Buƙatar gina wa mataimakin shugaban Najeriya sabon gida ya tayar da kura

Buƙatar gina wa mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, sabon gida na ci gaba da tayar da ƙura a kasar.
Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ne ya bukaci majalisar dattawan kasar ta amince da gina wa mataimakin shugaban kasar sabon gida wanda ake sa ran za a kashe kudi har naira biliyan 15.
Kungiyoyi masu rajin tabbatar da mulkin adalci da gaskiya na daga cikin wadanda suka yi kira ga majalisar dattawan ƙasar a kan ta ƙi amincewa da buƙatar ministan birnin tarayyar.
Wata wasiƙa da ƙungiyoyin suka aike wa shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, ta yi kiran ya soke wannan buƙata a cikin kasafin ƙudin da ke gaban majalisar don kuwa ya saɓa wa tanadin mulkin adalci.
Auwal Musa Rafsan Jani shugaban kungiyar CISLAC, mai sanya ido a kan ayyukan majalisu da kuma yaki da rashawa a Najeriyar, ya shaida wa BBC cewa, wannan "wata dama ce ake nema ta wawure dukiyar kasa."
Ya ce,” Muna kira ga ‘yan majalisa a kan kada su yarda su ci amanar ‘yan Najeriya su amince da wannan kuduri don bai dace ba, saboda idan aka yi hakan za a sanya mutane cikin azaba ga kuma ranto kudi da ake yi.”
“Don haka bai dace ace ana ranto kudade ana wasu abubuwan da ba su dace ba, don mu abin da muka fahimta tun da wannan gwamnatin ta zo babu abin da ta ke ban da ranto kudade tana kashe su a wuraren da ba su da alaka da gyaran kasa ba.”
Auwal Musa Rafsanjani, ya ce, “Ya kamata ‘yan majalisar su yi zazari sosai a kan wannan bukata ta ministan birnin tarayyar don sam ba ta dace ba.”
Kungiyoyin dai sun bukaci shugaban majalisar dattawan da ya yi amfani da karfin ikon da mulkin kasa ya ba shi na sa ido da bibiyar ayyukan gwamnati wajen tabbatar da wannan bukata ba ta kai ga nasara ba.
Nyesom Wike, ya gabatar da bukatar gina sabon gida ga mataimakin shugaban Najeriyar ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar wakilai don kare kasafin kudin birnin tarayyar inda ya ce tun a 2010 majalisar zartarwar Najeriya ta amince da yin aikin a kan kudi naira biliyan bakwai, amma daga baya aka yi watsi da aikin.
A yanzu haka Nyesom Wike, ya sha alwashin gudanar da wannan aiki, kuma ya shaida wa majalisar cewa a wannan karon ‘yan kwangilar za su yi aikin ne a kan kudi naira biliyan 15.
Lamarin da kungiyoyin ke ganin cewa bai dace a aiwatar da aikin ba a wannan irin halin kuncin da al’ummar Najeriya ke ciki.











