Hajj 2024: Yadda ɗaruruwan alhazai suka rasu yayin aikin Hajjin bana

Alhazan da suka rasu

Asalin hoton, Getty Images

Sama da mutum miliyan 1.8 ne suka gudanar da aikin Hajji na bana, kuma 1.6 cikinsu baƙi ne 'yan ƙasar waje, kamar yadda mahukuntan Saudiyya suka bayyana.

Sai dai an kammala babbar ibadar ta Musulmai cikin alhini a ranar Laraba sakamakon mutuwar ɗaruruwan alhazai.

Ibadar Hajji ɗaya ce cikin rukunnan Musulunci biyar, kuma ana son duk wani Musulmi da ya samu dama ya je ɗakin Ka'aba mai tsarki don yin ta sau ɗaya a rayuwarsa.

Saudiyya ba ta bayyana adadin alhazan da suka mutu ba a hukumance, kodayake hukumomi sun ce an kai rahoton sama da mutum 2,700 da suka yi fama da bugun zafi a ranar Lahadi kaɗai.

Sai dai a cewar kamfanin labarai na AFP bayan tattara bayanai daga ofisoshin jakadancin ƙasashe, aƙalla alhazai 922 ne suka mutu yayin aikin Hajjin akasari saboda tsananin zafi da aka yi fama da shi.

Aƙalla 'yan ƙasar Masar 1,400 ne aka ba da rahoton sun ɓace cikinsu har da 600 da suka mutu, kamar yadda wasu jami'an difilomasiyya suka shaida wa AFP.

A shekarar da gabata, alhazai sama da 200 ne suka rasu kuma akasarinsu daga ƙasar Indonesia suke.

A ibadar ta wannan shekarar, an samu rahotonni na larurar tsananin zafi, da kuma ɓatan alhazai a kan mutum 27,000.

Hukumomin Saudiyya sun yi gargaɗi a ranar ƙarshe ta aikin Hajjin game da tsananin zafin, inda suka ce ya kai matakin 51.8 a ma'aunin celcious a birnin Makka ranar Litinin.

Alhazan sun rasu ne sakamakon shaƙewa saboda tsananin zafi, abin da ya jawo rashin natsuwa a tsakanin alhazai wanda shi ma ya jawo ƙarin mutuwar wasu alhazana.

Akwai 'yan nahiyar Afirka da dama da suka rasa rayukansu yayin aikin Hajjin na bana.

Alhazai a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Ƙasashen da lamarin ya fi shafa

Alhazai a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masar:

Ɗaya daga cikin jami'an difilomasiyyar Masar ya faɗa wa AFP cewa dukkan 'yan ƙasar 323 da suka mutu "tsananin zafi ne ya yi ajalinsu" ban da mutum ɗaya da aka ji wa rauni yayin turmutsutsu tsakanin alhazai.

A ranar Talata kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce ƙasar na haɗa kai da Saudiyya wajen neman alhazan da suka ɓata a bana.

Indonesia:

Jaridar Le Monde ta ruwaito ranar Talata cewa alhazai daga Indonesia 136 ne suka mutu yayin aikin Hajjin na bana, uku daga cikinsu saboda zafin rana.

Jordan:

Ita ma Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan ta sanar cewa ta ba da izinin yi wa 'yan ƙasarta 41 jana'iza a Makka kamar yadda iyalansu suka nema.

Tunisia:

Shugaban ofishin jakadancin Tunisia ya sanar da mutuwar alhazan ƙasar 23 yayin ibadar, inda ofishin ya wallafa sunayen mutanen a shafinsa na Facebook. Ya kuma gayyaci 'yan'uwan mamatan su tuntuɓe shi domin aiwatar da abubuwa na gaba.

Tun a ranar Asabar ne kuma shugaban ƙungiyar kare haƙƙi ta Tunisia, Mustafa Abdel Kebir, ya tabbatar da mutuwar alhazai biyar a Makka.

Mutum 11,227 ne suka je Saudiyya daga Tunisia domin gudanar da aikin Hajjin na bana.

Najeriya:

Hukumar kula da jin dadin alhazai kuwa ta Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu ya zuwa ranar Laraba.

Haka nan hukumar ta ce akwai wasu alhazan wadanda suka bace, ko kuma ba a san inda suke ba.

Iran:

A Iran kuma, kafar yaɗa labarai ta News Network ta ruwaito cewa alhazan ƙasar 11 ne suka mutu yayin da aka kai 24 asibiti, amma ba a ambato dalilin da ya yi ajalin nasu ba.

Moroko:

A cewar hukumomin Moroko, alhazan ƙasar biyar ne suka mutu a Saudiyya. Jakadan Moroko a Saudiyya Abdelillah Daddas ya ce sun rasu ne sakamakon "cutukan da suka daɗe suna fama da su; kamar cutar siga, da hawan jini".

A cewarsa, 'yan ƙasar kusan 34,000 ne suka je Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, 22,500 daga hukumar alhazai ta ƙasar da kuma 11,500 da suka je ƙarƙashin kamfanonin shirya tafiye-tafiye.

Senegal ta ba da umarnin a binne mamatanta a Saduiyya

Kamfanin dillancin labarai na Senegal ya ruwaito ranar Litinin cewa 'yan ƙasar uku ne suka rasu yayin aikin ibadar.

Rahotonni sun ruwaito cewa kamfanonin shirya tafiye-tafiye ne suka kai alhazan ƙasar zuwa Saudiyya.

Hakan ya sa gwamnati ta bai wa jakadanta a Saudiyya umarnin ɗaukar matakan haɗa gwiwa da hukumomin Saudiyya don ganin an binne su a inda suka mutu "kamar yadda addinin Musulunci ya tanada".

'Yan Senegal 12,860 ne suka je Saudiyya da zimmar gudanar da aikin Hajji na wannan shekara.

'Alfarma ce mutum ya mutu yayin aikin Hajji'

Duk da cewa wasu kan mayar da mamatansu zuwa gida don yi musu sutura, mafi yawa kan binne su a maƙabartocin da ke kusa da Masallacin Harami.

Wani malamin addini Umar Haruna ya faɗa wa BBC Pidgin cewa abin alfahari ne ga duku Musulmin da ya rasu yayin da yake tsaka da gudanar da aikin Hajji.

"Hasali ma, alfarma ce mutum ya mutu a ƙasa mai tsarki. Hatta 'yan'uwan ma duk da cewa suna jin alhinin rashin, ya kamata su fahimci cewa alfarma ce daga Allah," in ji shi.

A cewarsa: "Ba zai yiwu a mayar da gawar mamaci garinsu cikin awa 24 ba, saboda sai a binne ta a Saudiyya."

Shi ma jakadan Moroko a Saudiyya Abdelillah Daddas ya faɗa yayin wata hira a gidan rediyo cewa: "Game da alhazan Moroko da suka mutu, z a iya binne su a nan ko kuma a mayar da su gida. Amma dai kashi 99 cikin 100 na iyalai kan zaɓi a binne 'yan'uwansu a nan saboda tsarki da falalar wurin."

An tanadi maƙabartu na musamman domin binne alhazan da suka rasu yayin aikin Hajji. Daga cikinsu akwai Jannat Al-Mala da ke Makka, da Jannat Al-Baqi a Madina, da Al-Adl, da Al-Haram, da Al-Rabway, da kuma makabartar Arafa.