Waiwaye: Dakatar da Betta Edu da shari'o'in wasu gwamnoni a Kotun Ƙoli

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin mako da muke bankwana da shi

Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu

An shiga makon da ya gabatan ne da labarin dakatar da ministar ayyukan jin-ƙai da yaƙi da fatara ta Najeriya, Betta Edu.

Shugaban kasar ne Bola Tinubu ya sanar da dakatar da ministar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin.

Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.

Tun farko al'ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen badaƙar kuɗaɗen ma'aikatar da ake yi mata.

Sadiya Umar Farouq ta miƙa kanta ga EFCC

Jim kaɗan bayan sanar da sallamar Betta Edu, sai tsohuwar ministar jin-ƙan a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ta miƙa kanta ga hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC domin amsa tambayoyi.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na X, tsohuwar ministar ta ce ta amsa gayyatar da EFCC ta yi mata ne domin warware waɗansu batutuwa da hukumar yaƙi da rashawan ke bincike a kai.

A makon da ya gabata ne, EFCC ta gayyaci Sadiya Farouq domin neman bahasi game da zargin almundahanar biliyoyin naira da gwamnati ta ware domin yaƙi da talauci a Najeriya.

Tinubu ya rage yawan masu rakiya a tafiye-tafiyensa

A ranar Talatan makon da ya gabatan ne dai shugabanNajeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rage yawan jami'an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai yi a ciki da wajen ƙasar.

Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami'an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar cikin makon da ya gabatan, Tinubun ya ce matakin wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami'an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.

Matatar mai ta Dangote ta fara aiki

Haka dai a makon da muke bankwana da shi ɗin ne kuma matatar mai ta Dangote ta fara aikin tace ɗanyen man fetur.

Babbar matatar da ke birnin Legas ta fara aikin ne bayan kammala ta tare da ƙaddamar da ita a watannin da suka gabata.

Matatar ta fara aikin ne bayan tara kimanin ganga miliyan shida na ɗanyen man fetur a wannan makon

Tinubu ya dakatar da shirye-shiryen tallafin dogaro da kai na NSIP

A ƙarshen makon ne kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da dakatar da duka shirye-shiryen yaƙi da talauci na hukumar NSIPA da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gamnatin ƙasar ta ce an ɗauki matakin ne domin gudanar da bincike kan zargin badaƙa tsakanin jagorancin hukumar da kuma yadda take gudanar da shirye-shiryenta.

Sanarwar ta ce an dakatar da duka shirye-shirye huɗu da hukumar ke jagoranta, kama daga shirin N- Power, da biyan kuɗaɗen tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi da tallafa wa masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i da shirin ciyar da ɗaliban makarantun firamare.

Sanarwar ta ƙara da cewa a matakin farko dakatarwar ta mako shida ne, kafin a kammala bincike kan batun.

Za a ƙara yawan jami'an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna - IGP

Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya bayar da umarnin ƙara yawan jami'an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna, a wani mataki na tsaurara matakai domin inganta zaman lafiya da tsaro a kan titin.

Da yake nuna muhimmancin samar da tsaro domin zirga-zirga a yankin, babban sifeton 'yan sandan ya ce za a ƙara girke ƙarin jami'an 'yan sanda da kayan aiki, musamman kayan fasahar zamani da sauran dabarun aiki don inganta tsaro a kan titin.

Mista Egbetokun ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar 'yan ƙasa da fasijoji.

Shari'o'in wasu gwamnoni a kotun ƙoli

A ƙare makon kuma da shari'o'in wasu gamnonin jihohin Najeriya da aka kammala a kotun ƙolin ƙasar.

Kotun dai tabbatar da nasarar duka gwamnonin da aka ƙalubalanta ko suka ƙalubalanci hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a gabanta.

Daga ciki har da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wanda kotun ta tabbatar da nasararsa bayan kotun ɗaukaka ƙara ta soke nasararsa.