Palace. (Sun)
Tsohon kocin Manchester United Erik ten Hag na iya maye gurbin Nuri Sahin a matsayin kocin Borussia Dortmund idan kungiyar ta sha kashi da Bologna a gasar zakarun Turai ranar Talata. (Florian Plettenberg)
Manchester United da Chelsea za su fafata da Bayern Munich wajen siyan dan wasan tsakiyar Ingila Jamie Gittens, mai shekara 20, a bazarar nan. (Florian Plettenberg)
Real Madrid a shirye ta ke ta daina zawarcin dan wasan bayan Canada Alphonso Davies, mai shekara 24, wanda ke dab da kulla yarjejeniya ta tsawaita kwantiraginsa a Bayern Munich. (AS - Spanish)
Juventus na sha'awar dauko dan wasan baya na Newcastle Lloyd Kelly, mai shekara 26, zuwa Italiya watanni bakwai kacal bayan ya zo daga Bournemouth a kyauta. (Gianluca da Marzio)











