Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku gane jabun magani a kasuwa
A baya-bayan nan Hukumar kula da abinci da magani ta Najeriya (NAFDAC) ta gano wurare da dama da ake ajiye magunguna na jabu da ake sayarwa ko kuma ake shirin fara sayarwa a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan wani shiri da hukumar ta ƙaddamar an kai samame a wuraren da ake zargin ko dai an jibge ko kuma ana kasuwancin irin waɗannan magunguna.
NAFDAC ta ce tun bayan fara samamen, a cikin mako biyu ta gano jabun magani da ya kai tirela 10 a kasuwar Idumota da ke Legas, kudu maso yammacin ƙasar.
A kudu maso gabas kuma hukumar ta gano jabu da kuma haramtattun magunguna tirela biyu a kasuwar magunguna ta Onitsha Bridgehead Drug Market da ke jihar Anambra.
Haka nan a hukumar ta gano tarin magungunan jabu, wadanda suka haɗa da na zubar da ciki da maganin cututtuka na Antibiotics da wasu da dama a kasuwar Ariaria da ke garin Aba na jihar Abia.
Wannan na nuni da munin yawaitar magaugunan jabu a fadin Najeriya, ƙasa mai yawan al'umma sama da miliyan 200.
Hukumar ta NAFDAC ta fitar da wasu bayanai kan yadda za a iya gane jabun magunguna:
Kantin sayar da magani
Hukumar NAFDAC ta ce ya kamata mutane su lura da wuraren da suke zuwa sayen magani.
"Kantin da Nafdac ta yi wa rajista ne kawai ya kamata mutane su sayi magani a wuri," in ji hukumar.
Hukumar ta ce a mafi yawan lokuta ana sayar da jabun magunguna ne a kantuna ko wuraren sayar da magunguna da ba su da rajistar hukumar.
Farashi
Wuraren da ake sayar da magunguna cikin rahusa fiye da sauran kantuna, za su iya kasancewa wuraren da ake sayar da jabun magani, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Irin waɗannan kantuna kan kawo magunguna marasa kyau suna sayar da su a farashi mai rahusa, wanda hakan kan ja hankalin mutane sanadiyyar arhar maganin.
Wani dalilin da ke ƙara sanya farashin magani ya yi sauki a irin waɗannan kantuna shi ne saboda ba su biyan haraji.
Mazubi
Abu na uku da ya kamata mutane su lura da shi shi ne mazubin magani. Hukumar ta ce ya kamata mutane su lura da rashin inganci a mazubin magani, wadda babbar alama ce ta rashin ingancin maganin.
Wata alama da za a lura da ita kuma a jikin mazubin shi ne yadda aka rubuta suna da kuma bayanin magani.
A lokuta da dama akan samu kurakurai a wajen irin wannan rubutu a kan mazubin jabun magunguna.
Ƙamshin magani
Ya kamata mutane su lura da magunguna waɗanda ke wari na daban, kamar warin fenti ko na jan-ƙumba.
Magunguna da ke yin wari na daban ba kamar ƙamshin maganin da kuka saba ji ba, akwai yiwuwar irin waɗannan magunguna na jabu ne.
Illar shan jabun magani
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce jabun maguguna na da matuƙar illa ga lafiya, inda suke gaza magance cututtuka yadda ya kamata wanda hakan zai iya haifar da matsaloli da dama, har ma ya kai ga mutuwa.
Hukumar ta yi ƙiyasin cewa sama da yara 280 ne ke mutuwa kowace shekara sanadiyyar shan magunguna marasa inganci a ƙoƙarin magance cutukan lumoniya ko maleriya a ƙasashen Afirka.
Illolin irin waɗannan magunguna su ne:
- Haifar da cutuka masu bijire wa magani
- Gaza magance cuta
- Cutar da lafiya sanadiyyar sanadarai masu illa wadanda za su iya kai wa ga mutuwa
- Asarar kuɗi