An gargadi wani masallaci kan kiran sallah a Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran hukumomi a birnin Cape Town na gabar teku a Afirka Ta Kudu za su gana da wakilan wani masallaci bayan da aka yi korafin cewa kiran sallar da ake yi kullum na damun mutanen yankin, a cewar kafar yada labarai ta news24.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A wata wasika da jami'an lafiyar muhalli na birnin suka aike wa masallacin da ke yankin Strandfontein, sun ce sun samu korafi kan abun da mutane suka kira "damun su da hayaniya" a kowane lokaci da ake kiran sallah da lasifika.
Wasikar wacce aka rubuta ta a ranar 4 ga watan Disamba ta bai wa Masallacin Masjidus Sauligeen umarnin daina amfani da lasifikar su kuma aika da "wani tsari na yadda za su dinga kiran sallah" nan da kwana 21.
Kafar News24 ta ce wani tsoho ne da ke zaune kusa da masallacin ya aike da korafin.
News24 ta kara da cewa tuni masallacin ya sauya tsarin kiran sallar da lasifikar.
Limamin masallacin Moulana Yusuf Mohammed, ya shaida wa Cibiyar Shari'a ta Musulunci MJC cewa ya samu sakon korafi shekaru da dama da suka gabata kuma tun a sannan suka rage karar lasifikar tasu, amma bai san batun cewa an samu sabon korafi ba.
Wani jami'i a yankin Zahid Badroodien ya ce sanarwar ba ta bai wa masallacin umarnin daina kiran sallah ba.
"Bukatar ita ce ko dai a hada kai da birnin a samar da mafita kan hakan korafin ta hanyar ko dai rage karar lasifikar ko tambayar injiyoyi don sanya abun da zai dinga zuke kara," a cewarsa.











