Magungunan da mata suka fi saye na taimakon likitoci gano ko suna ɗauke da kansar bakin mahaifa

Alkaluman da ake tattarowa na kayan da masu sayayya ke sayowa ta hanyar amfani da wani kati na musamman da shaguna ke raba wa manyan abokan cinikayyarsu na taimaka wa likitoci gano wadanda ke dauke da cutar kansa.

Likitocin sun gano sayen maganin ciwon jiki da na ciwon ciki da jama'a ke saya a kai-a kai na bayyana kamuwa da cutar kansar mahaifa.

Sun kuma ce alamun cutar kan bayyana ne bayan cutar ta yi nisa a jikin mata.

Babu isassun alkaluman da za a gane alamun kamuwa da wannan cutar, misali kumburar jiki domin wasu cututtukan ma na da irin wadannan alamun.

Ga wasu daga cikin alamun cutar:

  • Kumburin ciki
  • Rudewar ciki
  • Ciwon kashin kwuibi da ciwon jiki
  • Karancin sha'awar abinci ko saurin koshi da abincin da aka ci
  • Bukatar yin fitsari sau da yawa

Sai dai gano kamuwa da cutar da wuri na taimakawa a magance ta baki daya.

Labarin Fiona

Fiona Murphy na da shekara 25 lokacin da aka gano tana da wani nau'i na kansar mahaifa wadda ba kasafai akan samu irinta ba.

Ta shafe shekaru tana fama da kullewar ciki, lamarin da wasu lilitoci suka dauka ciwon ciki ne kawai.

Ta shaida wa BBC cewa: "Na shafe watanni ina shan maganin nan mai suna Gaviscon kafin a gano cewa kansar mahaifa nake fama da ita."

Ta ce "alamun cutar ba su bayyana ba sosai, sai dai sun rika bayyana a kai-a kai.

Alamar da ta fi muhimmanci a lura da ita ke nan."

Bayan alamun sun ki bacewa, sai aka yi ma ta wani gwaji, inda aka gano wani tsiro mai girma.

Shekarun Fiona 39 yanzu kuma ta zama mai taimaka wa likitocin da ke binciken cutar a asibitin Imperial College da ke Landan.

"Yin bincike domin gano cutar da wuri na da muhimmanci.

Da an gano cutar na tare da ni tun da wuri, da ban sha wahalar jerin aikin tiyatar da aka yi min ba."

Likita James Flanagan shi ne ke jagorantar bayanan da ake wallafawa kan cutar kansa.

Ya ce: "Alamun cutar kansar da muke nema an saba ganinsu - sai dai ga wasu matan, wadannan alamu ne na bayyanar abu mai matukar wahalarwa a rayuwarsu."

"Ta hanyar duba bayanan kayayyakin da ake saye a shaguna, bincikenmu ya gano cewa matan da suka kamu da wannan cutar na sayen magungunan ciwon jiki da na rudewar ciki."

Ya ce wannan alamar na afkuwa ne kimanin watanni takwas gabanin likitoci su gano matan na dauke da cutar ta kansar mahaifa.

Masu binciken sun yi aiki tare da wasu manyan shagunan da ke sayar wa dubban mata kayayyakin da suke bukata na yau da kullum, kuma ta haka sun gano cewa fiye da rabin matan da ke sayen irin wadancan magungunan da aka ambata a sama, na dauke da cutar.

Sai dai akwai bukatar a gudanar da karin bincike domin tabbatar da sahihancin binciken na likitocin.

Ayarin likitocin da likita Flanagan ke jagoranta na shirin fadada binciken nasu ya duba wasu nau'in cutar kansar kamar na ciki da na hanta da kuma na mafitsara.

Sakamakon binciken likitocin na baya-bayan nan an wallafa shi ne a mujallar kimiyya ta JMIR Public Health and Surveillance