Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin yaɗa labarai shida a jihar

Gwamna Bello Matawalle na Zamfara

Asalin hoton, Twitter/Bellomatawalle1

Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ba da umarnin rufe kafofin yaɗa labarai shida saboda zargin saɓa dokokin da gwamnatin ta kafa.

Kwamashinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya faɗa wa BBC Hausa cewa an rufe su ne saboda sun yaɗa taron jam'iyyar adawa ta PDP duk da cewa gwamnatin jihar ta hana tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce Majalisar Tsaro ta Zamfara ce ta amince tare da ba da umarnin rufe gidajen labaran da suka ƙunshi Radio Najeriya, da Pride FM Gusau, da NTA Gusau, da Gamji Talabijin, da Vision FM, da Al Umma TV.

Sai dai jam'iyyar PDP a jihar ta musanta zargin karya dokar, tana mai cewa hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta ƙasa, NBC, ce kaɗai ke da ikon rufe kafofin.

A kwamashinan, majalisar ta kuma umarci kwamashinan 'yan sanda da ya kama dukkan 'yan jaridar da suka halarci taron wanda ɗan takarar gwamna na PDP, Dauda Lawal Dare, ya shirya.

Tun farko gwamnatin Zamfara ta ba da sanarwar hana tarukan siyasa tare da ɗaukar matakan tsaro na musamman a ƙananan hukumomin Anka da Gusau da Gumi da Bukuyum - inda hare-haren 'yan fashin daji suka fi ƙamari.

Sai dai PDP ta shirya taron a ranar Asabar da zimmar karɓar wasu 'yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar tasu, har ma rahotanni suka ce an samu hatsaniya tsakaninsu da 'yan jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Ƴan bindiga na zafafa hare-hare

'Yan fashin daji

Al'ummar Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a jihar ta Zamfarar na ci gaba da kokawa game da hare-haren da 'yan bindiga suke kai musu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mazauna yankin sun ce yan bindigar sun hana su sukuni sakamakon irin ɗauki ɗai-ɗai da suke musu da hare-haren ba zata da suke kai musu.

Wani mazaunin yankin na Bukuyyum ya shaida wa BBC cewa ko a ranar Juma’a sai da ƴan bindiga suka sace ƴan uwansa goma sha ɗaya a Nasarawa Burkullu da ker yankin na Bukkuyum.

Haka kuma ya bayyana cewa ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigan suka harbe wani yaro a garin.

Ya bayyana cewa kusan duka jama’ar da ke wannan yankin sun yi gudun hijira saboda bala’in ƴan bindigan.

Ya kuma ce a cikin Karamar Hukumar Bukkuyum ɗin sun sace shanu sama da 300 a ranar Juma’a.

Gwamnatin Jihar ta Zamafara dai ta bayyana cewa tana sane da abubuwan da ke faruwa a wannan yanki da wasu wuraren ma da ke makwaftaka da Bukuyyum.

Ibrahim Dosara shi ne kwamishinan watsa labarai na Jihar ta Zamfara ya kuma shaida wa BBC cewa akwai matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance wannan matsala.

Ya bayyana cewa sakamakon wannan matsala majalisar tsaro ta jihar ta yanke shawarar rufe wuraren da lamarin ya shafa domin gudanar da wasu ayyuka.

Jihar Zamfara dai na daga cikin arewa maso yammacin Najeriya da ƴan bindiga suka addaba.

Ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigar suka kashe mutum tara a Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar.