Lokuta huɗu da Tinubu ya sauya matsayar gwamnatinsa bayan shan suka

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan matakin da shugaban Najeriya ya ɗauka na sauya matsayarsa kan jerin mutanen da ya yi wa afuwa.
Mutane sun yi ca a kan shugaban ƙasar bayan da aka zarge shi da sanya sunayen mutanen da ba su dace ba a cikin jerin.
Baya ga sauran al'umma da suka yi ta sukar matakin shugaban ƙasar, hatta iyalin wasu daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar sun soki matakin.
Misali shi ne yadda iyalan marigayi Herbert Macauly suka yi watsi da matakin bisa dogaro da yadda aka yi afuwar.
A wani taron manema labarai a birnin Legas bayan fitar da jerin sunayen na farko, iyalin Macauly ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Olabode George sun ce bai kamata a cakuɗa sunan ɗan kishin ƙasar da "manyan masu sana'ar ƙwaya da masu aikata laifukan daban-daban ba."
Bayn haka nan ƴan Najeriya sun yi ƙorafi kan sanya sunan Maryam Sanda - matar da kotu ta yanke wa hukuncin kisa bayan samun ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu.
Wannan soke-soke sun turasasa wa ministan shari'ar ƙasar fitowa ya bayayyana cewa ba a kai ga kammala matakin afuwar ba, don haka afuwar ba ta tabbata ba.
Tun daga lokacin ne aka riƙa raɗe-radin wata-ƙila Shugaba Tinubu zai sauya ra'ayinsa kan wasu daga cikin waɗanda ya yi wa afuwar tun farko.
Ilai kuwa!
A cikin ƙunshin sunayen da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Laraba bayan "sake yin nazari" na waɗanda suka samu afuwar shugaban, babu sunan Maryam Sanda, kodayake sunan nata ya koma cikin waɗanda aka rage wa tsawon hukuncin da aka yanke musu.
A yanzu dai Maryam Sanda za ta yi zaman ɗaurin shekara 12, maimakon afuwar da tun da farko aka yi niyyar yi mata.
Ga sauran lokutan da gwamnatin Tinubu ta sauya matsayi kan matakan da ta ɗauka, bayan shan suka:
Sunayen waɗanda za a naɗa ministoci

Asalin hoton, Social Media
A farkon watan Agustan 2023 ne Shugaba Tinubu ya aika da ƙunshin sunayen mutanen da yake son naɗawa muƙamin ministan ga majalisar dattawan ƙasar domin tantancewa.
Cikin jerin sunayen har da na Maryma Shetty, wata matashiya daga jihar Kano.

Asalin hoton, FACEBOOK/MARYAM SHETTY
Bayyanar sunan Maryam Shetty ya zo wa mutane da dama da mamaki, ganin yadda jihar Kano ta tara manyan ƴan siyasa masu tasiri da ɗimbin mabiya.
Matakin kuma ya janyo gagarumar muhawara musamman a shafukan sada zumunta game da cancanta da dacewar naɗa ta matsayin minista.
To sai dai gabanin tantance Maryam Shetty a zauren majalisar dattawan, sai fadar shugaban kasar ta sanar da janye sunanta, tare da musanya ta da Dokta Mariya Mairiga, wadda a yanzu ke matsayin ƙaramar ministar Abuja.
Dokar haraji

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2024 ne Shugaba Tinubu ya aika wa majalisar dokokin ƙasar ƙudurin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
Sabuwar dokar ta ƙunshi yin gyara a yadda ake rabon harajin kayayyaki wato VAT, wani abu da ya janyo zazzafar muhawara a ƙasar, musamman daga arewacin ƙasar, da ke ganin matakin zai cutar da yankin.
Suka da adawa da matakin da gwamnonin arewaci da wasu fitattun yankin suka nuna, ya sa an jingine muhawara kan batun a majalisar dattawan ƙasar a watan Disamban 2024.
A lokacin, majalisar ta ce an jingine batun ne domin yin wasu gyare-gyare a kan saɗarorin da ake taƙaddama a kansu.
Daga ƙarshe an gyara wuraren da aka nuna turjiya a kansu, a wani zama da gwamnonin ƙasar suka yi a Abuja, kamar yadda Gwamnan Kaduna Uba Sani ya shaida wa BBC a wata hira.
A zaman da gwamnonin suka gudanar, sun yi gyare-gyare ga ƙudurin harajin , musamman ɓangaren rabon harajin kaya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo ce-ce-ku-cen.
"Mun zauna mun ga tsarin, mun ga cewa babu wata jiha da za a iya cutar da ita, inda a sabon kasafin zai kasance kashi 50 cikin 100 ne ga dukkan jihohi, yayin da za a bayar da kashi 30 ga jiha daga cikin abin da ta tara, sai kuma kashi 20 za a yi amfani da yawan al'ummar jihar'', in ji gwamnan Kadunan.
Daga baya, a ranar 26 ga watan Yuni ne Shugaba Tinubun ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin.
Cirewa da mayar da shugaban NTA

Asalin hoton, Social Media
Haka ma a cikin watan Agustan wannan shekarar ta 2025 ne wata sanarwa daga gwamnatin Najeriya ta sanar da sauke shugaban hukumar Talabijin ta Najeriya, NTA, Salihu Abdullahi Dembos.
Sauke shi ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.
Masu sukar sun ce sauke shi ba ya bisa doron doka, kasancewa wa'adin mulkinsa bai cika ba, kuma ba wani laifi ya aikata ba.
To sai dai ƴan kwanaki bayan haka Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin mayar da Salihu Abdullahi Dembos kan muƙamin nasa.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a 2023 - a yanzu zai dawo domin kammala wa'adin mulkinsa na shekara uku.
Me sauya matsayar ke nufi?
Audu Bulama Bukarti, ƙwararren lauya masanin dokokin Najeriya ya ce abin da matakin ke nufi shi ne Shugaba Tinubu da gwamnatinsa suna sauraron jama'a a duk lokacin da suka yi kuka kan wani abu da suka yi ƙorafi.
''Hakan na nufin cewa a duk lokacin da gwamnatin Tinubu ta ɗauki wani mataki, kuma ƴankasar suka nuna ba su ji daɗi ba, to Tinubu kan waiwaya ya sauyayi jama'a, domin sauya matsaya'', in ji gogaggen lauyan.
Haka kuma Barista Bukarti ya ce hakan naufin cewa a wasu lokuta gwamnatin ba ta yin dogon nazari kafin ɗaukar matakai.
Ya ƙara da cewa in da gwamnatin na dogon nazari kafin ɗaukar kowane irin mataki, to da ba za riƙa yin irin haka ba.
''Don haka ya kamata fadar shugaban ƙasa ta riƙa mayar da hankali wajen tantance abubuwa tare da yi musu duba irin na tsakani kafin fitar da su'', in ji shi.
Tasirin muryar mutane
Wasu masana na ganin matakin a matsayin irin tasirin da muryar mutane ke da shi a tsarin dimokradiyya.
Suna masu cewa inda komai gwamnati ta yi wanda bai yi wa jama'a daɗi ba, idan za su fito su nuna ɓacin ransu, gwamnatin za ta iya sauya matsayinta.











