Iskar gas ta hallaka aƙalla mutum 24 a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Reuters
Zuwa yanzu an gano akalla mutum ashirin da hudu da suka mutu, wadanda suka hada da mata da yara, a sanadiyyar shakar iskar gas mai guba ta Nitrate Oxide a wani wajen aikin hakar zinariya ba bisa ka'ida ba a Afirka ta Kudu.
Mutanen sun rasu ne sakamakon shakar iskar gas din a wani sansani na 'yan-kama-wuri-zauna a birnin Boksburg, wanda ke gabas da birni mafi girma a kasar ta Afirka ta Kudun, Johannesburg.
Masu aikin ceto sun shafe daren da ya gabata suna aiki har zuwa yanzu domin gano wasu da lamarin ya rutsa da su.
Yawanci masu aikin hakar zinariya ba bisa ka’ida ba ne ke amfani da iskar gas din Nitrate Oxide a kasar ta Afirka ta Kudu, inda suke kiran iskar da suna zama zamas, domin tace zinariya daga kasar da sukan sato daga wata mahakar ma’adanin da aka yi watsi da ita a yankin.
An gano daya daga cikin tukwanen iskar gas din da mutanen ke amfani da su na tsiyaya a wannan sansani na Angelo mai dimbin jama’aent, wanda ke gabas da birnin Johannesburg.
An samu mutanen da suka mutu ne a kewayen da’irar mita daro daya daga wajen.
Masu taimakon gaggawa sun sheda wa BBC cewa ba wanda aka kwantar a asibiti, amma yayin da suke ci gaba da aiki a cikin dare suna fargabar cewa za a iya samun karin mutanen da suka mutu
Wannan hadarin ya faru ne bayan wata shida da wanda faru a ranar jajiberin Kirsimati wanda wata tankar iskar gas ta fashe, ta kuma hallaka mutum arba’in da daya a wannan garin.
Aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba abu ne da ake yi sosai a yankunan da ke da zinariya a kusa da birnin Johannesbourg, inda jama’a yawanci masu wannan aiki galibi daga kasashe makwabta kan yi kale a wuraren da aka yi aikin a baya aka bari.
Wannan hadarin da ya faru a jiya Laraba ka iya harzuka hukuma a kan masu irin wannan aiki, wadanda ake dauka kungiyoyi ne na bata-gari da ake zargi da yada miyagun laifuka a unguwannin garin da suke aiki.
A bara rikici ya barke inda aka rika kai farmaki kan masu hakar zinariyar tsawon kwanaki a wani yanki da ke yammacin Johannesbourg, bayan da aka tuhumi wani gungun mutum 80, da ake zargin wasunsu masu wannan aiki ne da laifin yi wa wasu mata 8 da ke daukar hotuna na shirin talabijin a wata tsohuwar mahakar m’adanai a Afirka ta Kudun.











