Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta ɗauki Copa del Rey na 31 jimilla bayan cin Real Madrid
Barcelona ta lashe Copa del Rey na 31 jimilla, bayan doke Real Madrid 3-2 ranar Asabar a Estadio Olímpico da ke birnin Sevilla a Sifaniya.
Barcelona ta fara cin ƙwallo ta hannun Pedri a minti na 28 da take leda, kuma na biyu a Copa del Rey, sannan na farko tun bayan wadda ya zura a ragar Atletico Madrid cikin Fabrairu.
Daga baya Real Madrid ta farke ta hannun Kylian Mbappe a bugun tazara, saura minti 20 a tashi daga wasan na El Clasico.
Real ta kara na biyu ta hannun Aurelien Tchouameni, amma Barcelona ta farke ta hannun Ferran Torres, saura minti shida a tashi karawar.
Alkalin wasa ya bai wa Barcelona fenariti, bayan da Raul Asensio ya yi wa Raphinha keta a da'ira ta 18, daga baya aka soke bayan tuntuɓar VAR.
Haka suka tashi min 90 da ɗan karin lokaci suna 2-2, daga nan aka je karin lokacin minti 30, inda minti 15 ɗin farko sakamakon bai canja ba.
A mintin 15 na biyu ne a cikin karin lokaci, Barcelona ta kara na uku a raga ta hannun Jules Kounde, saura minti biyar a tashi fafatawar.
An bai wa Antonio Rudiger da kuma Lucas Vázquez jan kati a karawar ta manyan ƙungiyoyin Sifaniya.
Wasan karshe na takwas kenan da suka kara a Copa del Rey a tarihi, inda kowacce ta yi nasara lashe shi sau huɗu.
Wannan shi ne karo na uku da suka haɗu a gasa a kakar nan, inda Barcelona ta je ta doke Real Madrid 4-0 a La Liga a Santiago Bernabeu cikin Oktoban 2024.
Haka kuma dai Barcelona ta lashe Spanish Super Cup a kan Real Madrid da cin 5-2 a Saudiyya a cikin watan Janairun 2025.
Za su kara fafatawa nan gab a watan gobe, inda Barcelona za ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a La Liga ranar 11 ga watan Mayu.
Wannan shi ne Copa del Rey na 31 da Barcelona ta ɗauka, ita ce kan gaba a yawan lashe shi, sai Athletic Bilbao mai 24 da kuma Real mai 20 jimilla.
Tuni dai aka yi waje da Real Madrid a Champions League a hannun Arsenal, ita kuwa Barcelona za ta buga daf da karshe da Inter Milan.
Barcelona ce kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid mai rike da kofin bara.
Wasannin da suka rage a gaban Barcelona:
Champions League Laraba 30 ga watan Afirilu
- Barcelona da Inter Milan
Spanish Primera Liga Sa 03 ga watan Mayu
- Valladolid da Barcelona
Champions League Tu 06 ga watan Mayu
- Inter Milan da Barcelona
Spanish Primera Liga Su 11 ga watan Mayu
- Barcelona da Real Madrid
Spanish Primera Liga Th 15 ga watan Mayu
- Espanyol da Barcelona
Spanish Primera Liga Su 18 ga watan Mayu
- Barcelona da Villarreal
Spanish Primera Liga Su 25 ga watan Mayu
- Ath Bilbao da Barcelona
Wasannin da suka rage a gaban Real Madrid:
La Liga Lahadi 4 ga watan Mayu
- Real Madrid da Celta Vigo
La Liga Lahadi 11 ga watan Mayu
- Barcelona da Real Madrid
La Liga Laraba 14 ga watan Mayu
- Real Madrid da Mallorca
La Liga Lahadi 18 ga watan Mayu
- Sevilla da Real Madrid
La Liga Lahadi 25 ga watan Mayu
- Real Madrid da Sociedad
Bayanai kan ƴan wasan da Barca da Real suka fara wasan da su:
Ferran Torres ya fara buga wa Barcelona wasan a madadin Robert Lewandowski, wanda ke jinya.
Haka kuma Gerard Martin ya fara tsare baya daga ɓangaren hagu, wanda ya maye gurbin Alejandro Balde, wanda shima ke jjinya.
Ƙyaftin Marc-Andre ter Stegen yana benci, wanda ya daɗe yana jinya sakamakon raunin da ya ji a wasan La Liga tun daga cikin watan Satumba.
Ƴan wasan Barcelona 11 da suka fara wasan Real Madrid:
Szczesny, Kounde, Cubarsi, Martinez, Martin, De Jong, Pedri, Yamal, Olmo, Raphinha, Torres.
Masu jiran ko-ta-kwana::
Pena, ter Stegen, Christensen, Garcia, Fort, Araujo, Lopez, Gavi, Torre, Fati da kuma Victor.
Ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe, wanda ya ji rauni a wasa da Arsenal a Champions League a Santiago, ya fara da zaman benci.
Ferland Mendy ya fara wasan na Copa el Rey ranar Asabar, wanda ya sha jinyar mako uku.
Ƴan ƙwalllon Real Madrid da suka fuskanci Barcelona:
Courtois, Mendy, Rudiger, Aencio, Vazquez, Tchouameni, Ceballos, Valverde, Bellingham, Vinicius da kuma Rodrygo.
Masu jiran ko-ta-kwana:
Lunin, Gonzalez, Alaba, Garcia, Vallejo, Modric, Guler, Diaz, Endrick, Mbappe.