Da gaske ne jima’i na cikin jerin wasannin motsa jiki a Sweden?

..

Gwamnatin Sweden ta mayar da martani kan labarin da aka rinƙa yaɗawa cewar ƙasar ta sanya jima’i a cikin jerin wasannin motsa jiki na ƙasar.

Labaran da suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta sun ruwaito cewa za a fafata a wasan a lokacin bikin wasannin motsa jiki na ƙasar.

Sai dai a martanin da ta mayar, wata babbar jami’a a ofishin jakadancin Sweden da ke Najeriya, Anna Edoh, ta ce a baya-bayan nan wani kamfani mai suna Ƙungiyar Jima’i ta Sweden ya rubuta wa gwamnati takarda neman yin rajista da Hukumar Wasannin Motsa Jiki ta Sweden.

Sai dai ta ce “Mun yi watsi da takardar kasancewar ƙungiyar ba ta cika ƙa’idojin shiga hukumar kula da wasannin motsa jiki ta Sweden ba.”

Saboda haka ta ce ba gaskiya ba ne cewa an sanya jima’i a cikin jerin wasannin motsa jiki na ƙasar.

Ta ƙara da cewa shafin intanet da ya rinƙa yaɗa labarin ba ya da alaƙa da gwamnatin ƙasar.

A ƙarshe ta ce gwamnatin Sweden ba ta da masaniya kan cewa ko jima’i wasan motsa jiki ne.

Takardar martani daga ofishin jakadancin Sweden a Najeriya
Bayanan hoto, Takardar martani daga ofishin jakadancin Sweden a Najeriya

Binciken da BBC ta yi ya nuna cewa akwai wani shafin intanet na wata ƙungiya da ta kira kanta Ƙungiyarr Jima’i ta Sweden.

Dukkanin bayanan da aka wallafa a shafin na magana ne a kan abubuwan da suka shafi saduwa, sai dai ba mu iya tantance cewa gwanmati ta amince da shafin ba.