Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Whatsapp ya sanya harshen Hausa a tsarinsa
Whatsapp ya sanar da fara amfani da ƙarin harsuna uku na Afirka da suka haɗa da harshen Hausa a wayoyin komai da ruwanka na Android.
Kamfanin Meta mamallakin shafukan Whatsapp da Facebook da Instagram ya sanar da wannan matakin ne a wata sanarwa da ya wallafa a Tuwita a ranar Litinin.
Wannan mataki na Whatsapp ya zo ne bayan da a wani lokaci can Google da Facebook suka ɗauki irin sa.
Hausa na daga cikin manyan harsunan da ke ƙara samun tagomashi a duniya kuma masu magana da harshen sun kai kusan miliyan 72 a faɗin duniya.
Whatsapp na daga cikin shafukan da suka da matuƙar farin jini a duniya, kuma a Najeriya ma akwai miliyoyin masu amfani da shi.
Yanzu za a ziro ido a ga ko shafuka irin su Tiktok da Snapchat za su bi sahun ɗaukar irin wannan mataki.