Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An soke jan katin Lukaku domin a yaki kalaman batanci
Hukumar kwallon kafar Italiya ta soke jan katin da aka bai wa Romelu Lukaku, domin a yaki halayyar wariya a fannin taka leda.
An kori dan wasan Inter Milan a Coppa Italiya fafatawar farko ta daf da karshe kwana 11 da suka wuce bayan da ya ci fenariti sai ya je gaban magoya bayan Juventus ya dauki yatsa daya ya dora a kan lebensa.
Wakilan dan wasan sun ce an yi ta yi masa kalaman cin zarafi tun kan ya buga fenariti da kuma bayan ya buga ya ci kwallon a fafatawar.
Lukaku ya ce ''Hakika hukuncin ya yi adalci.''
Wata kotun daukaka kara ce a Italiya ta soke hukuncin jan katin da aka bai wa dan wasan tawagar Belgium,
Nan da nan shugaban hukumar kwallon kafar Italiya, Gabriele Gravina ya shiga bataun, bayan da ya bibiyi rahoton mai shigar da kara bangaren gwamnati.
Rahoton ya fayyace cewar ''halayyar da Lukaku ya nuna ce, bayan cin kwallon ta jawo aka yi masa kalaman batanci da nuna karan tsana ga dan kwallon''.
''Matakin da aka dauka zai dakile tsarin yaki da kalaman batanci da wariya a fannin kwallon kafa da aka dade ana yi.''
Da wannan sakamakon Lukaku zai iya buga wasa na biyu da Juventus a daf da karshe a Coppa Italiya, bayan da suka tashi 1-1 a karawar farko.
Lukaku ya yi jinjina da tsoma bakin Gravina: "Ya kara da cewar wannan sakamako ne mai karfafa gwiwa da aka aike sako ga duniya.
''Wannan ya nuna yadda ake yaki da cin zarafi da batanci da kalaman wariya.''