Ko hana hakar gwal zai magance kashe-kashen Zamfara?

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yanzu haka Shugaba Buhari ba ya cikin kasa, yana amsa gayyatar wasu sarakunan Larabawa a Gabas Ta Tsakiya.

A daya daga kwararan matakan da aka dauka don shawo kan mummunar matsalar masu kisan gilla da fashi a Jihar Zamfara, Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar dakatar da hada-hadar hakar ma'adanai a Zamfara da jihohin da ke makwaftaka da ita a ranar Lahadi.

Sai dai ba a bayyana hakikanin yadda al'amarin zai kasance ba.

Mukaddashin Sufeto Janar na 'Yan sanda, Mohammed Adamu ne ya bayar da sanarwar a fadar gwamnati da ke Abuja a wani jawabi da ya gabatar a gaban Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da Darakta Janar, na Jami'an asiri na DSS Yuwuf Bichi da Darakta-Janar na Jami'an Asirin kasa (NIA) Ahmed Rufa'i.

Bayanin ya yi nunin cewa, "Ayyukan hakar ma'adanai a Zamfara da sauran jihohin da al'amuran suka shafa an dakatar da su nan take.

Sakamakon haka, duk wani mai hakar ma'adanai da aka samu yana ci gaba da aikin hakar ma'adanai a irin wadannan wurare za a kwace lasisinsa bisa kin bin umarnin.

Kuma an ce, "Daukacin 'yan kasashen waje da ke gudanar da ayyukan hakar ma'adanai a wuraren su dakatar (da ayyukan) su bar wurin cikin sa'o'i 48.

Muna masu bayar da tabbaci ga al'umma, musamman wadanda ke zaune a wurare da ake fama da matsalar tsaro ana yin iya kokarin duk da ya dace wajen ganin an shawo kan matsalar.

A cewar Mukaddashin Sufeto-Janar, daukacin wuraren hakar ma'adanai a jihar za su koma karkashin kulawar rundunar tsaro ta musamman (STF), wadanda suka hada da muhimman hukumomin tsaro.

Wannan lamari na da matukar wahala, saboda akwai dubban wuraren hakar ma'adanai a daukacin fadin Jihar Zamafara, inda mafi yawancinsu suna hakar (ma'adanan) ne ba bisa bin ka'idar da doka ta tana da ba, kuma suna cikin sakon yankunan karkakara, wadanda ba lallai ba ne hukumomi sun san da zamansu ba.

Ko mene ne dalilin dakatarwar?

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami'an tsaron 'yan sanda da na soja da na farin kaya wato DSS da kuma na asiri duka za su yi aiki tare a Zamfara.

Adamu ya ce an yi hakan ne "bisa la'akari da bayanan sirri da aka tattara, inda ta bayyana karara yadda alakar masu fashi da makamai da masu hakar ma'adanai ba bisa doka ba take, inda kowane sashe ke taimaka wa sashe."

Kafin gwamnati ta dauki wannan matakin, wasu masu lura da al'amura a jihar Zamfara, musamman wasu daga cikin malaman addini, sun yi ta jefa zargi kamar yadda wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan Intanet ya yi nuni da cewa fafutika ce tsakanin mutanen da ke da karfi a cikin al'umma da abokan huldarsu 'yan kasashen waje.

'Yan kasashen waje wadanda ke kokarin mamaye dimbin dukiyar ma'adanai da ke shimfide Zamfara, al'amarin da ake ganin shi ya haifar ta'addancin kisan gilla.

Akwai dalilin tababa kan hakan. Ganin yadda ta'addancin kisan gillar ya watsu a cikin jihar, tabbas babu wani sashe da aka kyale, har da harkar hakar ma'adanai.

Matsalar kisan gilla a Zamfara ta samo asali ne tsawon shekaru bakwai da suka wuce. Lamarin ya fara ne kan mafi yawan abin da ake gani na satar shanu.

Al'umomin da ke zaune a yankunan sun dauki matakin kafa rundunar tsaro ta kato-da-gora, wadda ta samu nasarar halaka wasu daga cikin barayin shanun, wadanda daga bisani suka kai harin daukar fansa a kan wasu daga cikin al'umomin, musamman yadda suka rika kai wa shugabanin da 'yan kato da gorar hari.

Wannan al'amari dai daya bayan daya shi ya haifar da wani har zuwa halin da ake cikin a yanzu.

Har zuwa yau, mafi yawan wadanda aka kashe ko aka yi garkuwa da su da wadanda aka yi wa fashi da makami da wadanda aka tarwatsa su a Jihar Zamfara manoma ne, wadanda ba su da wata alaka da harkar hakar ma'adanai.

Wuraren da munin lamarin ya yi kamari, irin kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da ke Arewacin jihar ba sassa ba ne da ake hakar ma'adanai.

Wuraren da a baya-bayan nan ta'addancin ya far musu, wadanda suka hada da Mada a Karamar Hukumar Gusau da wani bangare na Karamar Hukumar Tsafe, sun fi shahara da noma, ba hakar ma'adanai ba.

Sai dai, Sufeto-Janar din ya ambaci "rahotannin asiri" kuma tunda al'umma ba za su iya bin kadin wadannan rahotannin ba, sai a ba shi damar tabbatar da gaskiyar lamarin. Abu mafi a'ala dai shi ne hukumar 'yan sanda ta yi kokarin tabbatar da hakikanin gaskiyar rahotannin, ta yadda kada a rufta da su cikin rudani.

An bayar da umarnin dakatar da hakar ma'adanai a Jihar Zamfara ne kwana biyu bayan da Mukaddashin Sufeto-Janar din 'yan sandan ya kaddamar da shirin 'Operation Puff Adder' don shawo kan garkuwa da mutane da ta'adancin kisan gilla a wasu jihohi.

Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar jami'an tsaron soja da na asiri na DSS. 'Yan sanda sun ce "za a aiwatar da shirin ne ta hanyar jibge jami'an tsaron da ke da horo da kayan aiki, tare da ba su tallafin rayuwa don zaburarwa.

Sannan da cikakken hadin gwiwar mabambantan jami'an tsaron da aka tsara su don kawar wa kasar nan da matsala, musamman a kan manyan titunan Kaduna zuwa Abuja da Kogi da Katsina da Neja da Zamfara, wuraren da ake fama da aikata miyagun laifuka da tafka ta'asa.

Abin lura a nan tun cikin shekarar 2016, rundunar soja ta kaddamar da shirin 'Operation Harbin Kunama' don tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.

Wannan shi ne shiri na uku da aka kaddamar makonni biyu da suka wuce.

Kodayake irin wadannan tsare-tsare yunkurinsu tashin farko yana da tasiri, sai dai sukan kasa kai ga gacin kakkabe ta'addancin kisan gilla a jihar daga karshe.

Mu dai yi fatan a wannan karon shirin kakkabe ta'addancin mai lakabin 'Operation Puff Adder" tare da dakatar da hakar ma'adanan a Jihar Zamfara za su kawo karshen mummunan kisan gilla da ake fama da shi.