Birtaniya ta sallami shugabar taron sauyin yanayi na MDD

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Birntaniya ta sanar da sallamar Claire Perry O'Neill daga mukaminta na ministar kula da yanayi ta kasar.
Claire O'Neill, ita ce shugabar babban taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniyada, wanda za a yi a Glasgow a watan Nuwamba.
Sanarwar ta ce daga yanzu ayyukan ma'aikatar za su koma karkashin sashen kula da kasuwanci wato Beis.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, O'Neill ta bayyana damuwa game da matakin sannan ta kara da sukar gwamnatin kasar.
Ta ce an gaza samar da wani sashe da zai kula da gudanar da babban taron, bayan abin kunya na rashin gudanar da taron majalisar ma'aikatar tun da aka kafa ta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Amma a martanin da ofishin ya fitar, ya ce Firaminista Boris Johnson ya yi wa Misis O'Neill godiya kan aikin da ta yi wa kasar.
''Za a ci gaba da shirye-shiryen taron a kan lokaci kuma za a nada sabon ministan da zai maye gurbinta a nan gaba," Boris Johnson ya bayyana.
Hakan na iya zama abin mamaki ga wasu kungiyoyin 'yan kasuwa da masu kare muhalli da ke aiki tare da O'Neill wurin shirya taron da ke tafe.
Wakilan kasashe da masu sasanta tsakani na kasashe da suka kulla alaka game da taron Glasgow ta dalilin Misis O'Neill ma za su yi mamakin sallamar.
Misis O'Neill ta taka muhimmiyar rawa a taron MDD na watan Disamban 2019 a birnin Madrid na kasar Sifaniya, a shirinta na ganin Birtaniya ta karbi shugabancin majalisar.
A wata hira da aka yi da ita a lokacin, O'Neill ta yi amannar cewa babbar damar da ake da ita a taron na Glasgow ita ce ta daukar mataki kan sauyin yanayi.
Idan ba haka ba mutane za su saka ayar tambaya a kan matakan.
Duk da cewa sai a watan Nuwamba za a yi taron akwai jan aiki a gaban gwamnatin Birtaniya na tabbatar da ganin taron ya gudana cikin nasara.











