Rashin kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma laifin Faransa ne?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Leonard Mbulle-Nziege da Nic Cheeseman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Masu sharhi a Afirka
Nijar ce ta ƙasa ta baya-bayan nan da sojoji suka ƙwace mulki a Afirka ta Yamma bayan Burkina Faso, da Guinea, da Mali, sai kuma Chadi - dukkansu waɗanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Tun daga 1990, kashi 78 cikin 100 na juyin mulki 27 da aka yi a ƙasashen baƙar fatar Afirka sun faru ne a ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Hakan ya sa masu sharhi ke ɗiga ayar tambaya: Shin Faransa - ko kuma tsare-tsaren mulkin mallaka - za a zarga da haddasa hakan?
Akasarin masu juyin mulkin abin da za su so mu yarda ke nan. Kanar Abdoulaye Maiga, wanda aka naɗa firaminista a Mali a Satumban 2022 bayan juyin mulki, ya ƙaddamar da yaƙin adawa da Faransa.
Mista Maiga ya soki Faransa da cewa "'yan mulkin mallaka na zamani, masu girman kai, masu take haƙƙi da kuma tsar-tsaren ramuwar gayya", sannan ya ce ƙasar ta "yi fatali da ɗabi'u na gari" kuma "ta ci amanar Mali".
Kazalika, ana ci gaba da ƙin jinin Faransa a Burkina Faso, inda sojojin juyin mulki suka katse daɗaɗɗun yarjejeniyoyi da suka ƙulla da Faransa waɗanda suka ba ta damar jibge dakarunta a watan Fabrairu, kuma suka ba wa Faransar wa'adin wata ɗaya kacal ta fice.
A Nijar, wadda ke maƙwabtaka da ƙasashen biyu, an yi amfani da zargin cewa Mohamed Bazoum karen farautar Faransa ne wajen halasta juyin mulkin da aka yi masa, kuma tuni sojojin suka soke yarjejeniyoyin soja da Faransa biyar.
Wani ɓangare na tarihi na goyon bayan wannan ra'ayi. Tsarin mulkin mallaka na Faransa ya ba da damar kwasar albarkatun ƙasa daga ƙasashe ta hanyar amfani da matakai na rashin imani.
Haka ma tsarin mulkin Birtaniya, amma abin da ya bambanta su shi ne yadda Faransa ta ci gaba da mu'amala - masu sukarta kuma su ce kutse - a harkokin siyasa da tattalin arzikin ƙasashen bayan samun 'yancin kai.
Bakwai daga cikin ƙasashen Afirka ta Yamma da Faransa ta yi wa mulkin mallaka har yanzu suna amfani da kuɗin CFA, wanda aka tsago darajarsa daga kuɗin yuro, wanda yana ɗaya daga cikin tsare-tsaren Faransa kan ƙasashen.
Haka nan, Faransa ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da ta ba ta damar kutsa kai da dakaru a ƙasashen don tabbatar da mulkin shugabannin da ke yi mata biyayya.

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokuta da dama, hakan na ƙarfafa wa 'yan kama-karya gwiwa kamar tsohon Shugaban Chadi Idriss Deby, da kuma tsohon Shugaban Burkina Blaise Compaoré, abin da yake ƙara zafafa gwagwarmayar neman dimokuraɗiyya.
Duk da cewa Faransa ba ta yi yunƙurin mayar da duka waɗanda aka kifar ba a kwanan nan, ana yi musu kallon "yaran Faransa".
Bugu da ƙari, alaƙar shugabannin Afirka da Faransa cike take da cin hanci, wanda hakan ke ƙara jefa 'yan ƙasashen cikin matsin rayuwa.
Shahararren masanin tattalin arziki a Faransa, François-Xavier Verschave, ya ƙirƙiiri kalmar Françafrique don siffanta mu'amalar Faransa ta mulkin mallakar a zamanance a matsayin "ɓoyayyen laifin da manyan 'yan siyasar Faransa ke yi".
A cewarsa, wannan alaƙar ta sa ana "almubazzaranci" da kuɗaɗe masu yawa.
Duk da cewa gwamnatocin Faransa na baya-bayan nan na nesanta kan su daga Françafrique, har yanzu gurɓatacciyar alaƙa tsakanin Faransa da kadarorinta da kuma Afirka a bayyane take ƙarara, ciki har da wasu lamurran cin hanci na abin kunya.
