Ba za mu bari a zalunci arewa ba - Ali Ndume

Ali Ndume

Asalin hoton, Senate

Ƙudurin gwamnatin Najeriya na mayar da hukumar kula da filayen jirgin sama ta ƙasar (FAAN) da wasu cibiyoyin babban bankin ƙasar (CBN) zuwa Lagos daga Abuja, yana ci gaba da shan suka da fuskantar ƙalubale.

Cikin 'yan kwanakin nan 'yan majalisar dokoki daga yankin arewacin ƙasar, sun nuna rashin amincewarsu da ƙudurin inda suke iƙirarin cewa matakin ɗauke ofisoshin, zai mayar da wasu yankunan ƙasar baya, tare da haddasa ka-ce-na-ce.

Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan ƙasar Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatin ta ɗauka ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ya tanadar cewa Abuja ce birnin tarayya kuma a nan ya kamata a ce duk wata hedikwatar ma'aikatar gwamnati take, kuma samun akasin haka zai iya cutar da yankin arewacin ƙasar.

Daga cikin dalilan da gwamnatin ta bayar na ɗaukar wannan matakin shi ne rage cunkoso a ma'aikatun gwamnati da ke Abuja, wanda ta ce yana kawo naƙasu wajen yadda ake gudanar da ayyuka a ma'aikatun. Amma Sanata Ndume ya ce hakan ba dalili ba ne, 'A duk Najeriya babu inda ya kai Lagos cunkoso, idan ana gudun cunkoso ne, a cikin Abuja akwai fili ko ta ina, a cikin hukumomin gwamnati waɗanda aka rage su ma suna da hedikwata da za a iya amfani da su idan har cunkoso ake son a rage'. In ji shi

Ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta yi adalci a duk wani mataki da za ta ɗauka saboda ka da kowanne ɓangare su ga kamar ana neman a muzguna masu.

Sanatan ya ce, 'Ina da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai yarda a zartar da wani matakin gwamnati da zai cutar da wani ɓangare ba, kuma mu 'yan majalisa na arewa ba za mu zauna muna gani a cutar da ɓangaren da muke wakilta ba, idan mun yi haka yana nufin ba mu yi aikinmu yadda ya kamata ba. Dole ne a yi mana adalci kuma adalcin nan shi ne a bar hukumomin nan a inda suke a hadikwtar ƙasa. ba mu amince a zalunce mu ko ta wani hanya ba kuma mu ma ba za mu zalunci kowa ba'.

Wannan dai shi ne karo na biyu da wata ƙungiyar Arewa za ta yi Allah-wadai da sauya wa hukumomin gwamnatin tarayyan biyu matsuguni.

A baya dai ƙungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta soki wannan lamarin, inda ta ce wannan matakin zai haifar da rashin cigaban yankin arewacin ƙasar.

Game da batun kasafin kuɗin 2024 da wasu ke ganin kamar an fifita wani ɓangaren ƙasar, Sanata Ndume ya yi bayanin cewa 'yan majalisa za su yi nazarin kasafin kuɗin da nufin gano yadda aka kasafta kudaɗe tsakanin ɓangarorin ƙasar domin su tabbatar da cewa an yi adalci.

Ya ce: 'Idan mun duba mun ga an yi rashin adalci za mu duba hakkin da ya rataya a wuyanmu na wakiltar jama'a, kuma za mu tabbatar cewa ba a cuce mu ba kuma mu ma ba mu cuci kowa ba,'