Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amfanin mantuwa ga rayuwar ɗan’adam
Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce yawan mantuwa na taka rawa wajen samun zuciya mai sauƙi, kamar yadda Charan Ranganath wani masanin lafiyar ƙwaƙwalwa ya rubuta a cikin wani sabon littafinsa.
Masanin ya ce dalilin da ya sa ƙwaƙwalwa ke tuna abin da ya wuce, yana da alaƙa da yadda mutum ke kallon kansa da kuma sauran mutane da yadda duniya take.
Farfesa Ranganath wanda ya kwashe shekara talatin yana karantar da halayyar ɗan'Adam da yadda ɗan'Adam ke tunani tare da hanyoyin tuna abin da ya wuce da mantuwa, ya ce yawancin bayanan da ake bayarwa kan mantuwa ba haka suke ba, saboda mantuwa na bayar da gudummawa cikin rayuwar ɗan'Adam.
Masanin lafiyar ƙwaƙwalwar ya tattauna da David Robson, ɗan jarida a fannin kimiyya, kan yadda mutane za su fahimci ƙwaƙwalwarsu domin samun kwanciyar hankali.
Littafinku yana cike da batutuwa masu wahala. Bari mu fara da ra'ayin "koyo bisa ga kuskure". Me ya sa muke koyo da kyau a lokacin da muka ƙyale kanmu muka yi kuskure da gangan?
Dan’Adam na iya ajiye abu a kwakwalwarsa da taimakon sauye-sauyen da ake samu na alakar da ke tsakanin kwayoyin da ke isar da sako, ƙa'idar koyo bisa kuskure ita ce, lokacin da kuke ƙoƙarin tuno abubuwan da suka wuce, ƙwaƙwalwa na fitar da abubuwa masu kyau tare da ƙoƙarin tauye wadanda ba su da kyau ta hanyar alaƙanta bayanan da na gaskiya.
Wannan yana nufin cewa hanya mafi kyau don ƙarin koyo ita ce mutum ya ƙalubalanci kansa domin nemo abubuwan da muke son koyo, saboda ta haka ne mutum zai gane inda ƙwaƙwalwarsa ke da rauni, kuma hakan zai ƙara taimaka wa ƙwaƙwalwa wajen tuna abubuwan da suka faru.
Shi ya sa a kodayaushe ana son mutum ya riƙa ƙoƙarin sanin wani abu, kamar misali, idan za ka je wani wuri da ba ka sani ba, maimakon ka yi amfani da manhajar Google, sai mutum ya yi amfani da ƙwaƙwalwarsa ko ta hanyar tambaya domin gano wurin, hakan na da matuƙar tasiri.
Yawancinmu idan mun yi mantuwa muna damuwa sosai to amma ka ce yawanci mantuwa tana da amfani. Ta yaya take da amfani?
Misalin da zan bayar a nan shi ne, idan na je gidanka na tambaye ka: me ya sa ba ka adana komai? Me ya sa ba ka ajiye komai? Idan ba ma manta komai za mu cushe ƙwaƙwalwarmu, kuma zai hakan zai sa mu kasa samun abin da muke nema, a lokacin da muke neman abin.
Yanzu haka, ina zaune ne a wani otal, ina ganin ba wani alfanu ko muhimmancin rike lambar wannan ɗakin otal din da nake zaune a mako biyu nan gaba. Haka kuma a ce na tuna da dukkanin mutanen da na haɗu da su a kan titi. Shin kana buƙatar haddace yadda fuskokin dukkanin waɗannan mutane suke?
Me ya sa mutum ke ƙara mantuwa yayin da yake tsufa?
Matsalar ita ce, yayin da muke girma, shekaru na kama mu, ba lalle ba ne a ce ba ma iya haddace abubuwa, illa dai a ce ba ma mayar da hankali a kan bayanan da ya kamata mu tuna.
Abubuwa na ɗauke mana hankali, kuma dukkanin waɗannan abubuwa da ba su da muhimmanci, suna ɗauke mana hankali maimakon mu bayar da muhimmanci ga abubuwan da ke da amfani garemu.
Saboda haka idan muka buƙaci tuna waɗannan abubuwa, sai mu kasa samun bayanin da muke nema.
Wace dabara za mu yi amfani da ita domin kauce wa hakan, da kuma inganta haddarmu?
Akwai hanyoyi uku.
