Wane ne Boakai - Sabon shugaban Laberiya da zai maye gurbin George Weah

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Joseph Boakai, ɗan jam'iyyar adawa mai shekaru 78, wanda ya bayyana shekaru a matsayin ''albarka'', ya samu sakon taya murna daga shugaban ƙasar Laberiya da suka fafata a zaɓen shugabancin ƙasa.
Sakamakon zaɓen na baya-bayan nan ne ya ba shi nasara kan fitaccen ɗan wasan kwallon kafa George Weah a zaɓen da aka gudanar cikin tsaro tun bayan kawo karshen yaƙin basasar ƙasar.
Masu suka dai na kiransa da "Sleepy Joe" bayan rahotannin sun bayyana ya yi barci yayin bukukuwan da aka shirya a hukumance, amma Mista Boakai ya yi alkawarin dawo da fata, kima da kuma darajar Laberiya.
Bayan ya shafe shekaru 12 yana mataimakin shugaban ƙasa a karkashin Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da ta zama shugabar ƙasa a Afirka, yana da masaniya kan harkar tafiyar da ƙasa.
A watan Janairun 2024 ne za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a hukumance.
Mista Boakai ya ayyana kansa a matsayin "motar tsere da ke ajiye cikin gareji," wata kalma da ta yi tashe lokacin zaɓukan 2017, wanda ya sha kaye a hannun Mista Weah a lokacin.
Ya ce kwatanta kansa da kalmar yana da alaƙa da zimmarsa na ganin yayi aiki tukuru a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Shafinsa na intanet ya saka jerin nasarori 58 da ya kawo, ciki har da yin gwagwarmaya don samar da kwalejojin al'umma da kuma sasanta rikice-rikice a faɗin Laberiya.
Babban nasarar da ya samu lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa, shi ne samun zaman lafiya a tsawon mulki, bayan samun yaƙi na kusan shekaru 15.
Samun rayuwa mai inganci
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haife shi a watan Nuwambar 1944, a cikin abu da mutane suka kira mafara mai kyau.
Joseph Boakai ya girma a wani ƙauye mai suna Worsonga, da ke arewacin lardin Lofa.
Iyayensa ba su iya karatu ko rubutu ba.
Mista Boakai ya fara karatu a wata makaranta a Saliyo mai makwabtaka, inda ya kammala a Kwalejin Yammacin Afirka, da ke Monrovia, babban birnin Laberiya.
Daga nan ya tafi gaba inda ya karanta fannin kasuwanci a Jami'ar Laberiya.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan rediyo, Mista Boakai ya ce a matsayinsa na matashi, ya tashi daga ƙauyen Worsonga zuwa babban birnin ƙasar domin samun rayuwa mai inganci.
Boakai da matarsa Kartumu suna da ƴaƴa huɗu. Ya kasance fasto a majami'ar Effort Baptist.
A shekarun 1980, Mista Boakai ya kasance a matsayin ministan aikin gona karkashin shugaba Samuel Doe, wanda aka yi wa kisan gilla a 1990.
Ɗaya daga cikin ayyukan da ya yi a ƙauyensa, shi ne gina hanya mai nisan kilomita 11.
Ya kuma yi aiki da wasu mutane wajen gina makaranta wa ɗalibai 150 da kuma asibiti wa ƙauyyuka goma.
Mista Boakai ya kuma jagoranci shirin faɗada ayyukan gona ta hanyar kirkiro da cibiyoyin noma a yankuna - inda manoma da dama suka samu alfanu.

Asalin hoton, REUTERS
Bayan shan kaye a zaɓukan 2017, Mista Boakai ya cika da zimmar ci gaba da nema.
A zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a wannan karo, babu wanda ya samu kuri'u sama da kashi 50 don lashe zaɓe tsakanin Boakaida Weah, abin da ya janyo a tafi zagaye na biyu.
A Yaƙin neman zaɓe, Mista Boakai ya mayar da hankali kan ɓangaren noma, yayin da ya zargi gwamnatin shugaba Weah da almubazzaranci.
Sai dai Mista Weah ya yi watsi da zarge-zargen Mista Boakai.
Da yake tattaunawa da BBC game da abin da yake son cimmawa idan ya samu nasara kafin zaɓe, Boakai ya bayyana cewa yana son mayar da hankali kan yaƙi da cin hanci da rashawa, bunƙasa aikin gona, rage farashin kayan abinci da kuma kyautata yanayin hanyoyi a faɗin ƙasar.
Ya c: "Mutanen mu na son samun ƙasa da za su yi alfaharin kira ƙasarsu, ƙasar da za su mutunta, amma cin hanci da rashawa na kawo cikas kan hakan."
Ya yi alkawarin cewa za a ja layi tare da hukunta masu aikata rashawa.
"A kwanakin 100 na farko, za mu tabbatar da cewa babu abin hawa da zai maƙale a cikin laka. Hakan zai shafi farashin kayan abinci da kuma lafiyar mutane."
Sabon zaɓabɓen shugaban ƙasar ta Laberiya ya kuma yi alkawarin yin bincike kan dalilai da suka saka farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, inda ya ce zai taimaki manoma.
"Muna da albarkatu a ɓangaren noma a ƙasar nan sai dai babu abin da aka yi a ɓangaren. Mun dogaro da abubuwan da ake shigo da su daga waje. Hakan zai sauya. Na san za mu yi hakan."
Mista Boakai ya kwatanta hnayar da ya bi har zama shugaban ƙasa a matsayin mai tsawo, sai dai ya ce yana da zimmar son ganin ya taimakawa miliyoyin ƴan Laberiya waɗanda suke fama da talauci, cutuka da kuma rashin tsaro.











