Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda uwa da uba da ‘ya’yansu suka rasu bayan cin abinci mai guba a jihar Sokoto
Iyalai shida 'yan gida ɗaya sun rasa ransu bayan da suka ci abinci a ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najerya.
Mazauna ƙauyen mai suna Naman Goma sun shaida wa BBC Pidgin cewa iyalan ba su da lafiya tun a ranar Alhamis, 8 ga watan Augustan 2024 bayan da suka ci rogo da gero da aka dafa tare kamar yadda suka saba.
Abdullahi Dandare ƙani ne ga maigidan da iyalan suka rasu, ya shaida wa BBC Pidgin cewa bayan sun gan su sun shiga mayuwacin hali sakamakon cin abincin sai aka garzaya da su asibiti.
Ya ce a washegari Jumma'a ne suka yanke shawarar kai su asibiti saboda sun ga halin da suka shiga.
Ya ƙara da cewa: "Muna kan hanyar zuwa asibiti ne ɗaya daga cikin yaran ya mutu, sannan bayan da muka isa asibitin kuma mahaifiyar yaran ma ta rasu.
"Daga bisani kuma bayan mahaifyar ta rasu, biyu daga 'ya'yan da suka rage ma suka rasu."
Dandare ya ce mahaifin yaran na cikin waɗanda suka yi jana'izar iyalan nasa da suka mutu.
"Bayan da aka kammala jana'izar matar da 'ya'yanta ne kuma, sai muka fahimci shi ma mahaifin yaran jikinsa ba ƙarfi daga nan ne muka ɗauke shi zuwa asibiti, shi ma washegari ya mutu." in ji Abdullahi Dandare.
Ya ce sauran yaran hudu na kwance a asibiti ana ba su magani sakamakon gubar da suka ci a cikin abincin.
Ɗaya daga cikin maƙwabtan mamacin mai suna Abdullahi, ya shaida wa BBC Pidgin cewa iyalan gidan mutanen kirki ne, ba ruwansu da fitina.
"Ni maƙwabcinsu ne tsawon shekaru, ba mu taɓa samun wata matsala a tsakaninmu ba, kuma ba ni jin sun taɓa samun wata rashin fahimta da wani ma a ƙauyen nan," a cewarsa.
Dagacin ƙauyen na Naman Goga ya ce a lokacin da lamarin ya faru ba shi nan.
Sannan ya ce ya san iyalin mutanen kirki ne, ba ruwansu da fitina da kowa a ƙauyen.
Ma'aikatar lafiya ta jihar Sokoto ta ce tana bincike a kan lamarin domin gano abin da ya haddasa mutuwar iyalan.