Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaratan ƴanƙwallo 10 da Messi da Cristiano suka hana lashe Ballon d'Or
A duniyar ƙwallon ƙafa, za a iya cewa an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa wajen ganin fitattu kuma gwarazan ƴanƙwallon ƙafa da suke zuwa su yi lokaci, sannan su shuɗe.
A duk lokacin da wasu suka shuɗe, ana samun wasu su biyo bayansu, su maye gurbinsu, har ma su rufe wasu tarihinsu da suka kafa a harkar ta tamaula, sannan su ɗaura.
Ana dai ganin a duk lokacin da ake maganar gwanancewa a ƙwallon ƙafa, akan yi amfani da kambun Ballon d'Or domin domin nuna wanda ya zama zakarar gwajin dafi.
Wannan ya sa masoya Lionel Messi suke cewa shi ne gwarzon ƙwallon ƙafa da babu kamarsa, duk da cewa masoya Cristiano Ronaldo suna cewa gwarzonsu yana sama da Messi, wanda hakan ke haifar da zazzafar muhawara a tsakaninsu.
A baya an yi hamayya da muhawara mai zafi tsakanin wane ne gwani na gwanaye tsakanin Pele da Maradona, amma yanzu wataƙila saboda ƙaruwar kafofin sadarwa, muhawara tsakanin magoya bayan Messi da Ronaldo ya fi zafi.
Haka kuma an yi zaratan ƴanƙwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu.
A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d'Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017.
Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun zo na uku sau ɗaya.
Hakan ya sa ake ganin kamar ƴanwasan biyu sun hana wasu fitattun ƴanwasan yin rawar gaban hantsinsu.
Wannan ya sa BBC ta kalato wasu fitattun ƴanƙwallo da suka yi zamani tare da gwanayen ƴanwasan, waɗanda ake tunanin sun tare musu gaba, har suka kasa lashe kambun Ballon d'Or ballantana su samu shiga cikin zaratan ƴanƙwallon duniya duk da suma gwanaye ne.
Andrés Iniesta
Andrés Iniesta ɗanwasan ƙasar Spain ne da ya yi tashe tare da Xavi da Messi a Barcelona, inda suka lashe kofuna da dama.
A lokacin da yake tashe tare da Xavi da Bosquets, sai da ya zama ana ganin babu ƙungiyar da take da ƴanwasan tsakiya kamar Barcelona.
Tsohon ɗanwasan mai shekara 40 a yanzu, bayan Barcelona ya koma ƙungiyar Vissel Kobe ta Japan daga shekarar 2018 zuwa 2023, sannan ya koma Emirates ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda ya yi shekara ɗaya kafin ya yi ritaya.
Ya lashe kofuna da dama ciki har da zakarun turai ta kofin duniya da ya lashe a shekarar 2010.
A shekarar 2010 ce aka yi tunanin Iniesta zai lashe kambun bayan Spain ta lashe gasar cin kofin duniya amma bai samu nasara ba, sannan a shekarar 2012 da Spain ta lashe gasar cin kofin nahiyar turai ta biyu a jere aka sake yin tunanin zai lashe, amma nan ma bai samu nasara ba.
Sai dai an yi amannar Iniesta gwani ne wajen taka leda, musamman wajen rarraba ƙwallo da murza ta yadda yake so.
Zlatan Ibrahimović
Zlatan Ibrahimović, wanda aka haifa a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 1981, fitaccen ɗanwasan ƙasar Sweden ne, wanda ya yi shekaru yana jan zarensa wajen zura ƙwallaye a raga.
Yana cikin ƴanwasan gaban da ake ganin sun ƙware a duniyar ƙwallo, inda ya lashe kofuna guda 34 a zamaninsa.
Ya zura ƙwallaye guda 570, ciki har da sama da ƙwallaye guda 50 a ƙungiyoyin da ya taka leda.
A shekarar 2022, Zlatan ya ce bai lashe kambun ba ne saboda yana bayyana ra'ayinsa a kan komai daidai da yadda ya fahimta, inda ya bayyana a wata tattaunawarsa da Bild da kafar Goal.com ta ruwaito cewa, "akwai siyasa a wajen bayar da kyautar nan. Matuƙar kana bayyana ra'ayinka, ba za ka samu ba."
Neymar Jnr
Neymar da Silva Santos Júnior ɗanwasan ƙasar Brazil ne da aka haifa a ranar 5 ga watan Fabrairun 1992.
Lokacin da tauraron ɗanwasan ya fara haskakawa, musamman wajen iya taka leda da zura ƙwallaye, sai aka fara tunanin an samu magajin Messi da Ronaldo.
Yanzu haka shi ne ɗanƙwallon da ya fi zura ƙwallaye a tarihin ƙasar Brazil, duk da zaratan ƴanƙwallon da ƙasar ta fitar a baya.
Saur tara ɗanwasan yana shiga cikin sahun ƴan takarar lashe kyautar amma bai samu nasara ba, sannan a shekarar 2015 da 2017 da aka fi tunanin zai lashe, sai duk ya ƙare a na uku.
Hazard
Eden Michael Walter Hazard ɗanƙwallon ƙasar Belgium ne da aka haifa a ranar 7 ga watan Janairun 1991.
