Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kacici-kacicin Ranar Hausa ta Duniya
A ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ce ake gudanar da bikin Ranar Hausa ta duniya.
Shekaru 11da suka gabata ne wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya suka kirkiro da wannan ranar tare da kebe kowace ranar 26 ga watan Agusta a zaman ranar wannan bikin.
A bana dai ana gabatar da gangamin bikin ranar ta Hausa ne a birnin Daura da ke jihar Katsina, inda za a baje al'adu da gargajiyar Malam Bahaushe tare da gabatar da muƙala da tattaunatanawa daga masana.
A bara ma an gabatar da irin wannan babban taro a birnin Khumasi da ke ƙasar Ghana.
Albarkacin wannan rana, BBC Hausa ta kawo muku wannan kacici-kacici domin ku wasa ƙwaƙwalwarku ta yadda za ku fahimci cewa ko kuna da masaniya sosai dangane da harshen na Hausa ko kuma a'a.
BBC ta zaɓo wasu kalmomi da ke bayyana launi a Hausa inda muka kawo muku jerin su da harshen Turanci domin ku zaɓi kalmar Turanci da kuke ganin ita ce ta dace da kalmar ta Hausa.
Kacici-kacicin ya ƙunshi tambayoyi guda 10, inda duk kalmar da kuka zaɓa ta Turanci daga cikin jerin kalmomin sai ku latsa "Submit" domin aike wa da amsar taku kuma take za a sanar da ku sakamakon abin da kuka zaɓa wato ya yi daidai ko kuma a'a.