Saƙonnin bogi da 'yan Najeriya ke tura wa kan Whatsapp

Lokacin karatu: Minti 2

Cikin masu amfani da WhatsApp musamman a Najeriya ya duri ruwa bayan da aka rika yada wani sako da ke cewa za a rufe asusunsu idan har ba su tura sakon ga akalla lambobi 20 ba.

Sakon wanda aka rika aika shi a rubuce da kuma sakon murya a harshen Hausa da kuma Turancin Ingilishi an ce ya fito ne daga "Daraktan kamfanin WhatsApp Varun Pulyani."

Har ila yau sakon ya ce an sayar da kamfanin ga Mark Zuckerberg wato mutumin da ya mallaki Facebook da shafin Instagram saboda haka aikewa da sakon zai sa "tambarinku na WhatsApp zai canza zuwa sabon gunki tare da 'f' na Facebook a cikin awanni 24," in ji sakon.

Ya ci gaba da cewa ƙin yin hakan zai sa a goge asusunka na WhatsApp ko kuma kamfanin ya fara cajan ka kudi duk wata.

Sai dai binciken da BBC ta gudanar kan wadannan sakon ya tabbatar da cewa batun ba gaskiya ba ne. Sakon ba daga kamfanin WhatsApp ya fito ba.

Da farko dai wasu mutane biyu ne suka kirkiro manhajar WhatsApp wato Brian Acton da Jan Koum a shekarar 2009.

Kuma suka sayar wa Mista Mark Zuckerberg a shekarar 2014 (kimanin shekara bakwai da suka wuce kenan) kan dala biliyan 19.

Will Cathcart shi ne shugaban kamfanin WhatsApp a halin yanzu don haka ba mu san inda masu yada wancan sakon bogin suka samo Mista Varun Pulyani ba.

Sannan kuma kamfanin WhatsApp yana da shafin kansa a Facebook da Twitter, kuma a can ne yake fitar da sanarwar sabbin sauye-sauyen da ke tafe da kuma sauransu muhimman abubuwan da suka shafi kamfanin.

Hakazalika kamfanin WhatsApp yana iya tura wa duka masu amfani da manhajar sako kai-tsaye ko ta WhatsApp status, kamar yadda ya taɓa yi a baya.

Wasu masana suna danganta wannan sakon bogin da wata sanarwar da kamfanin WhatsApp ya fitar, inda ya ce daga farkon watan Nuwambar 2021 manhajar za ta daina aiki a kan wasu tsofaffin wayoyi guda 43.

Sannan daga ciin saƙwannin akwai wanda aka naɗa na murya da wani Bature ya taƙarƙare yana zuba bayani.

To wannan ma babu tabbas a kansa, yawanci irin masu haɗa murya da hoto su naɗi abin da ransu ya yi musu su yaɗa. Sannan saƙon murya ma a yanzu ba shi da wani tabbas don kowa na iya yi ya aika, sannan ko a Turai ma a kan yaɗa labaran ƙarya.

Don haka wannan saƙo da ya zama ruwan dare a tsakanin ƴan Najeriya, inda suke ta tura wa mutane a kai a kai ba gaskiya ba ne.