Afirka ta Kudu ta ƙwace kadarorin mataimakin shugaban Equatorial Guinea

Asalin hoton, AFP
Jami’ai a Afirka ta Kudu sun ƙwace wani jirgin ruwan shakatawa da gidajen alfarma guda biyu mallakin mataimakin shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Teodoro Nguema Obiang.
Wata kotu ce ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin bayan da wani ɗan kasuwa Daniel Janse van Rensburg ya sami nasara a ƙarar da ya shigar kan Obiang saboda zargin sa da kama shi ba bisa ka’ida ba da kuma musgunawa.
Ya nemi a biya shi diyyar kusan $2.2m.
Ya ce an kama tare da tsare shi ba bisa ka’ida ba a Equatorial Guinea na tsawon kwana 500 bayan da aka samu akasi a wata cinikayya.
Mataimakin shugaban ƙasar, wanda ya kasance ɗa ga mutumin da yafi kowa daɗewa a mulki a duniya, bai ce uffan ba kan lamarin.
An daɗe ana zargin shi da shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na mayar da ƙasar mai arzikin man fetur a matsayin tasu su ƙadai, inda suke wadaƙa da dukiya da kuma albarkatun ƙasar.
Wannan na cikin hukunci na baya-bayan nan da kotuna suka yanke a kansa a faɗin duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Mun rubuta batun gidaje biyu a birnin Cape Town a cikin takarda makonni biyu da suka wuce da kuma jirgin ruwa na shakatawa a ranar Talata da ta wuce,’’ in ji wani lauya mai suna Errol Eldson, wadda ke wakiltar ɗan kasuwan a tattaunawa da jaridar AFP.
Ya ƙara da cewa an rubuta takardar sanya kadarorin a kasuwa.
Ƙarar da mista Van Rensburg ya shigar a kotunan Afirka ta Kudu na son mataimakin shugaban ƙasar ta Equatorial Guinea ya biya shi diyya ta daɗe ana muhawara a kai.
Ya kuma wallafa wata takarda a bara na yadda wata tafiyar kasuwanci zuwa Equatorial Guinea a 2013, ta koma zuwa ta raɗaɗi da ƙunci bayan tsare shi da aka yi a gidan yari mai cike da ƙangararru da ke kusa da baƙin ruwa.
Ana ganin Obiang wanda ke bin salon mahaifinsa – da ke kan mulki na tsawon shekara 43 – a matsayin wanda zai gaje shi.
A watan da ya gabata, ya bayar da umurnin a kama wani ɗan uwansa kan sayar da wani jirgi mai saukar ungulu.
Ana zargin ɗan uwan nasa da kin fitar da kuɗin da sayar da jirgin. Amma bai fito ya ce uffan ba kan batun.
Mataimakin shugaban ƙasar – wanda aka sani da yin sharholiya – shi ma ya fuskanci tuhume-tuhume daban-daban.
A 2014, hukumomin Amurka suka ƙwace wani gidan alfarma da ya kai $30m da sauran kadarori a Malibu, wanda ya kunshi wata mota ƙirar Ferrari, inda suka ce ya sayi abubuwan ne da kuɗaɗen al’umma.
Shekara biyu da suka gabata, masu yanke hukunci a Swiss suka ƙwace motocin alatu guda 11 mallakinsa.
A cikin motocin akwai ƙirar Bugatti da Lamborghini da Ferrari da Bentley da Rolls Royce – an yi gwanjonsu a kasuwa kan $27m.
A 2021 ne wata kotu a Faransa ta ci tarar sa da kuma yanke masa hukuncin je ka gyara halinka, kan amfani da kuɗin al’umma domin yin sharholiya a ƙasashen Turai. Sai dai, ya musanta aikata ba daidai ba.
Duka a wannan shekarar, Birtaniya ma ta saka masa takunkumi saboda zargin cin hanci.
Hukumomi sun ce yana kuma da wasu jerin kaya na shahararren mawakin nan na duniya Michael Jackson, wanda ya kunshi abin hannu da ya kai $275,000 wanda shi mawakin ya sanya a hannu lokacin da yake raye wadda ya samu kyautarsa a wata gasa a 1980.
Hukumomin Birtaniya sun ce sabbin takunkuman na cin hanci, an yi su ne kan mutanen da ke sace kuɗaɗen al’umman da suke mulka da barin su cikin ƙuncin rayuwa.











