Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Qatar'
Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta fara abin da ta kira ''martani mafi girma da nasara'' kan hare-haren Amurka a cikin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi
A ƴan mintunan da suka wuce ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Qatar.
Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da sanarwar kai harin ta kafofin yada labaran ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato sanarwar da ke cewa saƙon Iran ga Amurka da ƙawayenta ''a bayyane yake''.
''Iran ba za ta yarda da duk wani hari da aka kai cikinta domin keta mutuncinta da kimarta da tsaron ƙasarta a yafi a banza a kowane irin yanayi ba,'' in ji sanarwar dakarin na juyin juya hali.
Tun da farko an bayar da rahoton cewa ƙasar ta rufe sararin samaniyarta na wucin gadi, inda ta ce sansanonin dakarun sojin ƙasa na cikin shirin ko-ta-kwana.
Al-Udeid wani babban sansani soji ne da ke wajen Doha, babban birnin Qatar, wanda ya kasance babbar cibiyar rundunar sojin saman Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
A ranar Asabar da daddare ne Amurka ta ƙaddamar d ahare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku da ke faɗin ƙasar da nufin wargaza su.
Jim kaɗan bayan hare-haren, Shugaba Donald Trump ya ce jiragen yaƙin Amurka sun jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lamarin da ya ƙara girman yaƙin da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran.
Dama dai Iran ta sha alwashin mayar da martani kan hare-haren.
Gwamnatin Qatar ta yi Allah wadai da hare-haren, tana mai cewa ba a samu asarar rai ko jikkata a hare-haren ba.
Kawo yanzu dai babu bayanai game da halin da sansanonin sojin Amurka na Iraƙin ke ciki.
Amurka muka kai wa hari ba Qatar ba - Iran
Majalisar tsaron Iran ta ce harin da ta kai sansanonin sojin Amurka da ke cikin Qatar ba shi da niyyar cutar da ƙasar.
Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce Iran za ta ci gaba da martaba dangantar tarihin da ke tsakaninta da Qatar.
''Harin da muka kai ba ya ɗauke da wani hatsari ga mutanen Qatar, saboda ba ƙasar muka nufa ba'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ''yawan makamai masu linzamin da aka yi amfani da su a harin sun yi daidai da adadin boma-boman da Amurka ta yi amfani da su a cibiyoyin nukiliyar Iran uku''.
Abin da ya kamata ku sani kan sansanin sojin Amurka na Al Udeid da ke Qatar
Sansanin Al Udeid, na wajen Doha, babban birnin Qatar, wanda ya kasance cibiyar rundunar sojin sama Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma sansanin na ɗauke da dakarun Amurka kusan 8,000.
Haka kuma akwai sojojin Birtaniya a sansanin , da a wasu lokuta ake kiransa da filin jirgin saman Abu Nakhla.
Cibiyar ta kasance shalkwatar shirya dabarun yaƙin sojojin Amurka da ke aiki a Iraƙi da sauran ƙasashen yankin Gulf.
A shekarar 2000 ne Qatar ta bai wa Amurka iko da cibiyar Al Udeid.
Bayan Amurka ta karɓe ragamar sansanin a 2001, Qatar da Amurka suka amince da wata yarjejeniya a 2002 wadda a hukumance ta tabbatar da zaman sojojin Amurka a Al Udeid.
A shekarar 2024, kafar yaɗa labaran Amurka ta CNN ta cimma wata yarjejeniya da ta amince da tsawaita zaman dakarun Amurka a Qatar na tsawon shekara 10.