Ko tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila na nufin an kawo ƙarshen rikicin?

Shugaban Amurka Donald Trump ke jawabi wa manema labarai, kafin shigarsa jirgi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amuka Donald Trump ne ya bayyana tsagaita wutar a ranar Litinin
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran, wanda ya ce zai kai ga samar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.

Hakan ya zo ne bayan kwashe kwana 12 ana musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu, tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hari na farko a ranar 13 ga watan Yuni.

Matakin da Amurka ta ɗauka na jefa bama-bamai a cibiyoyin nukiliyar Iran ya ƙara ruruta barazanar da aka shiga na fargabar yaɗuwar rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya.

Tuni yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara tangal-tangal, inda shugaban Amurka Donald Trump ya zargi dukkanin ɓangarorin biyu da karya yarjejeniyar.

Idan yarjejeniyar ta yi nasara, ana sa ran za ta taimaka wajen cimma zaman lafiya mai ɗorewa.

To amma kamar sauran rikice-rikice, ana buƙatar tattaunawar diflomasiyya mai ƙwari kafin cimma hakan.

Me tsagaita wutar ke nufi?

Masu zanga-zanga a Isra'ila sun buƙaci da a atsagaita wuta

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wata ma'ana ɗaya tilo ta 'tsagaita wuta' duk da cewa kalmar ta samo asali ne daga kalaman sojoji na "cease fire" (tsagaita wuta), wadda akasi ce ta "open fire" wato buɗe wuta.

Ya danganta da abin da ɓangarorin biyu masu faɗa da juna suka amince a kai.

Tsagaita wuta abu ne da ya ƙunshi samar da wata yarjejeniya a hukumance wadda ta ƙunshi:

  • Dalilin tsagaita wuta
  • Matakin siyasa da zai biyo baya
  • Yaushe za ta fara aiki
  • Wurin da za a yi aiki da ita

Haka nan yarjejeniyar za ta iya bayyana ayyukan soji da za a iya yi da kuma waɗanda aka haramta, da kuma yadda za a sanya ido kan aiki da yarjejeniyar.

Mayaƙan tawayen NPFL a Laberiya a 1993

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarjejeniyar tsagaita wuta a shekarar 1993 ta kawo ƙarshen yaƙi tsakanin gwamnatin Laberiya da ƴantawayen NPFL

Tsagaita wuta na wucin-gadi ne ko dindindin?

Zai ta iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan.

Wani lokaci ɓangarorin da ke adawa da juna za su iya amincewa kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi ko kuma tsagaita wuta kafin gudanar da wani abu =.

Akan yi hakan ne domin rage tsananin rikicin ko kuma domin kai agaji.

Akan iya ƙulla ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta domin samar da yanayin da zai bayar da damar tattaunawa domin neman samun matsaya kan zaman lafiya na dindindin.

Shugabannin Ethiopia da Eritrea na gaisawa bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Algiers a shekarar 2000.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Habasha da Eritriya a shekarar 2000 ta kai ga yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin

Majalisar Dinkin Duniya ta taɓa shirya yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo ƙarshen yaƙin basasa a Lebanon a shekarun 1978 da 1981 da kuma 1982.

Sai dai yaƙin ya riƙa ci gaba a duk lokacin da yarjejeniyar ta ƙare, kuma ba a samu damar kawo ƙarshen rikicin ba har sai a shekara 1990.

Freed Israeli hostages on a bus, November 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza an saki ƴan Isra'ila 105 da ake garkuwa da su inda ita kuma Isra'ila ta sake Falasɗinawa 240 da take tsare da su
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Isra'ila da Hamas sun kira tsagaita wuta da aka ƙulla tsakaninsu a Nuwamban 2023 a matsayin ta kai agaji.

Tsagaita wuta domin kai agaji a wasu lokuta ana amfani da su domin rage tsananin yaƙi ko kuma domin rage uƙubar da al'umma ke ciki.

Misali, gwamnatin Sudan ta taɓa cimma yarjejeniya da ƙungiyoyin ƴan tawaye biyu, wato Ƙungiyar ƴanta al'ummar Sudan (SLM) da ta tabbatar da adalci da daidaito (JEM), lamarin da ya sa aka tsagaita wuta na kwana 45 domin bai wa ƙungiyoyin agaji damar kai kayan agaji ga al'umma.

A 2004, bayan ambaliyar Tsunami ta fada wa ƙasar Indonesia, gwamnatin ƙasar da kuma ƙungiyar Free Aceh Movement sun ayyana tsagaita wuta domin bayar da damar kai agaji a yankunan da ake yaƙi.

Akwai kuma yarjejeniyar da akan ƙulla domin kawo ƙarshen yaƙi a wani takamaiman yanki.

A shekarar 2018, Majalisar Dinkin Duniya ta cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Yemen da ƴan tawayen Houthi domin daina yaƙi a yankin tashar ruwa ta Hodeida domin kare al'ummar yankin.