Real Madrid, Man City da PSG na tsaka mai wuya a Champions

Lokacin karatu: Minti 1

Shin Manchester City za ta iya kai shiga cikin ƙungiyoyin takwas ɗin farko a Champions Lig? ina batun Real Madrid da PSG da Juventus za su iya kai wa zagayen 'yan 16 kuwa?

Wasanni uku ne suka rage a sabon rukunin Champions Lig na kungiyoyi 36 da aka fara.

Kungiyoyi takwas ɗin farko za su samu tikitin kai tsaye na zagayen 'yan 16, ba za su buga wasan neman gurbi ba.

Amma ba kowacce ƙungiya ba ce ke jin dadin sabon tsarin wasannin ba. Kamar gwarzuwar Premier Ingila Manchester City tana matsayi na 17 a wasanni biyar da aka yi.

Idan kuma ka leƙa ƙasan teburi za ka tarar da gwarzuwar Champions Lig Real Madrid, Paris St-Germain su duka za su iya gaza kai wa zagayen 'yan 16.

Da farko dai za mu iya tunawa duka ƙungiyoyi 36 na son tsallakawa zagaye na gaba.

Ƙungiyoyi takwas ɗin farko za su tsallaka zagaye na sili 'yar kwale.

Za su jira kungiyoyi 16 su yi neman gurbi, za a yi fafatawar zuwa matakin ƙungiyoyin 24.

Wadanda suke tsakanin tara zuwa 16 za su fafata da wadanda ke tsakanin 17 zuwa 24, wanda za a yi gida da waje.

Waɗanda suke daga 25 zuwa ƙasa an cire su daga gasar kai tsare ko gasar Europa ba za su je ba.