'Yan Najeriya a Amurka sun nemi Trump ya janye haramcin biza

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya mazauna Amurka sun bukaci Shugaba Donald Trump ya gaggauta janye haramcin bai wa 'yan ci-rani daga Najeriya takarudun biza da kasarsa ta sanya.
Kiran na kungiyar 'yan Najeriya mazauna Amurka ya ce hakan shi ne mafi munin abin da za a yi wa al'ummar kasar da ke fama da matsalar tsaro da bambancin addinai.
A ranar Juma'a ne Amurka ta sanar da matakin, wanda ya shafi kasashen Eritrea da Sudan da Tanzania da Kyrgyzstan da Myanmar da kuma Najeriya.
Amma shugabannin kungiyoyin sun ce matakin da Trump ya dauka wata gurguwar shawara ce da za ta taimaka wa "zaluncin" da Trump ya tabbatar ana yi a kasar.
A cewar sanarwar, "Baya ga alfanun da Amurka ke samu ta fuskar kudi daga daliban Najeriya, ilimantar da daliban kasashen duniya wata kafa ce ta inganta diflomasiyya tsakanin kasashe."
Sanya Najeriya a jerin kasashen, a cewar kungiyar zai yi illa ga huldar da ke tsakanin kasashen da tattalin arzikin Amurkan, yayin da tattalin arziki da kasuwancin China ke habaka.
Kungiyoyin sun ce daliban Najeriya 11,000 da ke karatu a Amurka na sama wa kasar kusan dala biliyan daya na kudaden shiga a shekara da kuma ayyukan yi a kasar.
Sannan kudin makaratar da 'yan Najeriyan ke biya ya taimaka wurin rage wa 'yan Amurka tsadar karatu.
Game da batun bambancin addini kuma kungiyoyin 'yan Najeriya sun ce kasar ce mafi girma a duniya wajen daidaiton yawa tsakanin Musulmi da Kirista.
Sanarwar ta kuma ce a baya ma, Birtaniya ta so kakaba irin wannan haramcin kan Najeriya amma ta janye bayan an tunasar da sabuwar gwamnatin lokacin cewa miliyoyin kudaden da Birtaniya ke samu na shigowa ne ta daliban Najeriya da ke karatu a kasar.
Kwamitin sulhu

Asalin hoton, AFP
Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce gwamnatin kasar ta kafa kwamitin sasantawa kan matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bayar da izinin shiga kasarta ga 'yan Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kwamitin wanda zai yi aiki karkashin ministan harkokin cikin gida, zai yi nazari tare da bitar ka'idojin da Amurka ta gindaya wa kasashen waje don ganin sun cika.
Ana sa ran kwamitin zai yi aiki tare da gwamnatin Amurka da hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa da sauran wadanda abin ya shafa domin cika ka'idojin.
Gwamnatin ta ce a shirye take ta yi aiki tare da gwamnatin Amurka da sauran kasashe musamman ta fuskar tsaro.
Hudu daga ciki kasashen nahiyar Afirka ne, ciki har da Najeriya.
Gwamnatin Amurka ta ce ta dauki matakan ne saboda kasashen sun kasa cika ka'idodin Amurka game da tsaro da samar da bayanai.











