Ɗan firamare mai shekara 84 da ya zaburar da wasu komawa makaranta

An elderly student Kimani Maruge

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kimani Maruge dan shekara 84, lokacin da ya koyi yadda ake rike fensir
    • Marubuci, Daga Vicky Farncombe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Witness History

A shekarar 2004, Kimani Maruge ya zama mutum mafi tsufa da ya fara karatun firamare, lokacin da ya shiga makarantar firamare ta Kapkenduiywo da ke Kenya.

Ɗalibin mai shekara 84 da haihuwa, tsohon soja ne da ya yi yaƙi da ‘yan mulkin mallaka a yunƙurin neman ‘yancin kai na Mau Mau.

Bai halarci makaranta ba lokacin da yake yarinta, don haka da Kenya ta soke karbar duk wasu kuɗaɗe na karatun firamare a makarantun gwamnati na jihar, sai ya ce wannan dama ce, da zai koyi karatu da rubutu.

Tsohuwar malamar dattijon Kimani, Jane Obinchu ta ba da labarinsa, wanda ya zaburar da mutane masu yawa a faɗin duniya.

Tsufa bai hana ilimi

A watan Oktoban 2003 ne, Jane Obinchu, shugabar firamaren Kapkenduiywo da ke Eldoret mai nisan kilomita 320 daga Nairobi, ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar ofishinta yayin da take shirye-shiryen shiga zangon karatu mai gabatowa.

An elderly student Kimani Maruge

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Burinsa na karanta Littafi mai tsarki na Baibul ne ya yi wa Kimwani Maruge kaimi

A wajen ƙofar sai ga Kimani Maruge. Ya shaida mata cewa yana so ya yi amfani da sabuwar dokar da Kenya ta bullo da ita, wadda ta bayar da damar samun ilmi kyauta a makarantun firamaren gwamnati.

Jane ta rikice kuma ba ta da tabbacin ƙara mutumin da ya kai shekara tamanin a rajistar makarantarta.

"Mun ce ya koma gida, mun ce masa: "Ka tsufa da fara karatu." Don haka, don na sallame shi, sai na ce masa ya dawo a watan Janairun shekara ta 2004," Jane ta shaida wa BBC.

Amma Kimani bai yi ƙasa a gwiwa ba.

“Abin mamaki lokacin da ake buɗe zangon karatu a 2004, sai ga shi a ofishina sanye da cikakken kayan makaranta, da jaka da ƴan littattafan rubutu da fensir a cikin jakar,” in ji Jane.

Jane ta sake ce masa ya dawo bayan mako ɗaya. Lokacin da Kimani ya sake dawowa, sai ta yanke shawarar zama ta tattauna da shi.

Ƙwarin gwiwa bayan gani a mafarki

Kimani ya bayyana mata cewa bai gamsu da sahihancin abin da ya ji daga bakin wani mai wa’azi a coci ba.

Ya fice daga cocin domin nuna adawa. Yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidansa, sai ya ji jiri ya kama shi, sai aka nuna masa kamar a mafarki.

An elderly student Kimani Maruge

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kimani Maruge ya ci gaba da karatu duk da yake yana rayuwa ne a tanti

Jane ta ce: “An nuna masa ya zo makarantarmu don a taimake shi ya koyi karatu saboda ya iya karanta Baibul da kansa.

"Sai ya faɗa mata cewa a cikin mafarkin, kuma an fada masa cewa akwai wata mace da za ta taimaka masa ya iya karatu. Kuma ya ce ba shakka ni ce ya gani a mafarkin nasa."

Jane ta ɗauke shi matsayin dalibi a makarantar. A ranar fara karatu, Kimani ya isa aji a kan lokaci, kuma ya fito tsaf sanye da sabon tufafin makaranta. Zaƙuwar da ya nuna ta jawo hankalin mutane.

Yakan je ya yi wasa da yara yana dogara sanda.

Bayan 'yan shekaru, Kimani ya bayyana kudurinsa.

"Dalilin da ya sa nake son yin karatu shi ne in nuna wa yaran Kenya, da ma duniya baki ɗaya cewa ilimi ya fi komai muhimmanci, ya fi zama mai arziki. Dukiya ta gaskiya ita ce Ilimi," in ji Kimani yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters a 2006.

