Ƙauyen da kowa ke fama da ciwon mantuwa

Ƙauyen Landais Alzheimer, da ke kudu maso yammacin Faransa, ƙauye ne da ke da bambanci - duk mutanen ƙauyen suna da ciwon mantuwa.

Shagon da ke tsakiyar ƙauyen yana samar da kayan abinci masu sauƙi kamarsu baguette amma ba ya karɓar kuɗi, don haka babu wanda zai tuna da bat8un lalitarsa.

Tsohon manomi Francis yana tattara jaridarsa ta ranar - sai na ba da shawarar mu je mu sha shayi nan shagon abincin da ke kusa wanda shi ne cibiyar zamantakewar ƙauyen.

Na tambayi Francis yadda ya ji a lokacin da likita ya faɗa masa cewa yana da cutar Alzheimer's.

Ya gyaɗa kai, yana mai da tunaninsa zuwa lokacin, kuma, bayan ya dakata, ya ce: "Abin da wahala."

'Ci gaba da tafiya'

Mahaifinsa ma yana da cutar Alzheimer's - amma Francis ba ya fargaba.

"Ba na tsoron mutuwa, domin hakan zai faru wata rana," in ji shi.

“A halin yanzu, zan yi rayuwata duk da cutar.

“Ina nan ne don in rayu, duk da dai ba yadda aka so ba ne.

"Idan ka miƙa wuya, shikenan, don haka ka ci gaba, gwargwadon iyawarka."

Kamar yadda suke zuwa shagon abincin, ana ƙarfafa wa mutanen ƙauye gwiwa kan su yi ƙoƙarin zuwa gidan wasan kwaikwayo - kuma su shiga cikin ayyukan da ke gudana.

Philippe da Viviane sun shaida mun cewa suna ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba kamar yadda za su iya biyo bayan gano cutar matuwa da dukansu biyu ke fama da ita.

"Muna fita mu ɗan zagaya da ƙafa," in ji Philippe, yana duban nesa.

Bayan sun gama shan shayinsu kuma sun dunƙule cikin tufafi masu dumi, ma'auratan sun koma cikin wurin shakatawa.

Lokaci ya bambanta a nan, in ji wanda ke yi mun jagora a ƙauyen.

Babu wasu sa'o'i da aka keɓe don alƙawura ko siyayya da kuma share-share tsa - kawai a hankali laƙabi da ƙauyen ƙauye, don ba su 'yanci gwargwadon iko.

Ana sa ido sosai kan ƙauyen - kuma Farfesa Hélène Amieva ta ce sakamakon da ake samu ya nuna cewa a zahiri yana yin tasiri kan yanayin cutar.

Abin da muka saba gani lokacin da aka ajiye mutane a asibiti shine ƙara taɓarɓarewar fahimi - abin da ba mu gani a nan," in ji ta.

"Muna ganin yadda abubuwa ke sauyawa cikin sauki.

"Muna da dalilan da ke nun cewa irin waɗannan cibiyoyin na iya tasiri kan ci gaba a ɓangaren samar da magunguna."

Sun kuma ga "muhimmin raguwar " a cikin tunanin iyalai da yanayin tashin hankali da suke shiga.

Da ta ke nuni da mahaifiyarta Mauricette, ’yar shekara 89, wanda ke zaune a ɗakinta, Dominique ta ce: “Ina da kwanciyar hankali, domin na san tana cikin natsuwa kuma hankalinta a kwance ya ke.”

Ɗakin na cike da hotunan iyali da zane-zane da kujeru, akwai kuma babbar taga da ke kallon lambu.

Tun da babu ƙaɓaɓɓen lokacin ziyara, mutane suna zuwa suna tafiya yadda suka ga dama. Kuma Dominique ta ce ita da ’yan’uwanta mata ba su taɓa tsammanin kulawar za ta yi kyau sosai ba.

"Duk lokacin da na bar ta, ina samun kwanciyar hankali, idan na zo ina ji kamar ina gidanta ne kawai - ina gida tare da mahaifiyata," in ji ta.

Kowane gidan mai hawa ɗaya yana da mazauna kusan takwas, tare da wurin abinci na gamayya, da ɗakunan zama da kuma na cin abinci.

Yayin da mazauna ƙauyen ke ba da gudummawa, kuɗin gudanarwa - na makamancin matsakaicin gidan kula da masu buƙatu na musamman - galibi gwamnatin Faransa ce ke ɗaukar nauyin da ta biya fam miliyan 17 ($ 22m) don kafa ƙauyen.

Lokacin da aka bude ƙauyen, a cikin 2020, shi ne ƙauye na biyu irinsa - kuma shi kaɗai ne ya kasance wani ɓangare na aikin bincike.

Kuma har yanzu ana tunanin akwai ƙasa da guda 12 irinsa a duniya.

Amma ya jawo sha'awar duniya, musamman daga masu neman mafita kan yadda ake tunanin mastalar ciwon manutuwa za ta haɓaka .

A shagon gyaran gashi a ƙauyen, Patricia, mai shekaru 65, wadda aka kammala busar mata da gashinta, ta ce Landais Alzheimer ta maido mata da rayuwarta.

"Ina gida - amma ba ni da wani abin yi," in ji ta.

“Ina da wata da ke dafa mun abinci. Na gaji. Ba na jin daɗin jikina, na san cewa cutar Alzheimer's ba ta da sauƙi kuma na ji tsoro.

"Ina so in kasance wani wuri inda ni ma zan iya taimakawa.

"Saboda a wasu gidajen kulawa, haka yake, amma ba sa yin komai.

"Amma a nan, rayuwa ce ta gaske, idan na ce ta gaske, ina nufin ta gaske."

Sau da yawa, ciwon mantuwa na iya sanya mutane su kaɗaita.

Amma a nan, da alama ana samun kyakkyawar zamantakewar al'umma, inda akwai mutane masu sha'awar ganin juna tare da shiga cikin lamuran da ake gudanarwa.

Kuma masu bincike sun ce wannan nau'in zamantakewa na iya zama wani ɓangare na mabuɗin rayuwa mafi farin ciki, kuma mai yiwuwa ƙarin lafiya lafiya, rayuwa tare da ciwon mantuwa.

Akwai kusan mazauna ƙauyen guda 120 da adadin ma'aikatan kiwon lafiya makamancin haka, tare da ƙarin masu aikin sa kai.

Tabbas akwai lamari na rashin makawa domin babu kuwa cutar ba ta da magani.

Amma yayin da cutar kowane ɗan kauyen ke ci gaba, ana ba su tallafin da suke buƙata.

Kuma yayin da rayuwar waɗannan mazauna ƙauyen ke kawowa ƙarshe, ma'aikata a nan sun yi imanin cewa yana zuwa a hankali tare da ƙarin farin ciki.

Wasu da cikin waɗanda aka tattauna da su sun buƙaci a sakaye sunayensu