Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo

Tuni aka riga aka fara kiɗayar ƙuri'a bayan rufe rumfunan zaɓe a faɗin jihar Edo, kuma daga yanzu za a iya fara samun sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. An dai gudanar da zaɓen ne ƙananan hukumomi 18 na jihar ta Edo.
Mutum 2,629,025 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, mai ƙananan hukumomi 18 da kuma rumfunan zaɓe 4,519.
Ƴantakara 16 suka yi takarar inda mutum ɗaya ya janye, inda maza 15 da kuma mace ɗaya suka takarar neman kujera mafi girma a jihar ta wato ta gwamnan a ƙarƙashin jam'iyyu daban-daban.
Sai dai ana ganin fafatawar ta fi zafi a tsakanin mutum uku daga cikinsu waɗanda ake ganin a cikinsu ne za a samu wanda zai lashe zaɓen - 'yantakarar PDP, da APC, da LP.
Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP na kammala wa'adin mulkinsa na biyu bayan shafe shekara takwas a matsayin gwamnan jihar. Yanzu abin da kowa ke son sani shi ne wane ne zai maye gurbin Obaseki?
Ku sa manuni a kan wannan taswira ta jihar Edo domin ganin sakamakon zaɓen kai tsaye da zarar hukumar zaɓen jihar ta fara sakin su daga ƙananan hukumomi 18 na jihar.







