Wace ce mace ta farko Babbar Alƙaliya ta jihar Kano?

Kano Chief Judge

Asalin hoton, Dije Aboki's Family

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Karon farko a tarihin Kano, mace za ta jagoranci ɓangaren shari'ar jihar a matsayin cikakkiyar babbar alƙaliya, ba riƙo ba.

Ana iya cewa, naɗin Mai shari'a Dije Aboki, wata muhimmiyar manuniya ce cewa matan Kano sun kawo ƙarfi, a yanzu suna iya gogawa da takwarorinsu, matuƙar aka ba su dama a fannonin da a baya maza ne kawai suka yi kaka-gida, kamar jagorancin ɓangaren shari'a da sha'anin mulki.

Ranar Alhamis ne, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin Dije Aboki a muƙamin babbar alƙaliya ta Kano.

Matakin ya zo ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika sunanta gaban majalisar, don ta amince da naɗa Dije Aboki, wannan babban muƙami a ɓangaren shari'a.

Mai shari'a Dije Aboki ta ɗare kan wannan kujera ce, tun cikin watan Maris ɗin bana a matsayin riƙo, bayan gwamnan wancan lokaci, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗa ta.

Mai shekara 59, Dije Aboki ta fara aiki da ma'aikatar shari'ar Kano a matsayin lauyar gwamnati a 1985.

.

Asalin hoton, Dije Aboki's Family

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne, majalisar dokokin Kano ta tabbatar da Dije Aboki a muƙamin Cif Jojin Kano

Me ake cewa game da nagartar Dije?

Lauyoyi da dama ne musamman a jihar ke bayyana kyakkyawan fata kan naɗin Jastis Dije Aboki a muƙamin cif joji ta Kano. "Alƙaliya ce da ta san doka kuma tana aiki da doka, sannan tana da zurfafa bincike, kuma ta fahimci dokokin Najeriya," a cewar wani lauya mazaunin London.

Ita ma, wata lauya mai zaman kanta kuma tsohuwar shugabar ƙungiyar mata lauyoyi ta jihar Kano, Barista Huwaila Muhammad Ibrahim ta ce naɗin babbar alƙaliyar, abin yabawa ne ga ɓangaren shari'a.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta bayyana Mai shari'a Dije Aboki a matsayin alƙaliya mai bin ƙa'ida a lokacin aiki. A cewarta, mata za su yi alfahari da wannan muƙami, kuma zai daɗa ƙarfafa musu gwiwa da zaburar da su a kan himmar ba da gudunmawa wajen inganta rayuwar mata da ƙananan yara, ci gaban Kano da ma al'ummarta gaba ɗaya.

Barista Audu Bulama Bukarti, fitaccen lauyan da ya taɓa aiki a Kano, amma yanzu yake zaune a London ya ce Mai shari'a Dije, alƙaliya ce mai ƙoƙarin tsaftace aiki, musamman wajen kauce wa cin hanci da rashawa ko yin alfarma. Kuma a cewarsa, ba a san ta da aikata abin da bai dace ba a kan aiki.

Bukarti ya ce a hannunta ya fara koyon aikin lauya, lokacin da yake ɗalibi a Kwalejin Koyon Aikin Shari'a da ke Kano. Ya ce yana da ƙwarin gwiwa a kan ƙwarewarta da ƙoƙarinta na tsayawa a kan gaskiya.

''Tun da nake shari'a a gaban kotunta, ban taɓa jin cewa ta yi wani abu da bai kwanta min a rai ba, bisa son rai. Ko ta yi ƙoƙarin karɓar wani abu. Sannan ban taɓa jin wani lauya ya yi ƙorafi da ita ba," in ji Bukarti.

A cewarsa, Dije "Alƙaliya ce mai ƙoƙarin yin aiki cikin gaskiya, babu cin hanci, babu almundahana, ba alfarma. Kuma ba sani, ba sabo, in dai aka zo batun aiki."

Ita ma, Barista Huwaila ta ƙara da cewa, wani hali da Mai shari'a Dije Aboki ta yi fice da shi, shi ne rashin wasa da aiki. Kuma ba ta yarda da mai wasa da aiki ba.

"Ni dai har na bar aikin lauya a Kano, ban taɓa ganin wani alƙali ko alƙaliyar da lauyoyi ke tsoron kawo masa wasa ba, kamar Justice Dije," in ji Barista Bulama.

Ya ce alƙaliya ce da ba ta lamuntar yawan neman ɗage shari'a a kotun da take jagoranta. "Ni kaina duk shari'o'in da na yi a kotunta sun ƙare a cikin ƙasa da shekara biyu."

Bulama Bukarti ya ce samun mutum kamar Mai shari'a Dije a matsayin babbar jojin Kano, babban ci gaba ne ga ɓangaren shari'a a lokacin da jan ƙafa wajen gudanar da shari'a ya zama babbar matsala.

"Ana samun ɗage shari'a tsawon sama da shekara huɗu ko biyar. Kai har shekara goma ana iya shafewa ana wata shari'ar," in ji shi.

Barrister Aisha Tijjani, malama a kwalejin koyar da harkokin shari'a ta Aminu Kano, ta ce kasancewar Dije Aboki, mace ta farko da ta riƙe muƙamin babbar jojin jiha, wani muhimmin ci gaba ne musamman ga mata.

