Me hukuncin Kotun Duniya ke nufi a tuhumar da ake yi wa Isra'ila kan Gaza?

Shugaban Kotun Duniya na lokacin, Joan Donoghue, ya ce ba a fahimci hukuncin ba
Bayanan hoto, Shugabar Kotun Duniya na lokacin, Joan Donoghue, ya ce ba a fahimci hukuncin ba
    • Marubuci, Dominic Casciani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Shari'a

Babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ci gaba da sauraron ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar gabanta tana zargin Isra'ila da aikata kisan ƙare-dangi a Zirin Gaza da kuma neman ba da umarnin hana kai farmaki a Rafah.

Isra'ila wadda ta siffanta yunƙurin na Afirka ta Kudu da "maras tushe" kuma "wanda bai dace ba", za ta ba da nata martanin a ranar Juma'a.

Kalaman hukuncin da kotun ta International Court of Justice (ICJ) ta yi ya jawo cecekuce tun bayan da Afirka ta Kudu ta shigar da ƙarar kuma an jingina kafatanin hukuncin kan kalmar "plausible", wadda ke nufin "mai yiwuwa".

A watan Janairu ne ICJ ta ba da hukuncin na wucin gadi - inda wani sakin layi a hukuncin ya fi jan hankali: "A ganin kotun, hujjoji da abubuwan da suka bayyana...sun isa a ce wasu daga cikin haƙƙoƙin da Afirka ta Kudu ke nema na kare rayuwar mutane masu yiwuwa ne."

Wannan ta sa wasu da yawa ke ganin hakan na nufin kotun ta amince cewa "akwai yiwuwar" Isra'ila ta aikata laifukan ƙare-dangi da ake tuhumarta da shi.

Wannan fahimtar ta yaɗu nan da nan har ma ta bayyana a cikin sanarwar MDD, da ƙungiyoyin kare haƙƙi, da kafofin yaɗa labarai da dama, cikinsu har da BBC.

Sai dai a watan Afrilu, Shugabar ICJ a lokacin da aka ba da hukuncin, Joan Donoghue, ya faɗa yayin wata hira da BBC cewa ba shi ne abin da kotun ke nufi ba.

Hasali ma, a cewarta, ana nufin Afirka ta Kudu na da haƙƙin ta shigar da ƙara a kan Isra'ila kuma Falasɗinawa na da "sahihin dalili na neman a kare su daga kisan ƙare-dangi" - haƙƙokin da ke fuskantar lalacewar da ba za su gyaru ba.

Bayanan bidiyo, Tsohuwar shugabar kotun ICJ ta yi bayani game da ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alƙalan sun jaddada cewa ba su da buƙatar su faɗa a yanzu ko an aikata kisan ƙare-dangi amma ta amince cewa wasua daga cikin ƙorafe-ƙrafen Afirka ta Kudu, idan an samu hujjoji, za su iya faɗawa cikin ma'anar kisan ƙare-dangi na MDD.

Bari mu duba yadda lamarin yas amo asali da kuma taƙaddamar da ake yi.

An kafa ICJ ne don sasanta rikici tsakanin ƙasashen duniya musamman game da dokokin ƙasa da ƙasa.

Hakan na nufin dokokin da ƙasashe suka amince da su, kamar yarjejeniya kan kisan ƙare-dangi, wadda aka amince bayan Yaƙin Duniya na Biyu don tabbatar da guje wa irin wannan kashe-kashen.

A watan Disamban da ya gabata, Afirka ta Kudu ta ƙaddamar da yunƙurin kafa wannan hujjar, wadda a ganinta, Isra'ila ta aikata laifin kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a Zirin Gaza a hare-haren ramuwa da take kai wa ƙungiyar Hamas.

Ta yi zargin cewa yadda Isra'ila ke aiwatar da yaƙin ya fi kama da "kisan ƙare-dangi", saboda a cewar ƙarar "an yi yunƙurin lalata rayuwar Falasɗinwa". Isra'ila ta yi watsi da zargin tana mai cewa ƙarar ba ta bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa ba.

Dole ne sai Afirka ta Kudu ta gabatar da cikakkiyar hujja kan hakan. Ita kuma Isra'ila tana da 'yancin yin nazari kan iƙirarin ɗaya bayan ɗaya kuma ta yi bayanin cewa yaƙin kare kai take yi da Hamas. Sai dai za a ɗauki shekaru kafin a iya tabbatar da hujjojin da kuma mayar da martani.

Saboda haka sai Afirka ta Kudu ta nemi ICJ ta fara ba da "hukuncin na ɗan lokaci".

Ma'ana umarnin kotu da za ta bayar don dakatar da wani yanyi, ko dakatar da cutar da ake yi wani kafin ta ba da cikakken hukunci.

Afirka ta Kudu ta nemi kotun ta ba da umarnin dakatar da kai farmaki a Rafah nan take

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Afirka ta Kudu ta nemi kotun ta ba da umarnin dakatar da kai farmaki a Rafah nan take

An nemi kotun ta ba da umarni ga Isra'ila ta ɗauki matakan "kare haƙƙi, da cigaba da cutar da rayuwa da haƙƙoƙin Falasɗinawa".

Hukuncin da alƙalai 17 suka bayar (amma wasu ba su amince ba), ya zo ne ranar 26 ga watan Janairu.

"A wannan matakin, ba a nemi kotun ta bayyana ƙarara ba ko akwai abin da Afirka ta Kudun ke nema a kare Falasɗinawa daga gare shi," in ji ICJ.

"An buƙaci a bayyana ko abin da Afirka ta Kudun ke nema akwai yiwuwar an aikata shi."

Ta ƙarƙare da cewa bayan an yarda Falasɗinawa a Gaza na da haƙƙi a yaejejeniyar kisan ƙare-dangi, ta amince cewa suna fuskantar lalacewar da ba za a iya gyara su ba - kuma ya kamata Isra'ila ta ɗauki matakan kare aukuwar kisan ƙare-dangi yayin da ake cigaba da duba faruwarsu.

Kotun ba ta duba yiwuwar ko Isra'ila ta aikata kisan ƙare-dangi ba - amma ko kalamanta sun nuna akwai yiwuwar faruwar hakan? A nan ne kuma taƙaddamar ta fara.

A watan Afrilun da ya gabata, wasu lauyoyin Birtaniya 600, ciki har da tsofaffin alƙalan kotun ƙoli, suka aika wa Firaminsita Rishi Sunak wasiƙa suna neman gwamnatinsa ta dakatar da sayar wa Isra'ila makamai suna masu ambato maganar "akwai yiwuwar aikata laifukan kisan ƙare-dangi".

ICJ

Asalin hoton, Reuters

Sai ga shi su ma lauyoyi masu goyon bayan Isra'ila (UKLFI).

Kwanaki kaɗan shugabar ICJ ta lokacin hukunci, Joan Donoghue, ta bayyana a shirin HARDtalk na BBC kuma ta fayace ƙarara abin da kotun ta ce.

"Ba ta yanke hukunci ba - kuma a nan ne zan gyara abin da ake yawan kuskure a kafofin yaɗa labarai...cewa an ce akwai yiwuwar an aikata kisan ƙare-dangi," in ji alƙaliyar.

"Ta jaddada a uamrnin cewa akwai barazanar cutar da Falasɗinawa zuwa matakin da ba za a iya gyara ɓarnar ba."

Maganar an aikata kisan ƙare-dangi ko ba a aikata ba, kotu ba ta kai ga yanke hukunci kan sa ba kwatakwata.