Amfanin shan hantsi don ƙara yawan sinadarin vitamin D

Asalin hoton, Getty Images
Vasuki, wani injiniya da ke yin manhajoji a birnin Chennnai, ya kasance yana fama da matsalar ciwon jijiyoyi da kuma gajiya akai akai.
"Na ɗauka gajiyar aiki ce ko kuma rashin barci," in ji shi.
Bayan fama da matsalar na tsawon watanni, ya yanke shawarar zuwa domin ganin likita - ya yi matuƙar kaɗuwa.
Gwajin jini da aka yi masa ya nuna cewa sinadarin vitamin D ya ragu matuƙa a jikinsa.
An gudanar da wani bincike kan muhimmancin sinadarin vitamin D a jiki da kuma barazanar raguwarsa a jiki a wasu birane da ƙauyukan birnin Delhi, babban birnin Indiya.
A cewar rahoton binciken, kashi 70 na mutanen da ke zaune a birane ba su da isasshen sinadarin vitamin D, yayin da na waɗanda ke zaune a ƙauyuka kuma ya kai kashi 20.

Asalin hoton, Getty Images
An gudanar da binciken ne kan mazauna birane da kuma ƙauyukan birnin Delhi da kuma ƙewayensa.
Idan matakin jini ya yi kasa da nanogram 10 na vitamin D, to hakan na nufin cewa sinadarin ya ragu matuƙa. Matakin vitamin D da aka samu a yawancin mutanen birane da aka yi binciken yana a nanogram 7.7.
Sannan a ƙauyukan kuma vitamin D ɗin yana a matakin nanograms 16.2. Yayin da matakin jini da ya kai nanogram 30 ke nufin cewa akwai isasshen vitamin D, mafi yawan mazauna ƙarƙara na fama da matsalar.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar lafiya ta Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce mata ne suka fi yiwuwar fama da rashin sinadarin vitamin D fiye da maza.

Asalin hoton, Getty Images
Yaya lamarin yake a Tamil Nadu?
Wani bincike da aka yi kan mata masu juna biyu daga birnin Chennai na Indiya, ya bayyana cewa kashi 62 na matan ba su da isasshen sinadarin vitamin D.
Mutane da dama daga Chennai sun shiga cikin wannan bincike kan "ƙarancin vitamin D a biranen Indiya da ke kudanci" wanda jami'ar Cambridge ta wallafa.
Har ila yau, binciken ya kuma gano cewa kashi 66 na mutanen da aka yi binciken a kansu suna da ƙarancin vitamin D. Kuma mata sun fi ƙarancin sinadarin a kan maza.
Bincike a birane irinsu Punjab, Tirupati, Pune da kuma Amravati ya nuna cewa an fi samun masu ƙarancin vitamin D a birane fiye da waɗanda ke zaune a ƙauyuka.

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne dalilin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana iya samun sinadarin Vitamin D ne kai-tsaye daga hasken rana. Jihohin Indiya da ke arewaci, na samun isasshen hasken rana a yawan lokuta in ban da ƴan watanni kalilan, yayin da yankuna masu zafi kamar birnin Chennai ke samun hasken rana a tsawon shekara - amma me ya sa yiwuwar samun ƙarancin vitamin D yake a wurin mutanen birni?
Wani likitan fata a Chennai Dakshinamoorthy, ya ce ɗan'adam na samun vitamin D ne ta hanyar hasken rana da kuma abinci.
"Ɗaukacin vitamin D da jiki yake buƙata na zuwa ne daga rana. Fatar mutun ta sama na samar da wasu sinadarai idan rana ya bugi fatar, sai waɗannan sinadarai su koma vitamin D3. Yayin da hanta da kuma ƙoda ke sauya shi zuwa vitamin D sannan ya aika shi zuwa jiki," in ji shi.
"Saboda zamani da kuma sauyawar yanayin aiki, lokaci da ake shafewa a cikin ɗaki da kuma ofisoshi ya ƙaru. Ko wurin fita waje, batun rufe jiki da tufafi na ƙaruwa, wanda ke rage damar da jiki ke da shi wajen samun hasken rana," in ji Peter, wani likita a asibitin gwamnati a Indiya.
Mutane na ɗaukar cewa idan aka shafe ƴan mintuna a waje za ka samu wadataccen hasken rana. Sai dai gurɓacewar yanayi, tufafi da kuma gilasai a tagogi, na hana jiki samun sinadarin vitamin D da ya kamata," a cewar Peter.

Asalin hoton, Getty Images
Wane adadin hasken rana ake buƙata?
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa namiji a Indiya na buƙatar shafe aƙalla sa'a biyu don shaƙar hasken rana a kowace rana, inda fuskarsa da hannunsa duka ke kallon rana - domin samun nanogram 30 na vitamin D da ake buƙata a rana.
Binciken ya kuma ba da shawarar cewa akwai buƙatar mutum ya yi tafiyar sa'a ɗaya a rana domin samun aƙalla nanogram 20 na vitamin D.
Sai dai, binciken bai yi duba kan mata ba a nan.
"Akwai yiwuwar samun ƙarancin vitamin D a wurin mata ya fi yawa. Saboda ayyukan gida, mata ba sa samun wadataccen hasken rana. Wannan ya sa vitamin D ɗin su yake raguwa," in ji masu binciken.
Likitoci sun ce idan burin mutum shi ne samun vitamin D, to bai kamata ya shaƙi hasken rana ba kusa da taga mai gilashi.











