Shugaban da ya fi kowa daɗewa a mulki na neman a sake zaɓen sa

Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, mai shekaru 80, ya jagoranci gwamnatin da ake zargi da cin zarafin bil adama da, azabtarwa da kuma ɓacewar mutane ba tare da wani bayani ba.
Wasu ƴan takara na jam’iyyar adawa sun shiga zaɓen, amma ba a sa ran za su yi nasara.
Shugaban ƙasar na da alaka mai karfi da ƙasashen da ke da arziƙin man fetur, kuma ya na da ƴan'uwa da ke riƙe da muhimman muƙamai a gwamnati.
Ɗansa, wanda ke rike da mukamin mataimakin shugabar ƙasar, Teodoro “Teodorin” Nguema Obiang Mangue, ya yi rayuwa ta bushasha a Amurka da Turai, har ma ya mallaki safar hannun Michael Jackson da aka yi wa ado da duwatsun ado masu tsadar gaske a cewar hukumomin Birtaniya.
Farfesa Ana Lúcia Sá ta shaida wa BBC cewa “zaben suna ne kawai, kuma babu abin da zai sauya,” Farfesa Sa, wacce ta kware kan harkokin siyasa da mulkin mallaka na Afirka a cibiyar Jami’ar Lisbon, ta ce “ta tabbata Obiang zai yi nasara a zaɓen da fiye da kashi 95 cikin ɗari na kuri’un.
Mai fafutuka Tutu Alicante ma yana da irin wannan ra'ayin, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: “A ranar Lahadi mutane za su kada kuri’ar da gwamnati ke fatan za su yi, saboda ba za ku iya fadin albarkacin bakin ku ba a Equatorial Guinea.” Mista Alicante ya kara da cewa “’Yan adawa ba su da wata dama, shugaban kasar zai yi duk abin da zai iya yi domin kada ya bar mulki.”
Gwamnatin ƙasar dai ba ta jure adawar siyasa, kuma abin ya ƙara muni ne saboda ƴancin yaɗa labaru, domin gwamnati da ƙawayenta ne suka mallaki dukkanin kafafen yada labarai na ƙasar.
Ana tunanin cewa shugaba Obiang, wanda a baya ya ki amincewa da take hakki da kuma tafka magudin zabe, na ƙoƙarin ganin ya wanke kansa a idon duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Satumba gwamnatin ƙasar ta yi watsi da hukuncin kisa, wani abu da ya janyo mata yabo daga majalisar dinkin duniya.
Shugaba Obiang, wanda ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin Mulki da dama, ya kwace mulkin kasar ne da ke a yankin Afirka ta Yamma, mai arzikin man fetur a shekarar 1979 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Bayan karɓar mulki daga kawunsa, Francisco Macias Nguema, ya yi wasu gyare-gyare.
Nguema, wanda mulkinsa ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma gudun hijira daga Equatorial Guinea, daga baya an kashe shi.
Kasar dai na da tarihin abin da masu suka suka kira magudin zabe. Jami’ai sun ce shugaba Obiang ya samu sama da kashi 97 cikin ɗari na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Disamban 2002. ‘Yan takarar adawa sun janye daga zaben, saboda magudi da rashin bin ka’ida.
An kuma samu irin wannan sakamakon a zabe a 2009 da 2016.
Akwai kuma zargin cin hanci da rashawa da ake wa gwamnatin Obiang, bayan da aka ci tarar ɗansa Teodorin Obiang, a wata kotun Faransa saboda amfani da kuɗin jama’a wurin bushasha a Turai. Tuni aka kwace kadarorinsa da ke Faransa.
Mataimakin shugaban kasar, wanda ke kan gaba a jerin waɗanda za su iya maye gurbin mahaifinsa, shi ma Birtaniya ta sanya masa takunkumi a karkashin wani shirin yaki da cin hanci da rashawa a shekarar 2021.
Mataimakin shugaban kasa Obiang ya musanta aikata ba daidai ba. Shi kansa shugaba Obiang ma ya musanta hakan.
Masu kaɗa kuri’afiye da 300,000 ne aka yi wa rajista domin kaɗa ƙuri'a a zaben na ranar Lahadi.
A shekarar 1968 Guinea ta samu ‘yancin kai kuma ta zama Jamhuriyar Equatorial Guinea tare da Francisco Macias Nguema a matsayin shugaban kasa.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana shugabannin kasar biyu – Francisco Macias Nguema da Teodoro Obiang Nguema – a matsayin wasu daga cikin masu taka hakkin bil'adama a Afirka.
Kasar ta gano tarin albarkatun man fetur a shekarar 1996, amma yawancin al’ummar kasar miliyan 1.4 ba su amfana da wannan ba, inda har yanzu talauci ya yi kamari.