Matsaloli

Wasu iyayen ba su ji daɗin ganin dattijo tare da 'ya'yansu a cikin aji ba. Sun gudanar da zanga-zanga.

An elderly student Kimani Maruge in a group picture

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kimani Maruge yakan yi wasannin motsa jiki tare da sauran yara

Jane ta tsorata. Sai dai dalibanta sun fito daga ajin suka kori iyayensu.

Wasu iyayen da ba su gamsu da abin da ya faru ba, sun kai ƙara ga hukumar ilimi, kuma sun sa aka sauya wa Jane wurin aiki.

Jane ta shiga ta fita sai da ta koma tsohuwar makarantar da take aiki. Ta samu damar kulla alaka da Kimani kuma ta koya masa yadda ake karatu.

"Mafi kyawun abin da nake tunawa shi ne lokacin da yake ƙoƙarin furta kalmomi," in ji Jane.

"Abin farin ciki ne kuma a lokacin darussan waƙa, yana iya rera waƙa da yin sauran darussan da sauran ɗalibai ke yi."

Kimani ya fara nuna ƙwarewa. Wata rana Kimani ya ɗauki Baibul ya karanta, surar John, aya, ta 316.

"Wannan ita ce ayar farko da ya karanta, tana magana game da Allah ya aiko da makaɗaicin Ɗansa domin ya mutu saboda zunubanmu."

"Mun yi farin ciki lokacin da ya karanta, sai da muka yi hawaye."

Jane ta yi imanin cewa a wannan lokacin mafarkin Kimani ya tabbata.

Yin suna a duniya

Akwai karin abin burgewa.

An elderly student Kimani Maruge on a bus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ya ji dadin tafiyarsa Amurka amma Kimani Maruge bai san dalilin da ya sa ba wanda ya gayyace shi gidajensa ba

A cikin 2005, an kai Kimani da Jane New York, don isar da saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya. Ƙungiyoyin agaji na duniya da ke fafutukar inganta ilmi ne suka shirya wannan tafiyar.

Hotunan kamfanin dillancin labarai na Reuters na Kimani a birnin New York sun nuna shi yana tafiya da wata babbar motar bas ta makarantun Amurka a dandalin Times Square.

Yana tafiya yana dogara sandarsa a wajen ginin Empire State Building kuma yana musabaha da wani jami'in dan sanda.

Amma, har cikin zuciyarsa bai gamsu da tarbar da aka yi masa ba.

"Bai ga kamar an mutunta shi sosai ba. Ya ci gaba da tambayar dalilin da ya sa ba a gayyace mu gidan wani ba, kamar yadda ake yi a Afirka."

Ya kuma ya yi kewar abincinsa na Kenya.

Amma duk da haka, ya isar da saƙo ƙarara ga Majalisar Dinkin Duniya.

"Ina fata kowa da kowa a duniya zai samu saƙon kuma waɗanda ba su samu damar zuwa makaranta ba, za su iya zuwa makaranta."

Kafa tarihi

Can a Kenya, Kimani ya zama shugaban ɗaliban makaranta. Labarinsa ya samu shiga kundin bajinta na Guinness.

Ya mutu a shekara ta 2009, kuma a shekarar da ta biyo baya, an yi wani fim a kan rayuwarsa mai suna The First Grader'.

Shekara ɗaya bayan haka, Priscilla Sitienei, wata unguzoma ‘yar ƙasar Kenya, mai shekara 85, ta shiga firamare domin koyon rubutu.

Ta fara karatu da tattaɓa-kunnenta guda shida da ’ya’ya da dama da ta taimaka wajen haihuwarsu.

An elderly student Priscilla Sitienel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Priscilla Sitienei tana zuwa makaranta har lokacin da ta mutu

Duk da yake, ta girmi Maruge da shekara daya a lokacin da ta fara karatu, amma ta kafa nata tarihin: har zuwa lokacin da ta mutu a 2022 tana karatu, tana da shekara 99, ana tunanin cewa ita ce ɗalibar firamare mafi tsufa a duniya.

"Wani abu da nake alfahari da shi shi ne, tsofaffi da yawa sun koma makaranta, ciki har da yawancin ma'aikatana da su ma suka koma azuzuwa don ci gaba da karatunsu," in ji Jane Obinchu.

"Wannan ta sa na ji kamar Allah na nufi na da wani abu, kuma manufar ita ce na taimaka wa Kamani ya koyi karatu da rubutu."