An tuntuɓe ni kan tsawaita zama na a Liverpool - Van Dijk

Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin Virgil van Dijk ya ce Liverpool ta tuntuɓe shi, kan maganar tsawaita ƙwantiraginsa a Anfield, domin ya ci gaba da taka mata leda.

Yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 33, za ta kare a karshen kakar bana, wanda ya sanar a cikin watan Maris cewar bai sani ba ko zai ci gaba da zama a ƙungiyar.

Mai tsaron bayan, yana daga cikin fitattu uku daga Liverpool da yarjejeniyarsu za ta karkare a karshen kakar nan, har da Mohamed Salah da Trent Alexander-Arnold.

Lokacin da aka yi masa tambaya, bayan tashi wasan Premier da Fulham ta ci Liverpool 3-2 ranar Lahadi sai ya ce ''Akwai damar zai ci gaba da taka leda a Anfield.

''Mun ci gaba da tattaunawa da mahukunta, ana samun ci gaba,'' inji ƙyaftin na tawagar Netherlands.

''Ban sani ba ko zan ci gaba da zama a Liverpool, amma dai muna tattaunawa kan batun, sai dai mu jira muga abin da zai faru nan gaba.''

''Ina ƙaunar Liverpool da magoya bayanta, waɗanda kullum suke tare da mu, hakan ne ya sa muke fatan ci gaba da faranta musu.

Liverpool tana matakin farko a kan teburin Premier League da tazarar maki 11 tsakani da Arsenal ta biyu, duk da rashin nasara a gidan Fulham ranar Lahadi.

Rashin nasara da Liverpool ta yi a Craven Cottage, shi ne na biyu a bana a Premier League, kuma na farko bayan wasa 26 a jere a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Van Dijk ya koma Liverpool kan yarjejeniyar £75m daga Southampton a 2018.

Ya ci ƙwallo 26 a wasa 323 a Liverpool, wanda ya yi fice karkashin Jurgen Klopp da lashe Premier League da Champions League da FA Cup da kuma EFL Cup sau biyu..