Ɗanwasan ya yi tashe matuƙa musamman a lokacin da yake ƙungiyar Chelsea da ma tawagar ƙasarsa ta Belgium.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin zarata ƴanƙwallon da aka yi a zamanin nan saboda ƙwarewarsa wajen iya murza tamaula.
Sai dai tauraronsa bai haska ba bayan ya koma ƙungiyar Real Madrid, wanda aka yi zaton shi ne zai maye gurbin Cristiano Ronaldo a kulob ɗin.
Ya lashe kyaututtuka da dama ciki har da gwarzon matashin ɗanƙwallo sau biyu da gwarzon ɗanƙwallon gasar Premier League, sannan ya lashe gasar ta Premier da sauran kofuna.
Wesley Sneijder
Wesley Sneijder ɗanwasan tsakiya ne na ƙasar Netherlands, wanda ya yi fice wajen iya rarraba ƙwallo a tsakiyar filin wasa.
Ya buga ƙwallo a ƙungiyoyin Ajax da Real Madrid da Inter Milan da Galatasary.
A shekarar 2010 ce ya kasance cikin ƴanwasan da suka fi nuna bajinta wajen jagorantar ƙungiyar Inter Milan ta lashe gasar zakarun Turai, sannan ƙasarsa ta Holland ta zo ta biyu a gasar kofin duniya, wanda hakan ya sa aka yi tunanin zai iya lashe kambun Ballon.
Amma a ƙarshe sai ya ƙare a na huɗu, inda Messi ya lashe kambun a shekarar.
Xavi Hernández
Xavi Hernández tsohon ɗanwasan tsakiya ne na ƙasar Spain, wanda ya fi yin fice a zamanin da yake taka leda a ƙungiyar Barcelona, kulob ɗin da daga bisani ya horar da ƴanwasanta.
Duk wata nasara da Messi ya samu, tare suka samu da Messi da Iniesta, inda suka yi kusan shekara bakwai suna kaka-gida a harkar ƙwallon ƙafa ta ƙungiyoyi.
Xavi ya lashe gasar La Liga biyar da Copa del Rey uku da zakarun turai biyu da sauransu.
A shekarar 2009 ya shiga ƴan takarar kyautar su uku, inda Messi ya doke su da shi da Cristiano, sannan a shekarar 2010 da 2011 ma ya shiga cikin mutum uku na ƙarshe, amma bai samu nasara ba.
Robert Lewandowski
Robert Lewandowski ɗanwasan ƙasar Poland ne da a yanzu yake taka leda a ƙungiyar Barcelona ta Spain.
Ɗanwasan gaba ne da ya ƙware wajen zura ƙwallo a raga. Zuwa yanzu ya zura ƙwallo sama da guda 700 a wasannin da ya buga waa ƙasarsa da ƙungiyoyin da ya wakilta, kuma har yanzu yana cigaba da jefa ƙwallaye.
A shekarar 2020 ce aka yi tunanin ɗanƙwallon zai lashe kyautar, amma annobar Covid-19 ta hana shirya bikin.
Sai dai ya cigaba da nuna bajinta bayan an dawo daga kullen annobar, amma sai Messi ya doke shi waje lashe kyautar a shekarar 2021, inda aka ba shi kyautar wanda ya fi zura ƙwallaye, lamarin da ya matuƙar haifar da muharawa a tsakanin masu kallo.
Griezmann
Antoine Griezmann wani fitaccen ɗanƙwallon ƙafa ne da ya yi tashe sosai, amma bai taɓa lashe kambun na gwarzon ɗanƙwallon ba.
Ɗanwasan gaba ne na tawagar ƙasar Faransa da a yanzu yake ƙungiyar Atletico Madrid.
Ya lashe kofuna da dama, ciki har da kofin duniya da wasu kofuna da daman gaske da ya lashe a ƙungiyoyin da ya wakilta.
A shekarar 2016 ce aka fi yin tunanin zai lashe kambun, amma ya zo na uku bayan Messi da ya lashe, da Cristiano Ronaldo da ke biye masa.
Franck Ribéry
Franck Henry Pierre Ribéry tsohon ɗanwasan ƙasar Faransa, sannan ya buga ƙwallo a ƙungiyoyi da dama, amma ya fi fice a zamaninsa a Bayern Munich.
A kyautar ta shekarar 2013 ce aka yi zaton ɗanwasan zai lashe, amma sai ya zo na uku, inda Cristiano Ronaldo ya lashe, Messi ya zo na biyu.
Amma ya lashe kyaututtuka da kofuna da dama, ciki har da gasar Bundesliga da ya lashe guda tara da sauransu.
Virgil van Dijk
Virgil van Dijk ɗanwasan bayan ƙasar Netherlands ne da yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Liverpool ta Ingila.
Ɗanwasan wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Yulin 1991 yanzu haka shi ne kyaftin ɗin tawagarsa da ƙungiyarsa.
A sheƙarar 2019 ce aka yi tunanin ɗanwasan zai lashe kyautar, amma Messi ya doke shi, duk da cewa shi ne ya lashe kambun gwarzon ɗanƙwallon nahiyar Turai a shekarar.
A wata tattaunawa da ya yi da kafar Goal.com, ɗanwasan ya ce bai ji daɗin rashin lashe kyautar ba a shekara.
An fara buga labarin ne a ranar 23 Mayun 2025.