Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Kamaru sun gaza tsallake gwajin shekaru da ake yi
Lokacin na kara kurewa tawagar Kamaru ta ‘yan kasa da shekara 17 domin bayar da sunayen ‘yan wasan da za su buga mata wasannin share fage na Gasar Cin Kofin nahiyar Afrika.
Wannan ya biyo bayan matsawar da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Samuel Eto’o ya yi, kan cewa sai an yi wa ko wanne dan wasa gwaji, wanda da yawa suka gaza tsallake gwajin.
Tsohon dan wasan Barcelona da Inter Milan ya dage sai an yi amfani da na’urar gwajin shekaru ta (MRI) domin tantance ‘yan wasan a filin atisayensu da ke Mbankomo, a wajen birnin Yaounde.
The former Barcelona and Inter Milan striker's insistence on using Magnetic Resonance Imaging (MRI) screening saw the squad ravaged at their training camp in Mbankomo, on the outskirt of Yaounde.
Cikin ‘yan wasa 30 na tawagar, 21 sun gaza tsallake gwajin shekarun.
BBC ta gano wani koma baya da kamarun ta kara fuskanta shi ne, wasu ‘yan wasa 11 na daban su ma sun gaza cin gwajin a ranar Talata, wadanda a yanzu haka mai horaswa Jean Pierre Fiala ke ta faman yadda zai maye gurbinsu.
Kamaru za ta karbi bakuncin Congo da Chadi da DR Congo da Kuma Jamhuriyyar Afrika Ta Tsakiya a wasannin share fagen gasar kungiyoyin Afrika tsakanin 12 zuwa 24 ga watan Janairu.
Inda za a nemi kasashe biyu kawai da za su iya kai wa ga gasar Cin Kofin kasashen Afrika na ‘yan kasa da shekara 17 da za a yi a Algeria.
Hukumar kwallon kafa ta Kamaru cikin wata sanarwa da ta fitar tace, Eto’o ne ya bayar da umarnin a dauki wannan mataki domin kaucewa bayar da bayanan karya na shekarun ‘yan wasa, wanda kasar ta rika fama da shi a baya.
“Hukumar kwallon kafar ta shawarci duka masu ruwa da tsaki da su tabbatar da shekaru sun yi daidai domin girmama juna.”
Yaki da karyar shekaru a kwallon kafa
Kasashen Afrika da dama sun ta fuskantar zarge-zarge amfani da ‘yan wasan da shekarunsu ya fi na gasar da suke bugawa.
A 2009 ne hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta kirkiro amfani da na’urar MRI a gasar Kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 da aka yi a Najeriya.
MRI na nazartar damatsan ‘yan kwallo ne domin gano shekarunsu.
A 2017 hukumar kwallon kafa ta KamaruFecofoot sai da ta cire ‘yan wasa 14 daga gasar da aka yi a Gabon ta ‘yan kasa da shekara 17.
Tun lokacin yakin neman zabensa a 2021, Eto’o ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen wannan matsala da aka dade ana fuskanta a Kamaru.
Kuma al’umar Kamaru sun yi maraba da wannan mataki na kakkabe masu karyar shekaru a kasar.
Sau biyu Kamaru na zama gwarzuwar gasar nahiyar ta ‘yan kasa da shekara 17, a 2003 da 2019.