'Yadda ƴansandan Brazil ke yanke wa mutane hukuncin kisa'

A woman lifts a blue tarpaulin which covers a body. She appears to be crying out. The legs of bystanders can be seen behind her.

Asalin hoton, Bruno Itan

    • Marubuci, Rute Pina
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 6

Fitaccen mai ɗaukar hoton nan na Brazil, Bruno Itan ya tashi da safiyar wata rana, inda ya tara da wayarsa cike da hotuna da aka turo masa ta manhajar Whatsapp.

A cikin zaurukan manhajar WhatsApp na ƴan'unguwarsu inda ya girma, inda mutane ke cewa fara jin karar hareb-harbe.

Wani abu da Itan bai sani ba sai a lokacin, mummunan samamen ƴansanda a tarihin ƙasar na aukuwa.

A cewar ofishin shigar da ƙara, wadda ke bayar da taimakon shari'a ga masu rauni, aƙalla mutum 121 ne aka kashe tare da kama 113 a samamen.

Kusan jami'ai 2,500 ne aka aika yankunan domin kakkaɓe ayyukan ƙungiyar Red Command, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin masu aikata laifi a Brazil, a garuruwan Alemão da Penha a arewacin Rio.

Residents walk past police officers during the operation in Alemão Complex

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Samamen ƴansandan shi ne mafi muni a birnin tun 1990, inda hukumomin suka kwashe gomman shekaru suna ƙoƙarin kakkaɓe ayyukan gungun masu aikata laifuka.
A topless man looks at a burnt car blocking the street

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Kusan jami'ai 2,500 ne aka aika yankunan domin kakkaɓe ayyukan gungun ƙungiyar Red Command, a Alemão da Penha.

'Hukuncin kisa'

Gwamnatin yankin ta bayyana samame a matsayin ''babban samame da dakarun birnin Rio de Janeiro suka aikata''.

A wani ɓangare na yunkurin da Rio de Janeiro ke yi na daƙile yaɗuwar ayyukan gungun masu aikata laifukan, gwamnan birnin Cláudio Castro ya bayyana samamen a matsayin ''babbar nasara'' da ya haifar da ''mummunar koma-baya ga aikata laifuka''.

Ofishin kare haƙƙin bil'adama na MDD ya ce ya ''kaɗu'' da samamen ƴansandan, kamar yadda Bruno Itan ya bayyana.

"Nan a Brazil babu hukuncin kisa a dokokin ƙasar. Duk wani laifi koma wane iri ne kama mutum ya kama a yi domin gurfanar da shi a gaban kotu. Amma wannan hukuncin kisa ne'', a cewar Itan.

"Ƴansanda ne ke iya tantance wanda zai rayu da wanda zai mutu."

Itan ya fara aikin ɗaukar hoto a 2008 kuma ya yi aiki a matsayin mai ɗaukar hotunan gwamnatin daga a hukumance 2011 zuwa 2017.

Gawarwaki a dandalin

Police officer during operation in the Penha and Alemão complexes

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Tun da farko, gwamnatin jihar Rio ta ce waɗanda ake zargi 60 da ƴansanda huɗu ne kawai aka kashe.
Police officers during the raid in Rio.

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Samamen ya ƙunshi jami'an tsaro 2,500
Burned car blocks passage in the favela

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, An tsara samamen ne domin aiwatar da sammacin kamu da aka yi wa gomman mutane a yankin
Police officers and residents during operation in Rio

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Fiye da mutum 100 aka kama a wani ɓangare na samamen

Itan ya isa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na safe, inda ya tarar da motoci da dama a ƙone ga kuma ramuwar harsasai a jikin wasu, sanna ya samu mutanen unguwannin cikin tashin hankali.

"Na ga harbi, na ga ƙonannun motoci. Haka ma mazauna unguwar sun bayyana yadda ƴansandan suka yi hareb-hare.''

Itan ya ce ''an kai gawarwaki masu yawa zuwa, ciki har da na ƴansanda Asibitin Getúlio Vargas'', amma har ya zuwa lokacin adadin wadanda suka mutu 64 ne.

A cewar mai ɗukar hoton ƴansandan sun hana ƴan jarida shiga garin Penha.

