Liverpool na zabarin Adam, Akwai yiwuwar Onana ya koma Saudiyya

Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool na son dauko dan wasan Crystal Palace Adam Wharton, Ana alakanta Andre Onana da komawa Saudiyya, David Moyes yana son sake haduwa da Tomas Soucek.

Liverpool za ta yi kokarin gwada yin zabarin dan wasan tsakiyar Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, don ya bar Crystal Palace a kan fam miliyan 50. (Sun)

Kungiyar Neom ta Saudiyya ta fara tattaunawa da wakilan golan Manchester United da Kamaru Andre Onana, mai shekara 29. (Footmercato)

Kocin Everton David Moyes na son dauko dan wasan tsakiyar Jamhuriyar Czech Tomas Soucek, mai shekara 30, daga West Ham. (Sun)

A gefe guda kuma rahotanni na cewa a shirye West Ham din take ta siyar da dan wasan tsakiyarta dan Brazil Lucas Paqueta, mai shekara 27, don taimakawa wajen sake gina kungiyar a bazara, sai dai ba ta shirya sayar da dan wasan gaban Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 28, a kowane farashi ba. (Express)

Barcelona na shirin zawarcin dan wasan gaban Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25, daga Atletico Madrid domin maye gurbin dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski, mai shekara 36. (Marca)

AC Milan na kokarin kulla yarjejeniya da Roma don ci gaba da rike dan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 27 a matsayin aro. (Gazzetta dello)

Kocin Manchester United Ruben Amorim ya sanya dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, da ake son sayarwa fan miliyan 40, a matsayin babban dan wasan gaban da yake son dauka a baraza mai zuwa, kuma United din na da kyakkyawar damar daukar dan wasan na Napoli bayan Chelsea ta ce a kai kasuwa. (Mirror)

Dan wasan Bayern Munich Leroy Sane, mai shekara 29, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Bundesliga, abun da zai kawo karshen fatan dan wasan na Jamus na murza leda a Arsenal ko Liverpool. (Christian Falk)

Tsohon kocin Chelsea da Manchester United Eric Ramsay na cikin wadanda Southampton za ta zaba a matsayin kocinta na gaba. (Sky Sports)

Tsohon dan wasan tsakiya na Wolves na Ingila 'yan kasa da shekara 21, Tommy Doyle, mai shekara 23, na shirin barin kulob din a bazarar nan, kuma duk wani yunkuri na tashinsa, na iya amfanar Manchester City, wadda ke da kashi 50 cikin 100 na yarjejeniyar sayar da shi. (Mirror)