Ta farko ita ce abu ya kasance fitacce - na daban. Abubuwan da muke sanya wa ƙwaƙwalwarmu suna gogayya ne da juna, saboda haka duk abin da ka fi yawan amfani ko ambato zai fi zama a ƙwaƙwalwarka.
Bayanan da ke ƙwaƙwalwarmu masu alaƙa da wasu hotuna na daban ko na musamman da sauti da ji a jika, su ne waɗanda suke zama a ƙwaƙwalwarmu.
Mayar da hankali kan bayanai masu muhimmanci da jikinmu ya ji ko ya san su, maimakon haddace su, ya fi taimaka mana haddace abubuwa.
Dabara ta biyu ita ce, mutum ya mayar da hankali wajen tsara abubuwa a ƙwaƙwalwarsa, domin ya ba su ma'ana sosai. A littafin, na tattauna kan tsarin gurbin hadda, wanda ya ƙunshi danganta bayanin da kake son ka koya da bayanin da kake da shi daman a ƙwaƙwalwarka.
Dabara ta uku ita ce, za mu iya ƙirƙirar dabarar tuna abu - Neman tuna abu na buƙatar aiki sosai kuma abu ne da zai iya gamuwa da kuskure. Yana da kyau mutum ya yi wata alama da za ta taimaka masa tuna abu, misali, samar da ma'auni zai iya taimakawa a nan.
Misali mun sani cewa waƙa na iya tuna mana da wani abu ko wani lokaci a rayuwarmu. Akwai kuma abubuwa da yau da kullum da yawa da za mu iya amfani da su.
Idan na yi ƙoƙarin tuna cewa zan fita da kwandon shara waje a ranar da za a zubar da shara, sai na sanya a zuciyata cewa, ga ni na kama hanya na nufi ƙofa, to sai na kalli kwandon sharar, kafin na nufi ƙofar.
Saboda haka a zahiri a duk lokacin da na je wajen ƙofa, hakan zai tuna min cewa ya kamata na kasance da kwandon sharar.
Bayan mantuwa, za mu ga cewa ƙwawalwarmu na ɗauke da kurakurai da ba su da alaƙa da abubuwa na gaske. Me ya sa wannan ke faruwa?
Muna da tsarin da ke taimaka mana wajen tuna abubuwa a taƙaice.
Ka ɗauka cewa yanzun nan ka je banki : tuni daman kana da masaniya kan tarin abubuwan da ake yi a bankin da kuma abubuwan da ba a yi a can.
To wannan zai taimaka maka wajen taƙaita bayanan da ya kamata ka tuna, wannan tsarin zai zama tamkar wata gada da za ta ba ka damar ɗaukar waɗannan sababbin bayanai ka yi amfani da su. To amma wani lokaci, zane-zane na cike gurabai da dama, da bayanai masu kura-kurai.
Dalili na biyu shi ne cewa bayan wani lokaci hadda na sauyawa.
Wannan yana da muhimmanci sosai saboda kana son sabunta bayanan da ka haddace.
Idan ka ga uba ko uwa, da ka daɗe ba ka gani ba kuma ka ga fuskarsa ta sauya daga yadda take a lokacin da ka fara ganinsa, dole ka yi ƙoƙarin tuno yadda ainahin fuskarsa take a da.
Amma wani lokacin tunaninmu na yi wa hadda ko ƙwaƙwalwarmu kutse.
Ta yaya hadda ke zama aiki na haɗaka?
Idan muka yaɗa abin da muka sani ga wasu, to za a iya sabunta waɗannan bayanai.
Idan na yi maka bayanin wani abu da ya faru, ƙirƙirar wannan labari na gaya maka shi, ka iya sauya yadda zan iya.
Yadda kake saurarena da abubuwan da kake yi a lokacin da nake ba ka labarin misali wannan na iya sa tsara yadda zan ci gaba da tuna labarin a nan gaba - labarin zai iya zama mai ban dariya fiye da da.
Za kuma ka iya bayar da ƙarin bayani - amma kuma bayanai masu kura-kurai - bayanan da ka iya kutsawa cikin haddata ta wannan labari - ta yadda zan iya rikita labarin ainahin abin da ya faru da kuma abin da ta gaya min, a lokacin da nake bayar da bayanin abin da ya faru. Saboda haka zan iya cewa abubuwa ko bayanai da yawa da muke bayarwa, ba namu ba ne kacokan - tarin bayanai ne namu da kuma na wasu.