Ƴanwasan Premier da kwalliyar sayensu ta kasa biyan kuɗin sabulu

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da wani lokaci akan samu sa'a a dace wajen sayen ƴan wasa a gasar Firimiyar Ingila, sau da dama kuma wasu ƙungiyoyin kan yi ɗaukar kara da kiyashi.

Bari mu duba wasu daga cikin musayar ƴanwasa da aka yi rashin sa'a a gasar ta Firimiya.

Romelu Lukaku (Inter zuwa Chelsea) - £97.5m

A shekarar 2021 Romelu Lukaku ya koma Chelsea, ƙungiyar da ya fi ƙauna tun yana yaro; bayan ya taimaka wa ƙungiyar Inter Milan lashe gasar Serie A ta hanyar zura ƙwallo 24.

Sai dai bayan cin ƙwallo takwas kacal a kakar 2021-22 ya koma Italiya a matsayin ɗan wasa na aro, kuma daga nan bai sake buga wa Chelsea wasa ba.

Bebe (Vitoria zuwa Man Utd) - £7.4m

Tsohon mai horas da Manchester United, Sir Alex Ferguson na da wata ɗabi'a ta zuwa ya kalli ɗan wasa a fili kafin ya saye shi. To amma ya karya wannan sharaɗin nasa lokacin da ya yi wata sayayya mai muni, inda ya ɗauko Bebe.

Wasa biyu kacal ɗan wasan na gaba ya buga wa United a gasar Firimiya, wanda hakan ke nufin an biya shi gwargwadon fan miliyan 1.06 a kan kowane wasa da ya buga.

Danny Drinkwater (Leicester zuwa Chelsea) - £35m

Chelsea a ƙarƙashin Antonio Conte ta sake haɗa Danny Drinkwater da abokin wasansa N'Golo Kante, wadanda su biyun suka taimaka wa Leicester City ta lashe gasar Premier a 2016.

To amma ɗan wasan tsakiyan ya buga wasa 23 ne kacal a tsawon kakar wasa biyar bayan kudi fam miliyan 35 da aka narkar domin dauko shi.

Antony (Ajax zuwa Man Utd) - £86m

Erik ten Hag ya taho da Antony zuwa Manchester United lokacin da ya bar Ajax.

Masoya ƙwallon ƙafa sun kyautata zato sosai a kan ɗan wasan gefen na Brazil bayan da United ta zuba zunzurutun fam miliyan 86 domin sayen shi.

Sai dai bayan zura ƙwallo 12 a wasa 96 da ya buga wa ƙungiyar, United ta tura shi Real Betis a matsayin aro a watan Janairun 2025.

Andy Carroll (Newcastle zuwa Liverpool) - £36m

Andy Carroll ya isa Liverpool lokaci ɗaya da Luiz Suarez, amma Suarez ne tauruwarsa ta haska a Anfield.

Ƙwallo 11 ne kacal Carroll ya ci wa Liverpool bayan sayo shi kan kudi fam miliyan 36, yayin da Suarez wanda kudinsa ba su kai haka ba, wato fam miliyan 22.8 ya ci gajiyar zamansa a Liverpool.

Andy Carroll arrived at Liverpool alongside Luis Suarez, but it was the Uruguayan who went on to light up Anfield. Carroll only scored 11 times during his stay after signing for £36m while £22.8m Suarez had a very contrasting fortune.