Su wa Trump zai bai wa muƙamai a gwamnatinsa bayan Susie Wiles?

Wasu da ke ganin za su samu muƙamai

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Tuni dai kwamitinnkarɓar mulki na Donald Trump ya fara tantance mutanen da ake ganin za su iya shiga sabuwar gwamnatin, idan ya karɓi mulki cikin watan Janairu mai zuwa.

A ranar alhamis, ya sanar da naɗin farko a sabuwar gwamnatin tasa, inda ya bayyana shugabar yaƙin neman zaɓensa, Susan Summerall Wiles a matsayin shugabar ma’aikatan fadar White House.

Mafi yawan man ƙusoshin da suka yi aiki ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin Trump a wa'adinsa na farko ba su da shirin komawa fadar ta White House, kodayake ana raɗe-raɗin wasu tsirarun masu biyayya za su sake dawowa.

Ga wasu sunayen da ake kyautata zaton za su shiga a dama da su a sabuwar gwamnatin.

Robert F Kennedy Jr

Robert F Kennedy Jr

Asalin hoton, Reuters

Shekaru biyun da suka gabata, sun yi wa ɗan ɗan'uwan tsohon shugaban Amurka John F Kennedy kyau.

Lauyan na kare muhalli ya tsaya takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Demokrats, inda mafi yawan iyalansa ke nuna adawa da ra'ayinsa na adawa da rigakafi, yayin da suka amince da sake zaben Joe Biden.

Daga nan ne ya koma ɗan takara mai zaman kansa, amma ya kasa samun magoya baya sakamakon abubuwa da dama.

Daga ƙarshe kuma ya janye daga takarar tare da mara wa Trump Baya.

A baya-bayan na Trump ya ce Mista Kennedy Jr zai taka muhimmiyar rawa a gwamnatinsa musamman shugabancin hukumomin da suka shafi lafiya, kamar Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta ƙasar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna.

Elon Musk

Elon Musk

Asalin hoton, Reuters

A farkon wannan shekarar Hamshaƙin attajirin duniyar, ya ayyana goyon bayansa ga tsohon shugaban ƙasar, duk kuwa da cewa a 2022 ya ce ''lokaci ya yi da Trump zai rataye malafarsa ta siyasa''.

Tun daga lokacin ne biloniyan ya zama ɗaya daga manyan masu goyon bayan takarar Mista Trump, waɗanda kuma suka bayar da tallafin kuɗaɗe masu yawa.

Musta ya bayar da tallafin fiye da dala miliyan 119 ga takarar Mista Trump.

Duka Musk da Trump sun mayar da hankali kan Musk ya jagoranci sabon ''sashen kula da manufofin gwamnati'', wanda zai rage kashe kuɗaɗen gwamnati da kawo sauye-sauye kan wasu dokokin kula da aikin gwamnati

Mike Pompeo

Mike Pompeo

Asalin hoton, Reuters

Tsohon ɗan majalisar na Kansas ya taɓa riƙe muƙamin daraktan a hukumar leƙen asirin ƙasar ta CIA, sannan ya zama sakataren harkokin wajen Amurka lokacin gwamnatin Trump.

Ya kasance mai kare muradin ubangidan nasa. Ana ganin shi ne zai zama sakataren tsaron ƙasar.

Kodayake ana alaƙanta muƙamin ga Michael Waltz, ɗan majalisar jihar Florida kuma tsohon soja, wanda ya kasance cikin kwamitin tsaro na majalisar wakilan ƙasar.

Richard Grenell

Richard Grenell

Asalin hoton, Reuters

Richard Grenell ne ya riƙe muƙamin jakadan Amurka a Jamus a lokacin mulkin Trum na farko, sannan daga baya ya riƙe muƙamin daraktan riƙo a ma'aikatar leƙen asirin ƙasar.

Ɗan jam'iyyar ta Republican ya taimaka wa yunƙurin Trump na soke sakamakon zaɓen 2020, a jihar Nevada, wadda ke ciki jihohi marasa tabbas.

Trump ya yaba wa biyayyar Grenell, sanna ya kira shi da ''jakadana''

Ana ganin shi ne zai kasance sakataren harkokin wajen ƙasar, ko babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wani muƙami da ba ya buƙatar tantancewar majalisar dattawa.

Karoline Leavitt

Karoline Leavitt

Asalin hoton, Reuters

Sakatariyar yaɗa labaran gangamin yaƙin neman zaɓen Trump na 2024, a baya ta riƙe muƙamin mataimakiyar sakataren yaɗa labaran fadar White House.

Mai shekara 27, ta yi yunƙurin zama mace mafi ƙanƙantar shekaru da aka zama a majalisar wakilan ƙasar a 2022, domin wakiltar jiharta ta New Hampshire, amma ba ta samu nasara ba.

Ana ganin ita ce za ta zama sakatariyar yaɗa labaran fadar White House - muƙamin da ya fi kowane hulɗa da jama'a cikin kusoshin gwamnati.

Tom Homan

Tom Homan

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin wa'adin Trump na farko, Tom Homan ya riƙe muƙamin daraktan riƙo a hukumar shige da ficen Amurka, inda ya yi ƙoƙarin raba yaran 'yan ci rani da iyayensu a matsayin wata hanya ta daƙile kwararar baƙi ta ɓarauniyar hanya.

Daga baya ya yi murabus daga mukaminsa a 2018, a lokacin tsakiyar mulkinshugaba Trump.

Tun daga lokacin ya fito a matsayin babban jigo na inganta shirin korar baƙin haure na Trump, kuma ana ganin shi ne zai jagoranci ma'aikatar tsaron cikin gida.