To amma Itan ya bi ta ɓarauniyar hanya, inda ya samu damar shiga yankin, ya kasance agarin har tsawon kwana guda yana ɗaukar hotuna.

Washe gari da safe mazauna garin suka ɗauki gawarwakin zuwa wani dandali a Penha, inda suka jera su a kan dogon layi domin nuna yawan kashe-kashen da aka yi a samamen.

Kafofin yaɗa labaran Brazil, sun ƙiyasta cewa an samu gawarwaki tsakanin 50 zuwa 70.

Around two dozen residents of Penha search a hillside for people who went missing after a police raid. Some of them are looking down what looks like a ravine, while others are walking.

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Mutnane da ba su ga yan'uwansu ba, sun fara nemansu bayan samamen.

Rahotonni sun ce an gano da dama daga cikin gawarwakin daga wani tsauni da ke kusa da garin, inda yansandan suka ce a nan ne aka samu mafi yawan arangamar.

"Ƴan'uwa ne da kansu ke neman gawarwakin. sun kuma samu damar zuwa tsaunin a kan babura da ƙananan motoci tare da ɗauko gawarwakin daga can,'' in ji IKtan.

Bodies covered in sheets lying in a row in São Lucas Square. People are surrounding the bodies.

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Mazauna garin sun kai gawarwaki kusan 55 a dandalin São Lucas

"Kusan gawa 20 aka fara ganowa tare da ɗauko su, daga nan adadin ya kai 25, sannan 30, sai 40 sai 45 haka dai...rayuka ne fa koma me suka aikata ai ba su cancai kisa ba'', in ji shi.

ƴan jarida sun tuntuɓi gwamnan Rio, Cláudio Castro game da kalamansa na bayyana kisan da ''na masu laifi'', tare da cewa ƴansanda ne kawai suka mutu a samamen.

Binciken kimiyya zai ci gaba

Families crying upon identifying bodies in Alemao Complex

Asalin hoton, Bruno Itan

Binciken kimmiya

A group of people - many of them women - look at the ground where bodies have been placed. One man is covering his mouth with his T-shirt. A woman is grabbing the shoulders of the woman in front of her and is crying.

Asalin hoton, Bruno Itan

Bayanan hoto, Mazauna garin Penha sun shiga cikin raɗani yayin da suke gano wasu gawarwaki a wani tsauni da ke kusa da garin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Itan na ganin cewa, tsare-tsaren jami'an tsaro a yankin ba su aiki yadda ya kamata.

"Abin mamaki kullum ƙarar harbin bindiga za ka riƙa ji. Ko da yaushe harkoki ba sa tafiya daidai, fannonin ilimi da lafiya da gidaje da al'adu, kowane fanni na fuskantar matsaloli.''

Itan, wanda ya tattara bayanan wasu samamen - kamar wanda aka kai a Jacarezinho da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 a watan Mayun 2021, wanda aka gani a matsayin mummuna a tarihin ƙasar - amma ya ce kwata-kwata babu haɗi tsakanin wancan da wannan.

A ranar 29 ga watan Oktoba, ofishin shigar da ƙara da ƙasar ya buƙaci cibiyar binciken kimiyya ta Rio de Janeiro ta fitar da bayanan binciken da ta yi kan mutanen da suka mutun sakamakon samamen ƴansandan.

Haka kuma ofishin ya buƙaci tabbaci kan cewa kotun ƙolin ƙasar ta bayar da damar samamen ƴansandan.

Matakan da za a ɗauka sun haɗar da sanya kyamaroria jiki, tsarin da ya kamata a bi a dokance idan z a akai samame irin waɗannan yankuna.

Haka kuma masu shigar da karar sun buƙaci gwamnan Rio ya tabbatar an bi wannan doka.

Haka kuma kotun kolin ƙasar ta buƙaci gwamnatin Rio ta smaar da cikakkun bayanai kan samamen da bayansa.

Bruno Itan ya kalli abin cikin takaici. Ya ce idan al'umma na kallon irin wanna abu matsayin nasara, ''to kuwa lallai an yi asara''.

"Ina tabbatar muku cewa idan wani ya mutu a harkar miyagun ƙwayoyi, akwai wasu biyu ko uku da za su maye gurbinsa," in ji Itan.