Ta ƙara da cewa "haƙiƙa, mu mata mun ji daɗi kuma mun yi murna game da wannan naɗi, don kuwa yanzu an samu gauraye a tsakanin masu jagorantar rassan gwamnati uku". Wato ɓangaren zartarwa da ɓangaren majalisa da kuma na shari'a.

Barista Aisha Tijjani ta ce naɗa Mai shari'a Dije, na nufin ɓangaren shari'a na Kano ya daɗa ƙarfi, ci gaba ne ga jihar don kuwa ya nuna ana fifita cancanta wajen naɗa mutumin da ya dace a matsayin cif joji, ba tare da la'akari da bambancin jinsi ba.

"Kuma muna fatan samun sauye-sauye a fannonin da suka shafi al'amuran mata, musamman laifukan da ake aikata wa mata'', in ji Barista Aisha

Wace ce Justice Dije aboki?

An haifi Mai shari'a Dije Aboki a cikin birnin Kano, ranar 10 ga watan Yulin 1964. Ta fara makarantar firamare a 1969.

Sannan ta halarci sakandiren 'yan mata ta Minna a jihar Neja tsakanin 1973 - 1978.

Dije Aboki ta yi digirinta na farko a fannin shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zari'a daga 1980 zuwa 1983.

Sannan ta halarci Kwalejin Koyon Aikin Shari'a da ke Legas tsakanin 1983 - 1984.

Ana iya cewa ta shafe tsawon rayuwarta tana aiki a ɓangaren shari'a, inda ta fara alƙalanci daga 1986 a matsayin majistare ta II. Mai shari'a Dije Aboki ta zama babbar majistare ta I a 1994.

A shekara ta 2006 ne kuma ta zama mai shari'a a babbar kotun jiha, kujerar da ta ci gaba da riƙewa har zuwa bana.

Justice Dije Aboki

Asalin hoton, Dije Aboki's Family

Sauyi huɗu da ake sa ran za ta iya kawowa ɓangaren shari'ar Kano

Barista Bulama Bukarti ya ce duk da yake, ikon da doka ta bai wa alƙalin alƙalai ko cif joji wajen kawo gyara a ɓangaren shari'a ba su da yawa, amma akwai muhimmiyar gudunmawar da yake kyautata zaton Mai shari'a Dije za ta iya bayarwa wajen kawo sauye-sauyen da za ta iya cikin huruminta a Kano.

Abu na farko, in ji Barista Bulama Bukarti, shi ne tura ƙararraki zuwa kotuna.

Ya ce da yake duk shari'ar da aka shigar gaban babbar kotun jiha, ana kai fayal ɗin zuwa ofishin cif joji, don ta raba wa kotunan da ke faɗin jihar su yi shari'a.

"To a nan, wasu lokuta ana yin hannu ya san na gida, wasu lauyoyi ko masu ƙara sukan shigar da ƙara, sannan su yi ta bibiyar takardun shari'ar don ganin an kai gaban alƙalin da suke tunanin za su samu sassauci, kuma mafi yawanci rashin gaskiya ake yi," in ji Bukarti.

Fitaccen lauyan ya ce a ganinsa irin wannan lamari, ba zai taɓa yiwuwa ba a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Dije.

Ya ce hakan zai kasance wani muhimmin sauyi da yake ganin za a samu a jagorancinta.

Abu na biyu kuma shi ne batun ɓata lokaci wajen gudanar da shari'a.

Barista Huwaila Muhammad ta ce sanin da ta yi wa Mai shari'a Dije na alƙaliya maras wasa da aiki, za ta iya kawo gyara a wannan lamari, ta yadda za a riƙa gudanar da shari'o'i kuma a kammala su a kan lokaci.

Wani lamari kuma da Barista Bukarti ya yi ƙarin bayani a kai game da Mai shari'a Dije Aboki shi ne: "kasancewarta alƙaliya mai girmama lokaci, wadda aka san ta a kan al'adar cewa idan ka je kotunta minti biyar bayan lokacin da doka ta ce a zauna, to ka makara".

Ya ce ta wannan fuska ma, yana ganin sabuwar cif jojin za ta iya kawo sauyi a kotunan Kano.

Haka kuma, ya bayyana fatan cewa za ta gyara wa masu ruwa da tsaki zama a ɓangaren shari'a wajen ganin suna girmama lokaci musamman ta hanyar halartar shari'o'i a kan lokaci.

Abu na gaba da ake tunanin za a iya samun canji a ƙarƙashin jagorancinta, shi ne ƙoƙarin rage almundana da cin hanci musamman a tsakanin ƙananan kotuna.

Barista Bukarti ya yi zargin cewa "akwai alƙalan da suka yi ƙaurin suna wajen aikata ba daidai ba, musamman ta fuskar cin hanci. To ina ganin Justice Dije ba za ta lamunci wannan ba".

Ɗumbin mata ne dai, ba kawai a Kano ba, har ma da wasu sassa, za su taya Mai shari'a Dije Aboki murna da fatan alherin za ta zame musu jakada ta gari a jagorancin da ta ɗauka na ɓangaren shari'ar Kano.

Cike da fatan bayar da gudunmawa ga duk wani yunƙuri na tsare haƙƙoƙin mata da ƙananan yara, da kuma bunƙasa rayuwar musamman masu ƙaramin ƙarfi, ta yadda a ƙarshe, al'ummar Kano za ta ce sambarka. Gwamma da aka yi, Dije!