Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a jerin ministocinsa

..

Asalin hoton, FACEBOOK/MARYAM SHETTY

    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a matsayin wadda za a naɗa kan muƙamin minista, inda ya maye ta da sunayen mutum biyu.

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da haka a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aika wa majalisar kuma ya karanta yayin wani zama a Juma'ar nan.

Sunayen mutum biyu da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar sun haɗar da Festus Keyamo da kuma Dr. Mariya Mairiga.

Ba a dai bayyana dalilin janye sunan Maryam Shetty a jerin ministocin da Tinubun zai naɗa ba

Rahotanni sun ce da safiyar yau, rukunin wasu mutane daga Kano sun yi dafifi a harabar majalisa, don nuna goyon bayansu ga naɗa Maryam Shetty a matsayin minista.

Ranar Laraba ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya aika da jerin sunaye na biyu na mutanen da yake so Majalisar Dokokin ƙasar ta tantance domin naɗawa a matsayin ministoci.

Bayyana sunan Maryam Shetty ya janyo gagarumar muhawara musamman a shafukan sada zumunta game da cancanta da dacewar naɗa ta matsayin minista.

Matasa da yawa sun yi ta nuna goyon bayansu ga yunƙurin naɗa Maryam minista, saboda a cewarsu matashiya ce kuma 'yar gwagwarmayar siyasa da ta ba da gudunmawa a jam'iyyar APC.

An riƙa yaɗa wani bidiyo da ke nuna Shetty da safiyar Juma'a, lokacin da ta isa harabar Majalisar Tarayya ta caɓa ado domin fuskantar tantancewa, kafin daga bisani ta samu labarin cewa an janye sunanta.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

An ga matashiyar a wani bidiyon daban lokacin da take cikin mota tana bayani kan yadda ta samu labarin cire sunanta.

Muhawara ta sake ɓarkewa game da Shetty

Tuni dai muhawara ta ƙara zafi bayan sanar da janye sunan Maryam Shetty cikin jerin mutanen da Tinubu zai naɗa ministoci.

A cikinsu masu sharhi a shafin sada zumunta na Tuwita har da Salihu Tanko Yakasai wanda ya ce na tausaya wa Maryam Shetty.

Ko ta cancanta ko ba ta cancanta ba.

Na ɗora alhakin tsarin da aka bi wajen bayar da sunanta da janyewar daga bisani.

Wannan abin kunya ne kuma mai yiwuwa ne ba za ta taɓa mantawa da wannan kunyatawar ba.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ganduje

Asalin hoton, GANDUJE/FACEBOOK

Dr Mariya Mairiga Mahmud, ita ce 'yar siyasar da aka maye gurbin Maryam Shetty da sunanta don naɗawa matsayin minista daga Kano.

Tsohuwar kwamishiniya ce a ma'aikatar ilmi mai zurfi a gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi mulki daga 2019 - 2023. Ƙwararriyar likitar iyali ce da ta yi aiki a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu, kafin naɗa ta kwamishiniyar ilmi a Kano.

Wace ce Maryam Ibrahim Shettima?

...

Asalin hoton, FACEBOOK/MARYAM SHETTY

An haifi Maryam Shettima ce a jihar Kano, a shekarar 1979.

Ta yi digirinta na farko a jami’ar Bayero da ke Kano, inda ta yi karatu a fannin lafiya, inda ta ƙware a fannin gashi.

Ta kuma samu digirinta na biyu a jami’ar Stratford da ke Birtaniya inda ta karanta fannin kula da ƙashi na ɓangaren wasanni.

Maryam ta kasance a cikin likitocin tawagar Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin Landon a shekara ta 2012.

Baya ga wannan, Maryam ta yi kwasa-kwasai da dama a wasu cibiyoyi na ƙasashen duniya, ciki har da Amurka.

Duk da cewa ba ta taɓa yin takara ba, ta kasance ƴar siyasa a a jam'iyyar APC mai mulki.

Ta kasance a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Kuma shahararriya ce a shafukan sada zumunta na Najeriya.

Me ƴan Najeriya ke cewa kan ba da sunan Maryam a matsayin minista?

Tun bayan sanya sunanta cikin jerin ministocin da shugaba Tinubu ke so Majalisar Dokoki ta tantance, ake ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta, musamman ma tuwita.

Muhawarar ta fi mayar da hankali ne kan cancanta ko kuma rashin cancantar ta.

Ga tsokacin da wasu suka yi a shafukansu na sada zumunta.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@YALHAQ ya ce "Ban san ki ba kuma ban yi tsammanin sunanki zai shiga jerin ministoci ba, to amma sai ga shi sunanki ya shiga ciki. Na yi amannar cewa tunda dai muna kan roƙon Allah Ya ba mu waɗanda suka fi(cancanta), to kin cancanci muƙamin kuma ina miki fatan samun nasara a wannan aiki da ke gabanki."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wata mai amfani da twitter mai suna Zainab Nasir Ahmed ta wallafa a shafinta, inda ta ce "Na gode shugaba Bola Tinubu da ka sanya sunan ƴar'uwata Dr Maryam Shetty a matsayin ministan gwamnatin Tarayyar Najeriya. Wannan zaɓi ne mai kyau kuma ina na yi amannar cewa za ta yi ƙoƙari a ma'aikatar da za a tura ta."

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 5

@Maxajee ya ce "Ba ina raina ƙwarewar Maryam Shetty ba ne to amma muƙamin minista ya yi wa mace kamarta yawa. Idan sunayen mata irin su Hadiza Bala Usman suka kasa shiga cikin ministoci, ban ga dalilin da zai sa a sa sunan Maryam Shetty ba. Wane ƙwarewa take da shi?"