Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ‘yan Zamfara ke fargabar sake rikicewar lamuran tsaro a yankunansu
Al’ummar wasu yankunan Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na nuna fargaba dangane da yiwuwar sake tabarbarewar matsalolin tsaro, tun bayan hare-haren da sojoji suka kai wa dabar kasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji.
Galibin mazauna jihar musamman yankin arewaci na cewa tun bayan hare-haren sojoji lamuran tsaro sun sake rincaɓe musu, musamman a kan titin Shinkafi, bayan hare-haren ramuwa da yaran Bello Turji suka kai.
A karshen makon da ya gabata ne jirgin saman sojin Najeriya ya kai wasu jerin hare-hare kan sansanin Bello Turji da ke daji, har rahotanni ke cewa an kashe wasu yaransa da dama.
An ce dan fashin ya sha da kyar, kuma tun bayan wannan harin ake zargin yaransa da kai harin huce haushi kan matafiya a masarautar Moriki da kuma wadanda ake tarewa a titin Kauran Namoda zuwa Shinkafi.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
Me ake cewa?
Dan madamin Shinkafi, Alhaji Aliyu Moye ya shaida wa BBC cewa a gabar da ake a yanzu ba sa bukatar a yi fito na fito da kasurgumin ɗan fashin dajin.
Ya ce sojojin sun gama nasu sun tafi, an bar matafiya da masu bin hanyar cikin wahala da fargaba.
Sannan ya ce yanzu hanyar Shinkafi zuwa Gusau ta zama bala’i a garesu.
"Ga shi muna fargaba ba lallai a ci kasuwar Shinkafi ba, saboda kowa na tsoro. Gona ma mutane na tunanin ba lallai su koma gona girbi ba."
Aliyu Moye, ya ce kafin wannan lokaci da aka yi sulhu da ɗan fashin dajin, suna cikin kwanciyar hankali saboda ‘yan bindiga sun daina taɓa su ko da kuwa sun haɗu ne a gonaki.
A cewarsa, suna ta mu’amala har da Turji ana haɗuwa da shi baya taɓa mutane.
Sai dai akwai wadanda ra’ayinsu ya sha bamban da wannan, inda shi ma wani da BBC ta zanta da shi ke cewa ai ba a tuba da makami a hannu.
Mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce har yanzu Bello Turji na kwashe mutane da tilasta musu yi masa noma da karfi babu abinci.
Kuma idan ɗan bindigar ya yaƙi ɓarayin daji da ya fi karfi shi ke ƙwace duk abin da ke hannunsu.
"Idan ya ƙwace kayayyaki a daji me ya sa baya kai wa gwamnati ta nemi masu kaya ta ba su, kawai dai ya ce ya tuba ne saboda ya more tarin dukiyar da ya yi fashinsu, hankali kwance."
Sannan ya ce shi ya goyi bayan gwamnatin tarayya ta kashe shi a huta.
‘Akwai sarkakkiya cikin tuban Turji’
Amma masana irinsu Abdullahi Yalwa na cewa sulhu da irin waɗannan mutane akwai sarkakiya.
Ya ce, saboda kana iya sulhu kuma su bada mamaki daga baya.
Sama da shekara 10 jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan fashin daji da ya haddasa asarar rayuka da dimbin dukiya.
Kuma tun daga wannan lokaci ana samun gwamnatoci daban-daban da ke yakar matsalar da har yanzu aka gagara kawo karshenta.