Yadda wasu 'yan Najeriya suka makale a bindin jirgin ruwa zuwa Spain

Asalin hoton, Salvamento Maritimo
Hukumomi a Sifaniya sun ce sun gano wasu mutane uku da suka makale a bindin jirgin ruwa, bayan shafe kwana 11 a kan hanya daga Najeriya.
Wani hoto da dakarun bakin teku suka wallafa ya nuna mutanen zaune a wani bangare na injin jirgin, yayin da kafafunsu ke lilo.
An kai mutanen uku asibitin garin da jirgin ya tsaya, Gran Canaria, domin duba lafiyarsu.
Babu tabbas ko suna zaune a kan bindin ne a tsawon tafiyar.
Bayanai daga shafin da ke bibiyar sufurin jirgen ruwa ya nuna cewa katafaren jirgin ruwan dakon kayan ya isa Gran Canaria na Las Palmas ne daga birnin Legas na Najeriya - inda ya yi tafiyar mil 2,700.

Asalin hoton, Salvamento Maritimo
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun mutanen da suke makalewa a irin wannan bangare na injin jirgin ruwa ba, wanda yake zama tamkar faifai, kuma da shi ne ake amfani wurin sauya akalar jirgi.
A shekarar 202, wani yaro mai shekara 14 wanda ya yi irin wannan kasada daga Legas zuwa Gran Canaria ya shaida wa jaroidar El Pais cewa ya kwashe kwana 15 na tsawon tafiyar ne a kan bindin jirgin ruwan dakon man.
An kwantar da shi a asibiti kasancewar ya rinka shan ruwan teku mai gishiri ne a tsawon tafiyar, yayin da shi da sauran mutane da suka makale suke yin bacci a wani rami da ke saman karfen.
Ya ce "mun gaji sosai. Ban taba tunanin za mu sha wahala haka ba."
Haka nan duk a shekarar ta 2020, an samu wasu mutane hudu kan bindin wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Norway, wanda ya taso daga Legas zuwa Las Palmas.
Rahotanni a wancan lokacin sun ce mutanen sun boye ne a wani karamin daki da ke saman faifan a tsawon tafiyar ta kwana goma.
A cikin shekarun nan yawan 'yan ci-rani da ke tsallakawa daga yammacin Afirka zuwa tsibirin Canary na kasar Sifaniya ya karu.
Tafiyar dai tana da tsawo, da kuma hadari. A shekarar 2021 Hukumar kula da masu hijira ta duniya ta ce mutum 1,126 ne suka mutu a irin wannan tafiya.











