Virgil van Dijk zai ga kwararru domin sanin makomar raunin da ya ji

Asalin hoton, BBC Sport
Dan wasan bayan Liverpool Virgil van Dijk zai ga kwararrun masana lafiya domin gano kaifin raunin da ya ji a cinyarsa.
Dan wasan bayan Netherlands din, ya bug awa Liverpool wasan nin da ta yi duka a Premier a wannan kakar, amma an yi canjin shi a zagaye na biyu na wasan da suka buga da Brentford a ranar Litinin.
Babu tabbaci kan jinyar da dan wasan zai yi, sai dai ana tsammanin ciwon ya zarce yadda ake tunani tun da fari.
Liverpool na da wasu yan wasan baya da ke buga mata tsakiya da za ta iya sakawa a madadinsa, kamar Joel Matip, Ibrahima Konate, Joe Gomez da kuma Nathaniel Phillips.
Kungiyar dai na matsayi na shida a gasar Premier kuma maki bakwai ne tsakaninta da matsayi na hudu.
Liverpool za ta fafata da Wolves a gasar FA a matakin zagaye na uku a ranar Asabar.
Bayan kashin da ta sha a hannun Brentford, kocin Liverpool Jurgen Kloop ya ce :“Virgil ya dan ji rauni amma dai kalau yake, zai iya ci gaba da wasa, amma ba zai iya daukar wannan kasadar ba.
“Dan wasan na cikin farin ciki, kuma dan na ce ba zai dauki kasada ba, baya nufin ba wai ciwo ya ji ba, shi ne ya san irin ciwon da yake ji.”
Liverpool ta samu koma baya sakamakon raunin da yan wasanta suka ji a wannan kakar, yayin da yan wasan gabanta Lui Diaz da Diago Jotta ke Shirin dawowa fagen wasa.
Wasanta na gaba da za ta buga a Premier za ta je gidan Brighton ne a ranar 14 ga watan Janairu a ranar 21 kuma zata fafata da Chelsea a gida.











