An haifi tagwaye bakwaini mafiya ƙarancin makonni a ciki

Iyalan

Asalin hoton, GUINNESS

Wasu jarirai tagwaye mace da namiji da aka haifa a Canada, cikin mako 22 sun samu shiga littafin bajinta na duniya kan zama mafiya ƙarancin kwanaki a ciki.

An haifi Adiah da Adrial Nadarajah ne bayan kwana 126 da ɗaukar cikinsu.

Masu tattara bayanan kundin tarihin na Guinness sun ce idan da an haifi jariran baya da sa’a ɗaya to da ma ba maganar ɗaukar matakan cetar rayuwarsu domin ba a ganin za su rayu.

Yawanci cikakken juna-biyu yana ɗaukar mako 40 ne, saboda haka su waɗannan tawagyen an haife su da gibin mako 18 ke nan.

Lokacin da mahaifiyar tasu Shakina Rajendram ta ce ta fara jin naƙuda a mako na 21 da kwana biyar bayan samun cikinsu, ta ce likitoci sun gaya mata cewa jariran ba su ƙosa ba, kuma babu yuwuwar za su rayu sam-sam.

Wannan shi ne cikinta na biyu bayan na farko da ya zube ‘yan watanni a wannan asibiti da ke kusa da gidansu a birnin Ontario.

Hoton tagwayen da lambarsu ta yabo

Asalin hoton, GUINNESS

Mahaifinsu Kevin Nadarajah ya ce likitoci a asibiti sun gaya musu cewa babu abin da za su iya yi a kan waɗannan bakwaini masu ƙarancin kwanaki, abin da ya sa ya shafe dare yana zubar da hawaye.

Asibitoci da dama ba sa ma wani yunƙuri na cetar jariran da aka haifa kafin mako 24 zuwa 26 da samun cikinsu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To amma waɗannan ma’aurata sun yi sa’a da suka je asibitin Mount Sinai da ke Toronto, wanda yake da sashe na musamman na kula da irin waɗannan masu haihuwa.

A rana ta biyu da matar da fara naƙuda wato mako 21 da kwana shida ke nan da samun cikin, likitoci sun gaya mata cewa idan ta haifi jariran ko da ‘yan mintina ne kafin su cika mako 22, za a bari su mutu ne kawai domin ba abin da za a iya yi su rayu.

Ta ce duk da yadda ta riƙa zubar da jini sosai ta yi ƙoƙarin ta riƙe jariran, wato ba ta fara yunƙurin haihuwa ba har suka ƙara wasu sa’o’i a cikin nata.

A ƙarshe dai ta fara shirin haihuwarsu minti 15 bayan sha biyun dare, wato ƙasa da sa’a biyu bayan cikarsu mako na 22 a mahaifa, inda a ƙarshe ta haife su.

Yanzu dai Adiah da Adrial sun cika shekara ɗaya da haihuwa duk da matsanantan matsalolin da suka riƙa gamuwa da su da farko.

Mahaifiyar tasu ta ce sau da dama suna zuba ido kawai suna jiran ganin rasuwar jariran amma sai su warware.

Har yanzu dai likitoci na ci gaba da sanya ido a kansu yayin da kullum suke ƙara girma da lafiya.

Jariri mafi ƙarancin kwanaki da aka taɓa haifa shi ne Curtis Means na Alabama, wanda aka haifa cikin mako 21 da kwana ɗaya.