Saboda haka abu ne mai sauƙi mu fahimci dalilin da ya sa wani ɗan Nijar ya faɗa wa BBC cewa: "Tun ina yaro nake adawa da Faransa...Sun kwashe duk arzikin ƙasata kamar makamashin uranium."
Ana yawan ɓoye ire-iren waɗannan badaƙalar yayin da su kuma 'yan siyasar Afirka masu goyon bayan Faransa ke ci gaba da azurta kan su, su kuma dakarun Faransa su taimaka musu ci gaba da zama a kan mulki.
A 'yan shekarun nan, yunƙurin Faransa da sauran ƙasashen Yamma na tabbtar da ƙarfin ikonsu ya gagara, inda suke ci gaba da fuskantar suka.
Duk da yawan kuɗi da na dakaru, sojojin ƙawance da Faransa ke jagoranta a yaƙi da masu iƙirarin jihadi sun kasa taimaka wa gwamnatocin ƙasashen Afirka ta Yamma su ƙwato garuruwansu daga hannun 'yan bindigar.
Wannan lamari ya fi ƙamari a kan shugabannin Mali da Burkina Faso saboda gazawarsu wajen kare rayukan 'yan ƙasa ta sa ake ganin kamar zaman dakarun Faransa a ƙasashen nauyi ne maimakon taimako.
A madadin haka, ƙaruwar ɓacin rai da kuma gajiyawa ta sa jagororin soja ke tunanin idan suka yi juyin mulki 'yan ƙasa za su yaba musu.
Sai dai kuma, ba zai yiwu a ɗora alhakin duka abin da ke faruwa ba a yankin a kan Faransa duk da irin kura-kuren da ta yi.
Ba ita kaɗai ce 'yar mulkin mallaka ba da ta taimaka wajen rainon shugabanni 'yan kama-karya.

Asalin hoton, EPA
Lokacin yaƙin cacar-baka, Birtaniya da Amurka sun taimaka wajen rainon 'yan kama-karya da yawa don neman goyon bayansu, kamar Daniel arap Moi na Kenya, da Mobutu Sese Seko da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Sannan ba a fiya samun alaƙa ba tsakanin juyin mulki da kuma ƙasashen mulkin mallaka a baya. Ƙasashe huɗu da suka fi saura fuskantar juyin mulki daga 1952 su ne Najeriya (8), Ghana (10), Saliyo (10), da kuma Sudan (17), dukkansu ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya.
Yayin da ake ci gaba da yayin juyin mulki a ƙasashen da Faransa ta bari da kuma alamun tsarin Françafrique a ƙasashen, lamarin na ƙaruwa ne saboda matsalar tsaro da take mamaye yankin Afirka ta Yamma da kuma Sahel.
A Mali, juyin mulkin ya biyo bayan kwarar 'yan bindiga bayan faɗuwar gwamnatin Libya ƙarƙashin Gadafi a 2011.
Da alama abin da ya haifar da juyin mulkin Nijar na da alaƙa da yunƙurin Mohamed Bazoum na yi wa rundunar sojan ƙasar garambawul, wanda zai sa a cire Janar Tchiani daga muƙaminsa.
Wannan alama ce da ke nuna ba a kifar da gwamnatinsa don kishin ƙasa ba, ko taimaka wa talakawa, sai dai don kare buƙatun jagororin soji.
A taron ƙasashen Afirka da Rasha da aka kammala kwanan nan, shugabannin Burkina Faso da Mali sun ayyana goyon bayansu ga Shugaba Putin da kuma yaƙin da yake yi a Ukraine.
Kamar a baya, waɗanda za su fi amfana da wannan alaƙar 'yan siyasa ne fiye da 'yan ƙasa. Da ma akwai rahotannin da ke cewa a watan Mayu, dakarun ƙungiyar Wagner ne ke da alhakin kasheewa da azabtar da ɗaruruwan fararen hula a yaƙin da suke yi da 'yan bindiga.
Rage tasirin Faransa ba abu ne mai sauƙi ba a wajen 'yan siyasa, kuma a shekaru masu zuwa akwai yiwuwar mu ga wasu sojojin sun yi juyin mulki saboda su yanke alaƙa da Rasha.
Leonard Mbulle-Nziege mai bincike ne a cibiyar Institute for Democracy, Citizenship and Public Policy in Africa da ke Jami'ar Cape Town, Nic Cheeseman shugaban cibiyar Centre for Elections, Democracy, Accountability and Representaton da ke Jami'ar Birmingham.











