An jefe masu hakar ma'adanai 9 a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a Afirka ta Kudu na neman wadanda suka jefe wasu mutane har lahira a Johannesburg ruwa a jallo.
Wadanda aka kashe din na hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne, kuma an yi ta jifansu ne har suka mutu.
An tsinci gawar mamatan 9 'yan asalin kasar Lesotho ne a wani titi, sannan aka garzaya azibiti da dayansu da ya samu munanan raunuka.
Dubban masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne ke aiki a kasar, inda ake yawan samun rikici tsakanin bagarori masu gaba da juna.
Kisan na zuwa ne kimanin sa'a 24 bayan wani samamae da 'yan sanda suka kai wurin hakar ma'adanan.
Kwamishinan 'yan sandan lardin Gauteng, Elias Mawela ya yi tir da kisan a matsayin dabbanci sannan ya ce za su yi duk abin da ya dace domin kawo aminci ga mutanen yankin.
Mawela ya ce 'yan sanda ba za su runtsa ba sai sun kamo wadanda suka aikata kisan kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannan.
Tuni aka bukaci karin jami'ai daga Johannesburg domin farautar wadanda suka yi kisana.
Afirka ta Kudu na daga cikin kasashe mafiya hadari a duniya. Gwamantin kasar ta ce a duk minti daya an kashe mutum 58 a bara.











