Majalisar Amurka ta amince da ƙara yawan bashin da ƙasar ke ciyowa

Asalin hoton, EPA
Majalisar wakilan Amurka ta amince da kudurin buɗe kofa ga kasar ta samu damar kara kuɗaɗen bashin da ta ke ciyowa.
Ƙudurin ya samu amincewa ne da gagarumin rinjaye, lamarin da zai kawo karshen fargabar matsin tattalin arziƙin da kasar ke gaɓar faɗawa.
Kakakin majalisa daga jam'iyyar Republican, Kevin McCarthy, wanda ya cimma yarjejeniya da shugaba Biden, ya yi murnar wannan nasara da yace an kafa tarihi.
Ya ce bayyana cewa sun bai wa muradun al'ummar Amurka fifiko duk da cewa ɗaukar matakin ba abu ne mai sauƙi ba.
Ya kuma yi watsi da sukar da sauran 'yan majalisa ke yi, kan ya gaza cimma manufar rage kuɗaɗen da ake kashewa.
Yanzu abin da ya rage shi ne ita ma majalisar dattawa ta amince da kudirin kafin ranar Litinin, gudun kada a koma gidan jiya.
Shugaba Biden ya nemi a hanzarta amincewa da kudirin saboda ya zama doka a cikin gaggawa.
Amurka za ta kai ƙarshen basukan da aka amince ta ciyo ne a ranar Litinin, biyar ga watan Yuni.
Abin da ake fargaba shi ne da zarar ranar ta cika, Amurka za ta gaza wajen samar da kuɗaden da take biyan bashin da ke kanta, wanda ya kai dala tiriliyan 31.4, lamarin da ka iya jijjiga tattalin arziƙin duniya.
Kuma hakan na nufin ƙasar ba za ta iya karɓar wani bashin ba, wanda zai sanya ta gaza sauke nauyin da ke kanta.
An samu jan-ƙafa wajen amincewa da ƙara yawan bashin da Amurkar za ta iya ciyowa ne kasancewar dole sai an samu amincewar majalisar wakilan ƙasar, wadda jam'iyyar adawa ta Republican ke da rinjaye a cikinta.
Lamarin ya kai ga cewa sai da Shugaba Biden ya gana da shugaban majalisar Kevin McCarthy domin ganin an samu fahimtar juna.











