Sunak ya jaddada goyon bayan sa ga Ukraine kan mamayar Rasha

Rishi Sunak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sunak da Zalensky sun tattauna da wayar tarho

Sabon Firaiministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya yi alkawarin ci gaba da taimaka wa Ukraine, kamar yadda ya shaida wa shugaba Volodymyr Zelensky ta wayar tarho.

Ya ce ya na fatan za su gana da juna nan ba da jimawa ba.

Sunak, ya ce a shirye Birtaniya ta ke, domin tabbatar da tallafa wa Ukraine kan halin da ta samu kan ta a ciki a hannun Rasha.

Mista Zelensky, ya wallafa a shafinsa na Tiwita, cewa kasashen biyu sun bude sabon babin alaka. Mr Sunak ya kuma tattauna da shugaban Amurka Joe Biden, ta wayar tarhon, duk dai kan batun mamayar Rasha a Ukraine da hadin gwiwar taimaka mata.

Tun da fari masana sun bayyana Sunak zai fuskanci matsaloli da dama da zarar ya fara aiki, ciki kuwa har da yakin Ukraine da karancin makamashin da ya shafi duniya, musamman ma kasarsa.